← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 198 OF 313

Sashe 198

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ta hango gold rosary din dake makale wuyarta, Ceo tace "But she left so soon, Amina died 7 years ago, har yau har gobe ina jimamin mutuwar Amina da nake jinta kamar er uwata, her in-laws sent her to her early grave, they made marriage life difficult for her, they shattered her, har yau mijinta na nan Abuja" tissue din dake saman table dinta ta zaro tana share hawayen cikin idonta, jikin Mayraah yayi sanyi tana kallonta a hankali tace "Sorry about that ma'am" Ceo tayi murmushi tace "Thank you, zan hada ki da yaranta in sha Allah, i know they too will attest that u have a resemblance with Hajiya Amina, Abbakar is in Uk, Yusuf is in India, and Maryam is married in UK also, but they are all adopted, she adopted them tun suna yara from orphanage, ita Allah bai bata rayayyun 'ya ya ba, it's always one thing or another" jikin Mayraah yayi sanyi sosai ta kasa ce ma Ceo komai, har cikin ranta taji tana son tasan wa enda suka san Hajiya Aminar nan, a hankali tace "Don Allah zaki hadani da yaran nata?" Ceo na murmushi tace "Sure i will... You can leave now, tell MD to come over with the phone i took to him" Mikewa Mayraah tayi tace "Thank you Ma" Daga haka ta nufi kofa Ceo ta bi ta da kallo har ta fita ta kulle mata kofar. office din Dr Khalil ta nufa duk jikinta a sanyaye, ya ajiye wayarsa da yake ta kiran Ahmad yaki dagawa saboda yasan abinda ya aikata, ya mike yana kallonta bayan ta shigo ganin yanayinta yace "Ya ku ka yi da shi?" Mayraah ta zauna tace "Ka kirasa kace masa tace ya kai mata waya" Dr Khalil yace "Kin je office din nata ne?" Gyada masa kai tayi, yace "Shi ya turaki?" Ta girgiza kai tace "Ta sameni ne a office dinsa" zagayowa yayi ya dawo inda take yace "To ya ku ka yi da ita?" Mayraah tace "Kawai ta nuna min hoton matar da tace ne" Yace "Kuma kinga kuna kama?" Ta daga kai ta kallesa tayi masa nodding kawai, Dr Khalil yayi shiru with different thoughts running his mind kamar yanda ita ma tunani iri iri ke yawo a ranta a lkcn, can yace "Tace zata hada ku ne?" Nan da nan hawaye ya cika idon Mayraah a hankali tace "Ae tace ta rasu" buda ido yayi sosai, can yace "To yaranta fa?" Mayraah na goge idonta tace "Tace zata hadamu" Khalil yace "Ita matsalarta shiririta ta da shauninta yayi yawa, yanzu tana iya kama hanya in ta tafi sai bayan shekara za mu ganta a kasar nan" Mayraah dai sai kallonsa take, yace "Amma ki kwantar da hankalinki kafin ta koma dai in tana ganin ki she will be remembering definitely" Mayraah tayi shiru, sai kuma a hankali tace "Zan wuce gida" Yace "Wani gida?" Ta daga kai ta kallesa, ya sauke idonsa yace "Zaman kan naki zaki koma Sulejan ki ci gaba da yi?" Ta wani kallesa, calmly yace "Mayraah" shiru tayi bata amsa masa ba, yace "Kamar yanda nace maki jiya, it's high time ki koma gida yanzu, you've given them enough space nasan yanzu komai ya daidaita in sha Allah" Mayraah ta girgiza kai tace "I will go back when i know it's right to do so" Da mamaki Dr Khalil yace "Abinda Ahmad yayi maki har yanzu bai zame maki darasi ba kenan, to let me tell you, ba Ahmad ba kowa ma kallon da zai maki kenan, don duk mace me mutunci ko gunduwa gunduwa da namanta iyayenta ke yi baxata bar gabansu ba, kuma duk warce kika ga ta bar gida ta tafi wani gari to babu wanda ya isa ya canza kallon er iskan da mutane za su dinga mata, ba ga su nan muna gani a Abuja ba sun tsallake sun bar gida sun dawo nan suna ta iskancinsu" Mayraah ta mike tace "Ni ai Allah ya san ba iskancin nake ba, kuma ban ce bazan koma