← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 158 OF 313

Sashe 158

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ur evidence via 07087865788 Musharraf na dakinsa bayan la'asar Maminsa tayi knocking, yasan ita ce but saboda damuwar da ya cika zuciyarsa ya ki tashi ya bude kofar, may be idan taji shiru zata yi tunanin bacci yake ta wuce kawai, continuously yaji take knocking din kofar, hakan ya sa ya ajiye wayar hannunsa da yake ta dialing number Mayraah amma switch off, ya mike ya nufi kofar ya bude yana kallonta bai dai ce komai ba, daga sama har kasa take kallonsa tace "Me kake yi a ciki nake knocking baka responding Musharraf?" Ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya yace "Kawai na kwanta ne Mami, i want to get some rest" Mami ya dinga kallonsa, ganin damuwar dake fuskarta yace "Is anything wrong Mami?" Ta karasa cikin dakin ya bi bayanta yace "Mami wani abu ya faru ne" Mami ta juya tana kallonsa cike da damuwa tace "I should be asking u that Musharraf, tell me what are you hiding from me? menene ke faruwa?" Musharraf ya shafa kansa yace "Me ke faruwa kamar me fa Mami, kin ga anyi wani abu ne?" Mami tace "You are not saying the truth, tell me kai da waye ku ke da matsala? Menene kake boye min?" Ya ɗan buda ido yace "Matsala kuma? I don't have issue with anyone" Mami tayi shiru still looking at him kafin tace "Then me yasa police officers suka zo gidan nan nemanka yanzu?" Kallonta ya dinga yi cike da mamaki yace "Police officers kuma? I don't understand" Mami tayi kasa da murya sounding so disturbed tace "Kar ka boye min komai don Allah son, me yake faruwa?" Musharraf yace "Wallahi Mami ban sani ba..." Bai sake cewa komai ba ya fice daga dakin Mami ta bi bayansa tana kiransa bai tsaya ba har ya sauka downstairs, ya nufi kofar parlor ya bude, wasu mutane uku ya gani tsaye dai dai bakin kofar parlon, daya daga cikinsu yace "Musharraf Abdallah??" Musharraf yace "Yes, how may i help you?" ID card dinsa ya ciro don dukkansu ba uniform bane a jikinsu, Ɗan sanda na nuna ma Musharraf ID card din yace "You are under arrest" Juyawa Musharraf yayi ya kalli Mami dake tsaye bayansa, trying all possible best to calm her down yace "U need not to worry pls Mami, it's not something serious, zan bi su mu je" Mami da hankalinta yayi mugun tashi bata ko kallesa ba balle ta sauraresa tana kallon officers din tace "Pls wani division din ne?" Wani officer ya gaya mata, ta juya ta koma sama da sauri don dauko makullin motarta da gyale, Musharraf ya bi yan sandan har kofar gida zuwa gun motarsu, babu wanda zai ce yan sanda ne don motar ma me kyau ce suka zo da shi, nan suka kama hanyar station tare da Musharraf. Maheer na zaune asibitin da aka kwantar da Haseenah wajen karfe biyar na yammacin ranan, she is responding to treatment don har ta fara iya cin abinci a hankali, amma fa tana jin jiki don fuskarta ya kumbura suntum saboda azaban bugun da kanta ya sha, tun da abun ya faru shi dai bai ga mahaifiyarta ta zo asibitin duba ta ba, danginta ne kullum ke sintirin asibitin su kawo mata wannan su kawo mata wancan, kuma ko sun zo basa ce ma Maheer komai, ko Aunties dinta idan ya gaishesu basa amsawa fuska a murtuke suke wucesa shi kam ko a jikinsa don duk ya kagu a sallameta a asibitin shi ma ya sallameta zuwa gidansu don har ransa yasan bazai iya zama inuwa daya da Haseenah ba kuma, shi mamakin ma yanda aka yi har ya auri Haseenah yake kamar wanda aka yi ma rufa ido, ko da yake baka sanin halin mutum ai sai ka zauna da shi dama, he regret knowing her har suka kai ga aure, yana zaune haraban hospital din yayi nisa tunanin da yake don shi har a sannan gani yake Mayraah na gun Musharraf, infact bai ma yarda bata wajensa ba, few minutes ago Abba ya kirasa ya sanar masa anyi arresting Musharraf, so kawai yana jiran Abba ya sake kiransa yace masa Musharraf yayi admitting Mayraah na wajensa, yana wannan tunanin kiran Abba ya shigo wayarsa, da sauri ya daga, Abba yace "Akwai wanda ke tare da matar taka a asibitin ne ka taho Miller road ka sameni yanzu?" Maheer yace "Miller road, Ina kenan a nan Abba?" Abba yace "I will send you the full address" Maheer yace "To" Shi fa duk tunaninsa Abba baya kano da bai gansa a gida ba, though ya dai lura kamar Hajiya Amina ma bata can gida amma he was thinking tare Abba ya tafi da ita, mikewa yayi don Aunties din Haseenah na ciki tare da Haseenar ya shiga motarsa ya bar hospital din, address da Abba ya tura masa ya bi har dai daga karshe ya ga kansa a wani hadadden layi na manyan masu kudi, don duk gidajen