Sashe 265
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
You'll never regret buying from us. Mikewa Aunty Mariya dake zaune parlor tayi da mamaki tana kallon Ammi da suka shigo parlon tana rungume da Mayraah, ta karasa kusa da su da sauri tace "An sallameku ne Ammi?" Ammi bata amsan tambayarta ba, hakan yasa Aunty Mariya ta taimaka mata wajen rike Mayraah da ko tsayuwan kirki ta kasa suka wuce sama zuwa Bedroom din Ammi, Ammi ta kwantar da ita a hankali saman gadon sannan ta rufa mata duvet tana kallonta cikin sanyin murya tace "Sannu" Mayraah dai ta kasa cewa komai don ji take kamar an kara mata ciwon da take ji a kirjinta tun da suka fito asibitin, ga wani sabon ciwon kai, Aunty Mariya dai na tsaye ita ma sai sannu take mata ganin yanda take sauke numfashi, Mayraah ta lumshe ido don baza ma ta iya amsawa ba, mikewa Ammi tayi ta fita daga dakin, Aunty Mariya ta bi bayanta ta sameta zaune parlor tayi tagumi, Aunty Mariya tace "Wai an sallameku ne Ammi? naji jikin nata da zafi fa, numfashin ma kamar da kyar take yi" Ammi ta kalleta a fusace tace "To ya bazan dawo da ita gida ba Mariya? Ban san me matar take nufi da ita ba...." Kasa ci gaba tayi ta fashe da kuka, Aunty Mariya that is confuse ta zauna kusa da Ammi tace "Ban gane ba Ammi, me ke faruwa? wace mata?" Cikin rawan murya Ammi tace "Tun fara aikinta a asibitin dama hankalina bai kwanta ba Mariya, har cikin raina naji ban yarda da CEO din asibitin ba, in baki manta ba ai har kiranki nayi na gaya maki tafiyar da ta sa aka yi da ita zuwa UK, ban san meye manufarta akan Mayraah ba, yanzu kuma ana zaune kalau kawai ta kira Abbansu wai tana bukatar birth certificate, to me zata yi da birth certificate din Mayraah? Dama ana haka a asibiti ne? Me yasa tun kwantar da mu ba a bukata ba sai yanzu?" Da damuwa Aunty Mariya tace "Kai Ammi, shine zaki fito da yarinya babu izininsu bayan kin san halin da ta tsinci kanta a kwanakin baya da kyar kuma aka samo kanta, what if jikin nata ya kara rikicewa Ammi? Sannan meye a ciki don an tambayi Birth certificate dinta? This is not enough reason na dawo da ita gida Ammi, ni damuwata kar ciwon nan ya dawo sabo mu shiga uku" Ammi na hawaye tana girgiza kai tace "In sha Allahu hakan bazai faru ba, kawai Alhaji ya dawo a canza mana wani asibitin gaskiya don bani da kwanciyar hankali a asibitin nan, ban san meye manufarta akan yarinya ta ba, wa ya sani ma ko er Cult ce, wallahi duk fargaban da nake kenan" Aunty Mariya dai ta kasa cewa komai tayi tagumi tana kallon yayar tata, Ammi dai hawaye sai sauka idonta yake, bude kofar Parlon aka yi duk suka juya, Abba ya shigo Usman na biye da shi a baya, Abba sai kallon Ammi da ta wani hade rai yake, sai kuma ya kalli Aunty Mariya yace "Ina Mayraahn take?" A hankali Aunty Mariya tace "Tana daki" Wucesu yayi ya shiga dakin, Usman ya karaso kusa da Ammi ya duka yana kallonta yace "Ammi meyasa za ki taho da ita gida a halin nan da take ciki?" Ammi ta fashe da kuka tace "Wallahi Usman ban yarda da Ceo din nan ba, da kyar in ba er shan jini bace" Usman ya ma rasa abinda zai ce mata sai kallonta yake, Abba na shiga Bedroom din yaga wani sabon zazzabi ya rufe Mayraah, sai sauke numfashi take da kyar, ya fito parlor a fusace yana kallon Aunty Mariya yace "Kin dai ga karamin tunani irin na yayarki ko? Ina ce kin dai gani? Yarinyar da dakyar aka samo kanta shine saboda rashin tunani baiwar Allahn nan zata fito da ita asibiti bata duba halin da take ciki ba? Wani me hankalin ne zai yi wannan abun da tayi?" Aunty Mariya ta mike da sauri bata bar sa ya ci gaba ba ta dinga basa hakuri, Ammi dai ko kallonsa bata yi ba hawaye na sauka idonta, Abba da ransa yayi mugun baci yace "Zan maida ita asibitin kuma wallahi bana son ganin kafarta a can, gwara ke Mariya ki je ki ci gaba da jinyarta" Ammi ta mike tace "Wallahi bazaka maida min yarinya asibitin matar nan ba, ai asibitoci kala kala ne a Abuja kuma masu kyau, wanda ma suka fi wancan kyau, me yasa baza a canza wani asibitin ba..." Ko kallonta Abba bai yi ba ya shige dakin Aunty Mariya ta bi bayansa, Usman ya kama hannun Ammi da ke kuka suka fita parlorn ya maidata wani parlor yayi kasa da murya yace "Ammi bai kamata ki fito da ita asibitin ba, har yanzu fa ba wai samun sauki tayi ba kuma kema kin sani..." Katse sa tayi tana kuka tace "Me yasa baza ku fahimce ni ba ne wai Usman??" Usman ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace "Na fahimce ki Ammi, birth certificate dinta da ta bukata ka'idar