← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 222 OF 313

Sashe 222

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

komawa nasa office din ya kalli Mayraah yace "You can go to his office, but plss Mayraah be a good girl, kiyi abinda ya kamata he is our boss, and he is employing you, speak to him with respect and calmness, kalmominki kar su wuce Yes sir, Ok sir, sorry sir, thank you sir" Murmushi Mayraah tayi tana kallonsa ta rasa dalilin da zai dinga cewa she should be a good gal in zata je gun jarababben mutumin can, to tayi kama da bad girl ne? Ta sunkuyar da kai tace "Toh Dr" Yace "You can go now, yana jira" Mikewa tayi ta dau jakarta da Envelope din takardunta, ga cire glasses dinta zata saka a jaka, Dr Khalil yace "Me yasa kika cire, ki maida abun ki" Mayraah ta kallesa yace "Ki sa mana, ai ya maki kyau" Ɗan murmushi tayi ta maida glasses din sannan ta nufi kofa, har ta rike handle din sai kuma ta juyo tana kallonsa a hankali tace "But do u have any idea akan abinda zai tambayeni" Dr Khalil yace "Ki kwantar da hankalinki and be calm, ba wani tambayar da zai maki na sani, kawai zai duba takardunki sai kuma ya tambayeki informations dinki to be imputed, yana ganin result din ki ma nasan sai ya rasa tambayar da zai maki don mamaki.... So just go" da murmushi ya kare maganarsa, Mayraah ta sauke idonta kasa ta juya ta fita daga office din, last floor ta tafi zuwa office din MD, gently tayi knocking kofar har sai da ya amsa sannan ta bude ta shiga, Coffee dinsa yake sha bai kuma daga kai ba balle ya kalleta, ta karasa har gaban table dinsa ta tsaya calmly tace "Good morning sir" Dago kai yayi, kiris ya rage ya saki cup din coffee din hannunsa don har sai da ya ɗan zube masa a white shirt dinsa, mikewa yayi da sauri ya ajiye cup din yace "Kee, why will u just badge into my office are you okay? Ance maki kasuwa ne nan?" Bai jira me zata ce ba ya shige Bedroom dinsa dake office din, Mayraah ta bi sa da kallo, can ta taɓe baki a ranta tace kilan dai Dementia garesa, cause sai da tayi knocking ya bata permission din shigowa kafin ta shigo, tana ta tsaye har ya fito bayan minti biyar with another white shirt, ya wani daure fuska kamar bai taɓa ko murmushi ba, ita dai bata yarda ta kallesa ba har ya karaso table dinsa ya dau cup din coffee din ya tafi ya zubar ya dawo, still yaki kallonta yace "Me kike jira har yanzu?" Calmly tace "I came for the interview u ask me to come for, here are my credentials" Bata jira me zai ce ba ta ajiye envelope din kan table dinsa sannan ta koma gefe ta tsaya, yace "Ohk shi Khalil din ne yace maki kina zuwa ki ajiye CV din kan table dina?" Mayraah bata ce komai ba, ta dau envelope din ta nufesa ta tsaya a gabansa tana mika masa while looking at him, ƙin yarda ya kalleta yayi may be he wasn't expecting that, kawai taga ya bar wajen ya koma seat dinsa ya zauna, ta juya tana kallonsa still ya ki kallonta, kwankwasa office din aka yi, ya mike da sauri duk tunaninsa Ceo ce, Dr Balogun ya bude office din ya shigo da wani file, yana ganin Mayraah yace "Ohh Madam, where have u been all this while?" Mayraah ta gaishesa da ladabi, ya amsa da hausansa irin na yoruba yace "Kwana biyu baki zo aiki ba, ina kika tafi?" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "Ya ce in zo interview ne tukunna kafin in ci gaba" Dr Balogun ya kalli MD that was unnecessary clearing stuffs off his table, Dr Balogun yace "Ohk MD in je in dawo kenan after the interview, dama akan aikin da za mu yi da daddare ne..." Sai a sannan MD ya daga kai a takaice yace "You can interview her Balogun, i am a bit busy...." Dr Balogun ya kalli Mayraah yace "Are you with ur CV?" Ta gyada masa kai ta mika masa Envelope din hannunta, zaunawa yayi kan kujera ya nuna mata kujeran dake kallon wanda ya zauna yace "Sit..." MD yace "Why should she sit? She should take off those glasses we are not doing fashion here" Dr Balogun ya kalli Mayraah da ta cire glasses din idonta, sai kuma ya fara fiddo da takardun, Mayraah ta wani harari MD dake kallonta ta gefen ido, Statement of result dinta Dr Balogun ya fara dubawa, sai kuma ya kalleta da sauri yace "Waow, first class from this prestigious university? It's my alma mater also, nasan lecturers dinku sosai" Mika ma MD yayi, MD dake kallonsa yace "First class in Botany or what?" Dr Balogun ya zaro ido yace "Nursing Science Malam, ina jin fa department din nan rabon da a fita da first class zai kai shekara sha biyar ko ma ya fi, and she just graduated" MD dake ta kallonsa yace "Nursing Science?" Dr Balogun yace "Gashi ka duba" MD ya girgiza kai yace "Wani makaranta ne?" Dr Balogun ya gaya masa, MD yace "That's a lie" Da mamaki Dr Balogun yace "Ka taɓa ganin anyi forging result a makarantar nan?" MD ya dau wayarsa yace "I have a frnd that is a Lecturer in the department, i will confirm it now" Shiru Dr Balogun yayi yana kallon MD da ya amshi result din yana dubawa sannan ya dau wayarsa ya fara dannawa, Ita dai Mayraah ko kallon inda yake bata sake yi ba, har cikin ranta bata taɓa jin ta tsani mutum irin yanda take jin tsanar mutumin nan ba, she detest him with passion, ji take kamar ta fice daga office din amma bazata yi haka ba sbda Dr Khalil, tana ta jiran taji ya kira wayar sai kuma bai yi ba, ya maida wayar ya ajiye yace "I will confirm that later, Dr Balogun you can leave, we will discuss the issue at hand later" Mikewa Dr Balogun yayi, har sannan kallon Mayraah yake don ko kadan bai ji shakkan result dinta ba, bayan fitar Dr Balogun ya jawo laptop dinsa after some minutes ba tare da ya kalleta ba yace "Ur name?" Sai a sannan Mayraah ta kallesa, a takaice tace "Mayraah Mahmud" Ya hade rai ya kalleta yace "Kee sunanki zaki gaya min ba sunan gayunki ba, ko an gaya maki wajen wasa ne nan?" Tace "U can check the name in my result for ur self" ita kanta bata san sanda ta gaya masa haka ba, ya dinga kallonta, kawai ya rufe laptop dinsa yace "Get out" Bude office din aka yi Ceo ta shigo, ya mike da sauri yace "U need something Ma?" Karasowa ciki tayi tana kallon Mayraah cikin sanyayyen muryarta tace "Hello, how are you, i just asked of u not long ago" Mayraah ta gaisheta da ladabi, MD dai kallonsu kawai yake, Ceo tayi mata side hug, sosai gaban Mayraah ya fadi, Ceo na kallonta with calmness tace "Why are you not on scrub?" Mayraah ta kasa kallonta tace "I..." Sai kuma ta rasa me zata ce, Ceo ta kalli MD tace "Is there anything?" Da sauri yace "No, not really, just adjusting some mistakes in her data.... She is not on duty today" Ceo tayi murmushi tana kallon Mayraah a hankali tace "If he is done, Come make me coffee in my office Mary Ann" Mayraah ta gyada mata kai tace "Ok Ma" Daga haka ta ajiye takardun hannunta ta juya ta nufi kofa, Mayraah ta bi ta da kallo babu ko kiftawa, juyawa tayi suka hada ido da shi, lkci daya ya mike ya dau wasu textbook zai kai Library dinsa na office din, tace "Can i take my leave?" Wani shegen kallo ya jefa mata, hakan yasa ta fara kokarin tattara takardunta yace "Hey get out" Juyawa tayi ta bar takardun ta fita daga office din.....
Chapter 222 · 0% Book details