wajen hadaddu ne na karshe, yayi parking a number gidan da Abba yace yayi parking yana kallon gidan wondering whose house Abba yace ya zo, bude gate din gidan aka yi bayan ya kira Abba ya sanar masa ya iso kofar gidan, ganin haka ya shiga ciki yayi parking, a compound ya tarar da Abba tsaye waiting for him to come in, ya sauko daga motar Abba yayi leading dinsa har zuwa babban parlon gidan shi dai Maheer na ta mamaki yana bin gidan da kallo, Maheer na shiga lafiyayyen parlon ya zauna yana kallon Abba yace "Abba whose house is this?" Abba yace "Gidana ne" Da mamaki Maheer yace "Gidanka kuma Abba? Gidanka?" Maimakon Abba ya basa amsa sai cewa yayi "Yanzu kawun nan matar ka suka bar nan, her paternal and maternal Uncles" Nan da nan mood din Maheer ya canza, Abba yace "Sun zo sun bada hakuri akan abinda ya faru...." Maheer ya girgiza kai trying his possible best to be calm yace "Abba gaskiya bazan iya ci gaba da zama da ita ba....." Abba yace "Maganar banza ma kake kenan, ni zaka mayar karamin mutum? Meye dalilin da baza ka ci gaba da zama da ita ba, anyi abinda yafi haka ma an koma an ci gaba da zama balle wannan abun da ya faru duk kwamacalar mata ne da haukan mata" Maheer ya kalli Abba cike da damuwa yace "Abba wai kaga abinda sisters din mahaifiyarta suka yi ma...." Abba ya dakatar da shi yace "Bana son jin komai, dama su mata ai abinda yafi haka ma za su aikata don haka babu ruwana da wannan batun, har mahaifiyar yarinyar yanzu sai da ta kira suka bani waya tace ayi hakuri, ta kuma ce za ta zo har gida ta bada hakuri sannan ita ma kakar taku zata je ta bata hakuri, kaga wannan na nuni da iyayen nata ma ba kananun mutane bane ai, balle ko da basu zo bada hakuri ba ban ga dalilin da zaka saketa ba, ita da ma aka ji ma mummunan rauni take asibiti..." Maheer ya dake yace "Amma Abba...." Abba ya dakatar da shi again yace "Maheer bana son gardama, a lokacin da aka ce maka ka dauke Mayraah daga gidanka ai baka yi gardama ba, sai nine ka raina? Wato ni ban isa in gaya maka ba" Maheer bai sake cewa komai ba ya jinginar da kansa da kujera yana jin zuciyarsa ba dadi, shi duk zatonsa a kan Mayraah Abba ke kiransa, ya zata an gano inda take ne shine Abba yace ya zo anguwan ya dauketa, ashe kawai bacin rai zai zo ya ji, Dai dai nan Hajiya Amina ta sauko downstairs Maheer ya dinga kallonta babu ko kiftawa, ta karaso parlon tace "Sannu da zuwa Maheer" Ya sunkuyar da kansa yace "Ina wuni" Tace "Lafiya lau" Sai kuma ta kalli Abba tace "Alhaji ya ake ciki, kun sake waya da yan sandan ne?" Abba yace "Sun ce inyi expecting call dinsu ko zuwa nan da magrib, so ina jira in sha Allah" A hankali Hajiya Amina tace "Toh Allah ya sa a dace" Daga haka ta juya ta koma sama, Maheer felt so bad at what he saw, wato dauko matar nan Abba yayi suka dawo nan suka bar Ammi ita daya a can gidan, lokaci daya duk jikinsa yayi sanyi damuwan suka taru suka cunkushe masa a zuciya, ga na Mayraah, ga Haseenah da Abba ke cewa lallai sai ya zauna da ita, ga kuma halin da Amminsa ke ciki, ga Abba na neman kaurace mata, cikin sanyin jiki ya mike yana kallon Abba, Abba yace "Mu je ka duba gidan, i finished it few months back ban dai gaya maku bane kawai" Maheer ya dake yace "Sai na sake dawowa Abba, babu kowa a asibitin, zan koma ne" Abba yace "Ohk, nima ina jiran kiran yan sandan ne idan sun kirani naji yanda ake ciki na dan samu nutsuwa to zan zo asibitin da Hajiya Amina ko zuwa bayan isha ne in sha Allah" Maheer ya ki ce masa komai ya nufi kofa zai fita, can kuma dai ya juyo yayi gathering courage yace "Abba ina ɗan son za mu yi magana in babu damuwa" Abba ya mike yace "Okay" Can babban compound din gidan suka fita, Maheer na kallon Abba yayi kasa da murya cikin ladabi yace "Amma kayi hakuri in maganata zata ɓata maka rai Abba, Abba i don't think Ammi deserves this from you...." Abba ya dakatar da shi yace "Ni nayi deserving abinda ta min? Ni nayi deserving walakanci da rashin mutuncin da ta min wanda gashi yanzu a sanadin selfishness dinta ban san whereabout din Mayraah ba? Maheer let me be frank with you, for now I can't withstand the sight of ur mother billahi, albarkacinku kawai ta ci ban ce mata kar ta sake dawo min gidana ba, tayi failing dina ta yanda bana tunani, assuming the issue is just between us bazan wani damuwa ba, amma ta jefa rayuwar yarinya karama a halaka, ko da ace yanzu Mayraah na gun shi saurayin nata da muke zargi mahaifiyarku bata cuceta ba? Don't forget ta dalilinta Mayraah ta samu guts din zuwa gidan saurayi for days now, duk ita ce silar
Chapter 158 · 0% Book details