asibitinsu ne za ayi photocopy a saka cikin file din patient, kinsan ko wani asibiti da rules din su, so baki tsaya kin fahimci dalilin tambayar certificate din da tayi ba kika yi saurin yanke hukunci" Ammi dai bata fasa kukan da take ba, Usman ya dinga kokarin kwantar mata da hankali. Aunty Mariya na rike da Mayraah suka sauka downstairs Abba na biye da su a baya, gaba daya jikin Aunty Mariya yayi mugun sanyi, bata san sanda Abba ya dawo mafadaci haka ba cikin kankanin lokaci, da da ne a yanda ta san sa uffan bazai ce ma Ammi ba sai dai kawai ya maida Mayraah asibiti, amma yanzu sam ba haka ba, ya daina mata uzuri kwata kwata, Mayraah na rungume jikin Aunty Mariya har suka isa asibitin a motar Abba, zuwa sannan kam gaba daya jikinta ya rikice don sai sarkewa numfashinta yake, hakan ya sa aka shiga Emergency da ita. Duk yanda Ammi ta so zata koma asibitin bayan tafiyar su Aunty Mariya Usman bai yarda ya bar ta ta koma ba ganin yanda ran Abbansu ya baci, cikin kwantar da murya yace "Ammi pls ki bari gobe da safe sai ki je tunda tare suka koma da Aunty Mariya kuma kinsan zata kula da ita sosai, don Allah kiyi hakuri ki bari gobe, nima yanzu bazan koma ba, idan ya so gobe da sassafe sai mu je" a haka dai ya dinga kwantar mata da hankali har ta hakura da komawa asibitin amma ba can cikin ranta ba, su Hajja da Mama Ladi suna can dakin visitors basu ma san me ke faruwa ba a gidan. Karfe sha biyu saura aka cire ma Mayraah oxygen da aka sa mata bayan numfashinta ya dawo dai dai, MD da Dr Hamid ne tsaye Emergency ward din watching her closely, MD ya karasa kusa da ita ganin kamar magana take son yi, dukawa yayi yana kallonta bai dai ce komai ba, da kyar tace "Ina son zan sha ruwa pls" Yayi shiru bai ce komai ba kuma bai fasa kallonta ba, hakan yasa ta dauke kanta tana kallon direction din Dr Hamid kilan shi zai taimaketa, shi ma da yaga magana take son masa ya isa kusa da ita ya duka yace "Ya aka yi?" Murya can kasa tace "Dr ruwa nake son zan sha" Calmly Dr Hamid yace "Za ki sha zuwa anjima, be patient" Ta marairaice tace "I'm very thirsty" Yace "I know, za ki sha anjima kadan" Daga haka ya juya ya fita ward din, Abba dake bakin Emergency din a zaune tun dazu ya mike yana kallon Dr Hamid, Dr Hamid yace "Numfashinta is stable yanzu, zuwa karfe daya za a maida ta ward" Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Toh Alhamdulillah" Barin wajen Dr Hamid yayi.... Mayraah ta kara kallon MD kamar zata yi kuka tace "Don Allah ku bar ni in sha ko kadan ne" Shiru yayi da farko, sai kuma yace "Zan baki anjima" Hawaye ya cika idonta tace "To ka kira min yayana nasan shi zai bani" Ya kafeta da ido, a hankali yace "Wani yayan naki?" Tace "Ya Maheer" a hankali yace "Ohk..." Juyawa yayi ya fita daga ward din, bayan wani lokaci ya dawo rike da disposable cup karami da ya debi ruwa kadan cikin Dispenser din dake reception, tana ganin ruwan zata mike zaune amma ta kasa don duk jikinta is weak, ya ajiye karamin cup din, helping her to seat on the bed gently, sannan ya dau ruwan da kansa ya bata very little a ciki, zai mayar ya ajiye a hankali tace "Kadan fa na sha" Sake bata sip daya yayi dai dai nan Dr Balogun ya shigo, da mamaki yake kallonsa da ruwan hannunsa, MD yayi saurin ajiye sauran ruwan sai kuma ya fita ya bar ward din, Dr Balogun yayi disposing ruwan da cup immediately, Aunty Mariya dai na zaune reception tayi tagumi kamar ance ta juya taga Ammi kamar an jefota, mikewa tayi da mamaki ta nufeta da sauri tace "Ammi? Meyasa kika taho cikin daren nan" Ammi da idonta ya kumbura don kuka cikin rawan murya tace "Bazan iya bacci ba Mariya" Aunty Mariya ta kasa ce mata komai, a ranta kuwa fata take Allah yasa kada Abba ya sake wani fadan in ya ganta, can ta kama hannunta suka tafi suka zauna tana kallonta tace "Kin shiga kin duba Maheer?" Ammi na share idonta tace "Ina? Me ya samesa?" Aunty Mariya tace "Ai yana gidan, yana dakinsa baya jin dadi" A hankali Ammi tace "Ai ban sani ba" Aunty Mariya tace "Da ku ka dawo dazu bacci yake ne, saboda shi ne ma nake zaune parlor sai ga ku kun shigo" Ammi dai tayi shiru bata ce komai ba. MD na komawa office dinsa ya tadda Musharraf zaune yana duba wani littafi to distract him daga damuwar halin da Mayraah take ciki, tun da ya fito daga Emergency da aka shigar da Mayraah ya dawo office din yayansa ya zauna, kallo daya Musharraf yayi masa ya maida idonsa kan littafin hannunsa, MD ya ajiye stethoscope dinsa ya zauna kan sofa din office din without