Sashe 300
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
parlon ta wuce sama, Mayraah na kallon Dr Khalil a hankali tace "Ya Aunty Zainab fa?" Dr Khalil yace "She is fine Alhamdulillah, congratulations once more Mayraah, i am really happy for you with how things turn out" Mayraah ta sauke idonta cikin sanyin murya tace "I will forever be indebted to you Dr, i will always appreciate you in my life, bazan taɓa mance kulawarka gareni ba da kariyar da ka bani" Tana kai wa nan ta mike ta nufi hanyar da zai kai ta kitchen tana tafiya a hankali nan ko tunanin effort din Dr Khalil a kanta ta dinga yi tun farkon zuwanta Abuja har karshen zamanta ita kadai a Abuja, Dr Khalil ya kalli MD that is pressing his phone, kawai dai yayi murmushi bai ce komai ba, bayan wasu yan mintuna MD ya mike ya nufi hanyar kitchen din Dr Khalil ya ɗan buda ido ya bi sa da kallo.... Juyawa Mayraah tayi jin an bude kofar kitchen din tana ganinsa ta ci gaba da abinda take, ba tare da ya kalleta ba yace "Kar ma ki wahalar da kanki kiyi da nawa, i am not interested...." Ta bi sa da wani kallo ganin ya dau cup yaje yana wankewa zai yi making coffee da kansa, bata san sanda tace "To kai kafi kowa tsafta kake tunani ne?" Juyawa yayi ya kalleta calmly yace "Eh" Ta kyabe baki ta ci gaba da abinda take, ya gama dauraye daurayensa yayi making coffee ya nufi kofa, ta bi sa da wani kallo har ya fita, ta ci gaba da abinda take yi, bayan some minutes ta fita, ta kai ma Dr Khalil Breakfast dinning table, yana zaune area din tare da MD, Ta ajiye masa tana kallonsa tana murmushi tace "Dr ga breakfast, hope dai kai lafiyarka qlau?" Ya ɗan buda ido don bai gane abinda take nufi ba, MD ya ajiye coffee din da yake sha yana kallonta, ko kallonsa bata yi ba zata bar wajen taga wayarsa da ya ajiye yana vibrate, kallon screen din ta dinga yi ganin Dr Musharraf, daukar wayar tayi Dr Khalil ya buda ido yana kallonta da mamaki, bata tsaya wajen ba ta sauka parlor, sannan tayi picking call din kafin ya katse, ta bar parlon gaba daya, MD ya bi ta da kallo, muryar Musharraf taji yace "Good morning" Da kyar tayi gathering courage a hankali tace "Why did u decide to break your promise Musharraf?" Shiru Musharraf yayi bayan yaji muryarta, bata taɓa kiran sunansa ba sai ranan, ta shiga daki ta kulle ta fashe da kuka a hankali tace "I never expect this from you, shi yasa kaki barin mu hadu in maka magana ranan?" Calmly Musharraf yace "Mayraah, we should stop deceiving our self haka" Cikin rawan murya tace "How please?" Yace "Mu yi hakuri, ur parents have better plans for you and you know that wannan ne ma yasa ranan kika yi shiru a parlon baki ce komai ba" Mayraah that was confuse tace "Ban gane nayi shiru ba, me kake so ince a wajen? Kai ma ai ban ji kace komai ba" Yace "No problem, dama ba komai mutum ke nacin so yake samu ba a rayuwa, kuma Allah shi yasan dai dai....." Trying hard to control her self tace "So what are you insinuating now?" Yace "Look Mayraah, am not taking a second risk i promise, probability din samunki bai wuce 5% ba, sai zuciyata ta buga ko kin ga na fadi na mutu za ki san ina sonki da gaske? Wait kina tunanin da bana sonki zan ta ɓata lokacina ina ci gaba da bibiyarki after all that happened?" Mayraah ta dake tace "Amma ai kudin aurenka za a kai Adamawa yanzu haka, ni kuma wa kaga ya kawo kudin aurena? Tell me plsss" Musharraf yayi shiru bayan yaji abinda tace, bayan few seconds a hankali yace "Jiddah is my cousin sister, a rashin ki yasa na amince zan auri Jiddah ba don mun yi courtship ba, i need rest of mind Mayraah, bana son ciwon zuciya ya kamani at my young age..." Mayraah dake ta sauraronsa ta ɗan yi murmushi hawaye na sauka idonta tace "Is that so?" Yace "Yeah, where did u get my brothers phone, kuna tare ne?" Cike da karfin hali Mayraah tace "It is not necessary you ask me that" Musharraf ya ɗan yi murmushi, bayan few seconds yace "Let me be blunt to you Mayraah, ur foster parents plan is for you to marry one of their sons, baza su taɓa barin someone outside of their children su aureki ba, ni kuma ban ki idan Allah ya ƙaddara min ban aureki ba Yayana ya aureki ki dawo cikin mu, ur foster parent are being selfish, kansu kawai suka sani.... Why trying to manipulate you lallai sai kin auri daya daga yaransu? Suna tunanin ta haka ne kawai zaki biyasu rikon da suka maki? By all means suna nufin za su sake nisanta ki da mu dangin mahaifinki bayan kaddara ce ta hanaki rayuwa da iyayenki, me yasa suke da son kansu haka? Yau monday, gobe Tuesday, next Wednesday then Thursday za mu ga abinda zai faru a wannan rana, kuma a ranan zaki tabbatar da abinda na gaya maki yau" Kasa cewa komai Mayraah tayi tana jin duk abinda yake cewa zuciyarta na bugawa don bata yi expecting maganganun nan nasa ba, a haka taji ya katse wayar ta dinga kallon screen din wayar ko kwakkwaran motsi bata yi, hoton Mami ne jikin screen din wayar, Mayraah ta daga kai da sauri jin ana knocking kofar dakin, goge hawayen idonta tayi cike da karfin hali ta karasa bakin kofar, ji tayi gaba daya bata son wannan ranan alhamis din da Musharraf yace mata ya karaso don bata san me zai zo mata da shi ba a rayuwarta, har cikin ranta taji da ma a bar ta da wani batun aure a kyaleta kawai.