Sashe 88
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da danna wayarta, Musharraf ya nuna ma Badiyyah kujeran dake kallon na Mayraah yace "You can sit" a hankali ta zauna edge din kujeran tana wasa da hannunta, sanye take da wani atamfa da dinkin yayi matukar yi mata kyau ya amshi jikinta, ga mayafinta da ta daura saman kai, hannunta kuwa ya sha lalle baƙi da ja da ya kara haska farar fatarta, light make up ne a fuskarta that made her look naturally beautiful, Duk a few seconds Mayraah tayi mata wnn kallon ta side eye, Dr Musharraf ya gama duba abinda Badiyyah tace bata gane ba sannan ya mike ya zagayo ta inda take zaune ya ajiye textbook din a side dinta yace "Now listen, so that u won't get confuse, ba wani abu me wahala bane" Badiyyah da taji kamshin turarensa ya cikata don dab da ita ya duka taji kamar ta sume a inda take a zaune, ko sanin abinda yake cewa ma bata yi ba, nan ya fara kokarin mata explaining din abinda tace bata gane ba, ita dai kallonsa take ko kiftawa babu, bata san haka gayen nan ya hadu ba sai yau da take kallonsa dab dab da ita, his nose, his eyes, his white teeth, his thick eyebrows, cute lips, the way he speaks fluently, and the best of all his cool scent me makalewa a hancin mutum, Subhanallah.... ji tayi kamar ta jawo sa ta rungumesa gam gam, bayaninsa kawai yake amma babu abinda Badiyyah take ji a abinda yake cewa, Mayraah ta mike rike da jakarta, Musharraf ya juya ya kalleta, makullin motarsa ya dauka ya bata yace "Gashi ki dauko stuff din" without looking at him tace "Aa zan yi picking call ne, i will be back" Daga haka ta juya ta nufi kofa ta fice daga office din, Musharraf ya jawo kujeran da ta zauna ya zauna a kai, yana facing din Badiyyah da ta riga ta gama narkewa a wajen, yace "Hope you get where i am heading?" Ta gyada masa kai da sauri, nan ya ci gaba da mata bayanin da bata ganewa ita kuma ta dinga kallonsa babu ko kiftawa.... Mayraah na sauka downstairs kiran Usman ya sake shigowa wayarta, dagawa tayi, a hankali tace "Ina kwana yaya" Yace "Baki ga calls dina bane?" Turo baki tayi tace "Yanzu muka fito lectures ai" yace "Me yasa kika ce in kawo maki jakarki kin san da sassafe za ki fita?" Tace "Ka kawo ne?" Yace "Fito department dinku ki amshi jakarki" Daga haka ya katse wayar, ta saka wayarta cikin jakan hannunta ta tafi inda zata samu Hamidah tace "Hamidah sai gobe in sha Allah" Hamidah tace "Lectures din anjima fa?" Mayraah tace "Kawai ki min attendance pls" Hamidah tace "Toh shikenan sai gobe" Daga haka Mayraah ta juya ta fita daga department din, ba ma kusa da department din nasu yayi parking ba, haka ta karasa har inda ya tsaya da kafa, ta bude motar tana kallonsa tace "Ina kwana" Ya dau jakarta ya mika mata, taki amsa, ta marairaice tace "Yaya don Allah ka ajiye ni gida" Daga sama har kasa yake kallonta yace "Kun gama lectures din ne?" Tace "Kawai na gaji, ina son in kwanta" bata jira me zai ce ba ta shiga motar ta kulle ta jinginar da kanta da kujera without looking at him, bayan few seconds ya tada motar suka bar school din, suna hawa main road ta ɗan juya ta kalli bayan motar jin aroma din abinci dake tashi, ledan wani babban eatry ta gani, can dai ta kallesa tace "I am even hungry" A takaice yace "Me too" Ta ɗan hade rai, sai kuma tace "Naga abinci a back seat fa" Ya jefa mata wani kallo yace "To naki ne?" Shiru tayi tana kallonsa, bata sake ce masa komai ba ta kauda kanta, wayarsa dake ajiye ya fara ring ya daga yace "I am on my way" after some minutes ride sai ga su a gate din wata makaranta wanda ke gaba da na su Mayraah, suna shiga school din bayan sunyi tafiya kadan ya juya yana kallonta yace "Will u wait for me under that tree?" Mayraah ta kallesa tace "No, i will follow u" Ya hade rai yace "Kika san inda zan je?" tace "To me yasa baka son in ganta ne Yaya?" Yace "Ki ga wa?" Ta langwabar da kai tace "Warce zaka kai ma abincin mana" Yace "You are not serious" Er dariya tayi tace "Dama yaya kana da budurwa ashe?" Ya tsuke fuska yace "Yaushe na fara wasa da ke" Ta rufe bakinta bata sake cewa komai ba, suna isa department din yayi parking, wayar da zai yi ma sai da ya sauka daga motar sannan yayi, ita dai Mayraah murmushi kawai take tana bin sa da kallo, baza ta manta ba few months back Ammi ta dage wai ai Usman bai da budurwa, saboda taga shi baya kawo mata waya su gaisa da budurwan yanda Maheer ke yi, shkkn Ammi ta saka a rai ai bashi da kowa, ita kuwa Mayraah ta dage ma Ammi kan cewar yana da ita kawai dai saboda shi introvert ne shi