gida ba, amma sai idan ta hadani da family din matar da na gani a hoto" Dr Khalil yace "Ai ko kina gida za a iya hakan, beside iyayenki na samun labarin kin samu aiki permanently a asibitin nan i know they will support u ki ci gaba da aikin ki, cause kowa yasan asibitin nan a kasar nan, it's ba privilege working here...." Mayraah tace "I will think about that" Dr Khalil yace "Kinsan menene matsalarki Mayraah?" Mayraah tayi shiru tana kallonsa yace "Taurin kai" Zata yi magana aka bude office din duk suka juya, MD ne tsaye bakin kofar, Mayraah ta kauda kanta tana kallon Khalil tace "We will continue on phone" Daga haka ta dau pack din burger dinta da jakarta ta nufi kofa ganin babu hanyar da zata wuce tace "Excuse me pls" Dr Khalil ya koma kujeransa ya zauna yana kallonsu yana murmushi, MD na mata wani kallo yace "Zan ƙwada maki mari, ni kike ce ma excuse you pls? Or are you harebrained?" Bata ko kallesa ba ta raba ta gefensa almost touching him tayi ficewarta a ranta kuwa cewa tayi sai dai ya ci kansa. MD ya juya ya kalli Dr Khalil a fusace kafin yace komai Dr Khalil yace "Kasan me Dr Aliyu? Har nayi picturing ka mace ma yarinyar nan kun fara soyayya da zai yi leading to marriage, it will really make sense, dama naga kamar yanzu baka da budurwa ko?" Yana kai wa nan ya fashe da dariya not minding MD's weird facial expression a lokacin. Mayraah na isa Suleja bayan tayi share sharen gidan don ta kwan biyu bata zo ba ko ina yayi ƙura, tayi wanka sannan ta dafa Indomie ta ci, tun jiya da daddare ta kulle sim card din da ta kira Musharraf da shi saboda yanda ya dinga kiranta, dauko wayar tayi kamar zata bude sim din kuma kawai ta fasa ta ajiye wayar, tana ta zaune dakinta maganganun Zainab na mata yawo a kai, making her feel so hurt a zuciyarta, kawai sai tayi murmushi tana goge hawayen da ya cika idonta, hoton nan da ceo ta nuna mata ne kawai ya jinkirta abinda tayi niyya a ranta yau, she really want to know who the woman in the picture is, amma da ta tuna Ceo tace mata ta rasu sai jikinta yayi sanyi sosai, Ahmad ne ya fado mata, ita fa ta dade bata yi mamaki irin mamakin abinda Ahmad yayi mata ba, to gani yayi tayi kama da yan iska ne ko kuma ya taɓa ganin tayi wani action da yayi kama da na iskanci? Har cikin ranta taji tana appreciating Dr Khalil kuma tana jinsa kamar Ya Maheer because he was there for her always, kiran azahar ya sa ta tashi taje tayi alwala, sai da tayi sallah sannan ta kwanta tayi baccin da bata samu tayi ba jiya. Bayan la'asar Mayraah na wanke plate din da tayi amfani da shi a kitchen taji ana knocking gate din gidan, so tari idan Maman Hanan ta lura ta dawo suleja ta kan shigo mata su yi hira, wani lokacin kuma daya neigbor dinta Harira ma na shigowa duk sanda suka ga ta dawo, Hijab dinta ta saka ta fita, tana tsaye jikin gate din gidan tace "Waye?" taji muryar namiji yace "Assalamu alaikum" Mamaki ne ya cikata, tace "Waye?" Yace "Baƙi ne ki bude gate din ki fito" Sosai gabanta ya fadi tace "Baƙi kuma? Ni bana expecting baƙi daga ko ina" Mutumin yace "Eh mu ma dalili ne ya kawo mu, bamu yi tunanin za mu zo anguwan nan yau ba" Kasa cewa komai Mayraah tayi don gaba daya ta tsorata, mutumin yace "To cut everything short don naga kamar kin tsorata, mu jami'an tsaro ne... We are not here to harm u Madam, amma idan kika ki bude gate din, we are sorry there is nothing we can do about it za mu bude gate din by all means" Mayraah that was so afraid tace "But what did u want from me?" Yace "Open the gate" ƙin budewa tayi ta koma ciki ta dau wayarta ta fara dialing number Dr Khalil a tsorace.
Chapter 198 · 0% Book details