Sashe 48
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tuna wani abu ya juya da sauri yace "An tada sallah, let me go to the mosque" a hankali tace "Will u come back?" Yayi shiru yana kallonta, can yace "Are you afraid of anything?" Ta girgiza masa kai tana share hawayen da yaki tsaya mata cikin sanyin murya tace "I am no longer comfortable" Shiru yayi bayan bayan few seconds yace "Am not leaving you" Daga haka ya juya ya fita, Ta koma ta kwanta maganganun Mama Ladi na mata yawo a kwakwalwarta kamar a lokacin take fadan su, Mayraah bata san sanda ta fashe da matsanancin kuka ba tana jin zuciyarta na mata zafi sosai, bata san for how long she have been crying ba taji an bude kofar ward din, ta kulle idonta da sauri, muryar Maheer taji kusa da ita a hankali yace "Mimi" Still taki bude idon kai sai kace bacci take, Maheer ya ajiye fruits din da ya siyo mata outside of the hospital a kan overbed table sannan ya zauna kan Plastic chair yana kallonta don a tunaninsa bacci take, bayan some minutes Usman ya shigo ward din, yana kallon Maheer yace "I will be going home now to check on Ammi" Maheer yace "Ohk..." Daga haka ya fita daga ward din, Maheer ya ciro wayarsa dake vibrate, Tun yana sallah Haseenah ke kiransa, yaga calls goma tayi masa a mintunan da basu wuce 15 ba, ya daga kiran ya kai kunne, babu ko sallama tace "Maheer wai me kake nufi da dinner dinmu ne yau? Naga har anyi la'asar banji kace min ga abokanka nan zuwa da motoci ba" Maheer rasa abinda zai ce mata ma yayi tsabar takaici, Haseenah tace "Hello" Calmly yace "Ina jin ki" Tace "Ohh da kana ji na kayi shiru, wai ko ka manta munce babu African time ne? Nan da awa daya da wani abu fa ya ci ace duk muna can" Yace "Haseenah" Tace "Ina jin ka" yace "Kije ke da kawayenki da yan uwanki ku yi dinner din, i, my relatives, and my frnds won't be available" Haseenah ta wani zaro ido tace "What?? Ban gane me kake nufi ba Maheer" Yace "Abinda kika ji na fada shi nake nufi tunda ba wani yaren daban na yi maki ba, beside nasan Mumy da sisters dinta baza su rasa gaya maki halin da Mimi take ciki ba tunda sun zo duba ta wajen karfe daya ai" a fusace Haseenah tace "Wannan kai ta shafa Maheer don ni babu abinda ya sha min kai, kuma akan wata can bazan ɓata wannan day din nawa ba wallahi, abu dai da sau daya zanyi witnessing dinsa a duk rayuwata shine za ayi min haka? Naga dai ai ba kai kadai bane a gidan da dole sai kai zaka tsaya da ita a asibiti, don me ma wata tsohuwa a danginku bazata zauna da ita a asibitin ta kula da ita ba sai kai?" Maheer dake ta sauraronta yace "Mayraah din kike ce ma wata?" Ta fashe da kuka tace "Nace din Maheer, abinda duk labari ya gama bazuwa a duniya ashe babu abinda ku ka hada da ita er tsintuwa ce ba Ammi da Abba suka haifeta ba..." Maheer ya mike yace "You've successfully cross ur boundary Haseenah, wllh wllh kika sake furta wani kalma akan Mayraah a yau din nan zan datse igiyarki dake kaina, yanzun nan zan datse alaqar da aka kulla mana just some hours ago without second thought and no regrets" Haseenah that was soo shock and speechless ta buda baki tana sauraron abinda yake gaya mata a kunne, yace "Nonsense" Daga haka ya katse wayar, duk wannan abun Mayraah na jin su hawaye kawai ke sauka idonta. Bude kofar ward din aka yi Aunty Mariya ta shigo rike da basket me dauke da abinci a ciki, Maheer da har sannan xuciyarsa ke tafarfasa akan abinda Haseenah ta fada masa kan Mayraah ya nufeta ya amshi abincin hannunta yace "Sannu da zuwa" Aunty Mariya dake kallon Mayraah a sanyaye tace "Ta farka kuwa?" Maheer yace "Ta farka dazu, amma yanzu bacci take an mata allurai ne" Aunty Mariya ta zauna kan kujera duk abun duniya ya taru ya mata yawa ga Ammi ana tunanin za a taho da ita asibiti a kwantar da ita don jikin nata sai a hankali har yanzu, dafe kanta tayi a hankali tace "Sun je sun kwashe kayansu, in gaya maka abun ba mutunci Maheer, ban taɓa ganin matsiyata mara su kirki ma irin mutanen nan ba, sai kaga abinda suka mana wllh, don ma bakin Mama Ladi da wata makociyarku Maman Shafa bakinsu ba shiru yayi ba, abinda suka manta ne kawai su ma basu gaya masu ba, duk da su suka fara sakin maganganu, Mama Ladi ta fara dura masu zagi, abun dai ba dadi kai dai in gaya maka, zuga guda fa suka yo kamar yaƙi wai sun zo kwashe kaya, Allah ya rufa mana asiri an ga Gwal din nan da ban san ya za a kaya yau ba, don ba lallai ma su hakura muje kasuwa mu nemo ba tara mana