yasa ake ga kamar ba shi da, still dai Ammi bata yarda da Mayraah ba a lokacin, Mayraah wished daga nan wajen Ammi zata je ta kai mata news din nan, tunanin nan yasa lokaci daya jikinta yayi sanyi, ta jinginar da kanta da kujeran motar tana tunanin wannan sabuwar rayuwar tata, knocking din da taji ana yi ta side dinta ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta fada, wata ta gani tsaye jikin motar tana mata murmushi, Mayraah ta bude motar tana kallonta, baza su wuce age mates ba da yarinyar, ita ma doguwa ce fara me kyau da ita, Mayraah ta sauko daga cikin motar tana mata murmushi kamar yanda yarinyar ma ke mata, yarinyar tace "Hi Mayraah, i am Maleeha, nice meeting you for the first time" Mayraah tace "Nice meeting you too Maleeha, ya lectures" Maleeha tace "Alhamdulillah, ya naki?" Mayraah tace "Same too" Maleeha tace "I have been longing in hadu dake sai yau Allah ya yi" Mayraah tace "Ai kam, i am happy to meet you" Maleeha tace "Barrister ya gaya min Nursing Science kike yi, ni kuma i am studying Biochem, final year student just as you" Mayraah tace "Maa sha Allah, Allah ya bamu sa'a gaba daya" Lokaci daya Mayraah taji tana son Maleeha har cikin ranta, Usman ya zagayo inda suke ya bude back seat ya ciro ledan da ya kawo ma Maleeha ya mika mata yace "Sai anjima" ta amshi ledan tana kallonsa, ya kalli Mayraah yace "Shiga mota mu tafi" Maleeha tace "Tunda i am done with lectures for today ka bar ta mana plss, so we can stay together, and know our selves better" Usman yace "Not today" Mayraah ta tuna fa yanzu dole gida zai ajiye ta daga ita sai Haseenah, bata san sanda tace "Ya Usman, i will stay... sai anjima zan tafi gida ba yanzu ba" Maleeha tayi murmushi tace "Anjima kawai zan sa drivern mu ya fara ajiyeta before dropping me home" Usman ya zaga ya shiga motarsa ya bar su nan a tsaye, ko minti goma bai yi da tafiya ba sai ga message dinsa ya shigo wayar Mayraah, ta bude message din tana karantawa kamar haka "Watch ur words" ta mayar da wayar cikin jakarta kawai, Mayraah bata yi regretting staying back tare da Maleeha ba cause she enjoyed both her company and her 2 frnds kuma dukkansu sa'aninta ne, bayan sun idar da sallahn asr a masallaci Mayraah ta ciro wayarta a jaka taga miss calls din Dr Musharraf har uku sai na Maheer biyu, wayar a total silence yake don haka bata jin kira sai dai ta ga miss calls kuma she like it that way, zata ajiye wayar sai ga kiran Maheer ya sake shigowa, tayi excusing kanta ta bar jakanta wajen Maleeha sannan ta fita outside of the mosque, a karkashin bishiya ta zauna bayan ta daga kiran, daga daya bangaren Maheer yace "Mimi me yasa baki responding to my calls?" Tace "Muna lectures dazu, yanzu kuma mun idar da sallah ne" Yace "Why did u leave home without waiting for me?" Tace "Saboda ban san sanda zaka tashi ba, kuma ina da lectures karfe takwas" Yace "Me yasa baza ki kira wayata ba, sannan kawai kin fita without taking breakfast" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Zan kawo maki abinci yanzu" Tace "Aa ni na ci abinci yaya" Yace "A ina kika ci abinci?" Tace "Ya Usman ya kawo min" Shiru Maheer yayi, can dai yace "Yaushe?" Tace "Da rana" Yace "When is ur lectures terminating?" Tace "Anjima" Yace "6 kenan?" Ta ɗan yi shiru sai kuma tace "Eh" Yace "Zan zo in dauke ki" Tace "Ya Usman will pick me" Yace "Ohk, is that so?" Tace "Haka ya ce min" Maheer yace "Ok" Daga haka ya katse wayarsa ta turo baki, Mikewa tayi ta koma cikin masallacin. karfe biyar saura Maleeha ta kira Usman to tell him za su yi dropping Mayraah ba sai ya zo ba, yace "No Maleeha, ina hanya zan zo in dauketa" Maleeha tace "Toh sai ka zo" Suna karkashin bishiya gaban department din nasu Usman ya iso, tuni driver din Maleeha ya zo makarantar amma tana jiran Usman ya fara daukan Mayraah kafin ita ma ta tafi, Maleeha ta raka Mayraah har bakin motar Usman, suka yi sallama, tana kallon Usman tace "I will be going home too, nagode sosai Barrister" Yace "Ohk, a gaida su Umma" Daga haka ya bar department din, bayan sun fita makarantar yana kallon Mayraah ya wani hade rai yace "Hope u didn't talk too much?" Ta kallesa ta wara ido tare da dafe kirjinta tace "Did i use to talk much yaya?" Yace "Look Malama stop being silly.... Maleeha is my frnd, she is just a frnd kar ki yi zaton budurwata ce or anything of such, kanwar abokina ce ita, so mun saba da ita ta dalilin Hafeez, but we are only frnds da ita" Mayraah bata san sanda tayi dariya ba tace "Ae dama na san she is ur frnd, and nima zata