jama'ar anguwa kawai za su yi, amma anya da amincewar iyayensa yaron nan ya nemi Mayraah kuwa Maheer? Alamu duk sun nuna dama tun farko they were not in support of the marriage kafin wannan abun ma ya billo" Maheer dai yayi shiru yana kallonta don ya ma rasa abinda zai ce, Aunty Mariya na girgiza kai cike da takaici tace "In the other way round ni sai naga kamar rashin auren ma shi yafi alkhairi da dai wannan tashin hankalin da na gani da idanuwana yau..." Bude kofa aka yi Musharraf ya shigo ward din, Maheer ya sauke kansa kasa codedly yace "Do not say anything, shi ne" Aunty Mariya ta juya tana kallon Musharraf don bata san sa ba, ya karaso ciki ya gaisheta da ladabi, a dakile ta amsa ta dauke kai, Musharraf ya ajiye ledan fruits din hannunsa, Maheer na kallonsa ya ɗan yi murmushi yace "Nima na siyo mata, amma naga bacci take" Musharraf yace "Ohk" duk wannan abun Mayraah na jin su kawai ta rufe ido ne kamar tana bacci, amma ita kadai tasan abinda take ji a duk jikinta most especially her chest and her head that is banging, Musharraf ya juya ya nufi kofa cause duk sai jikinsa yayi sanyi ganin yanda Aunty Mariya ta amsa masa gaisuwa ta dauke kai, Maheer yace "Amma ba tafiya zaka yi ba" Mayraah bata san sanda ta bude idonta da sauri ba jin abinda Maheer yace, amma ta daure bata bari ta juya ba balle su gane idonta biyu, banda bugawa babu abinda zuciyarta ya fara yi da sauri da sauri, Musharraf ya ɗan yi murmushi yace "Aa ina waje" Maheer yace "Ohk" Daga haka Musharraf ya fita ya kullo masu kofar, a fusace Aunty Mariya tace "To uban me ya biyota nan yayi mata kuma? Yau naga iskanci" Maheer ya kwantar da murya yace "Aunty shi fa bashi da laifi, dangin Abbansa ne suke ta wannan abun, ba shi ne yace bazai aureta ba, fin karfinsa aka yi a gida, kuma kinga ba shi da yanda zai yi tunda ga abinda iyayensa suka ce" Aunty Mariya ta wani ja tsaki tace "To me zuwansa nan zai kara mana da shi? Gwara kawai yayi tafiyarsa ni bana son ganinsa gaskiya, yayi tafiyarsa kawai ba a bukatansa ya bar mana er mu ta dawo hayyacinta cikin aminci, tun ban bude baki nayi masa magana ba ka sallamesa gaskiya" Maheer dai ya ma rasa abinda zai ce mata ganin yanda ta hasala, Ta ci gaba tace "Wannan ai rashin kunya ne ma, salon ta farka tayi arba da shi abu ya kara lalacewa" Maheer dake neman yanda zai kauda zancen yace "Aunty Hajja fa?" Aunty Mariya tace "Tun dazu in gaya maka ta daga hankali ita zata tafi Bichi banda hanata da aka yi, kasan Badiyyar ta gudu ta tafi can ai, to shine wai take son zuwa ta sanar ma dangin ubanta abinda ta aikata, mun dai hanata don yanzu ba wannan bane a gabanmu, yanda Mayraah zata dawo hayyacinta ta kwantar da hankalinta, ita ma Ammi Allah ya bata lafiya is our major concern now" Maheer ya girgiza kai a ransa yana tunanin abinda zai yi ma Badiyya da za su yi ido hudu da ita, Aunty Mariya ta mike tace "Bari in koma gida wajen Ammi Maheer, in dai ta farka don Allah ka kirani, Hajja ma na son a kawota nace ta bari sai ta farka, karya muka masu ba a barin kowa ya shiga inda take shine muka samu lafiya amma da jama'ar da za su cika asibitin nan ai sai Allah yau" Maheer bai ce komai ba ya rakata suka fita, Aunty Mariya na kallonsa tace "Abba ya zo?" Maheer ya girgiza kai yace "Tun dai wajen karfe biyu da ya tafi" Aunty Mariya bata kuma cewa komai ba har suka fito haraban asibitin, zaune suka tadda Musharraf a karkashin bishiya, Ya mike yace "Allah ya tsare Aunty" Aunty Mariya tayi kamar bata ji sa ba ta shige mota tayi wucewarta, Maheer sai duk bai ji dadi ba, ya nufi Musharraf yace "Let me make some calls, ka ɗan shiga ciki ba kowa" Musharraf yace "Ohk" Maheer ya zauna karkashin bishiyar, Musharraf ya nufi cikin asibitin, Maheer yayi haka ne don yana tunanin ko da ta farka idan ya bata abincin zata ci tunda dazu da ya bata shayi ta amsa a gun sa.... Musharraf na shigowa ward din Mayraah ta juya jin kamshin turarensa, ya karasa kusa da gadon yana kallon drip din da sai a sannan yayi rabi, yayi kasa da murya yace "Are you still feeling much pain in ur chest?" Ta girgiza masa kai, don tun da aka mata alluran taji ya ɗan mata sauki ba kamar dazu ba, ya ɗan kara gudun ruwan, sannan ya bude basket din da Aunty Mariya ta kawo ya bude warmer din abincin, irish porridge ne da yaji hanta sai kamshi yake, Duk da halin da Ammi take ciki hakan bai sa ta mance abincin da Mayraah ke iya ci in dai bata da lafiya ba, haka ta sa Aunty Mariya tayi mata sannan