← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 294 OF 313

Sashe 294

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

din ma zata sa a dawo da ita in lokacin dawowar nata yayi" Sosai gaban Mayraah ya fadi bayan taji abinda Abba yace tana kallonsa, Ammi dai kanta na kasa bata ce komai ba, Abba yace "Kin fahimci abinda nake nufi?" Ammi ta daga kai a hankali tace "Na gane" Abba yace "Hakan ya kamata, don haka Usman ko Maheer za su iya dropping dinta tomorrow in the afternoon" Ammi dai bata sake cewa komai ba, Abba yace "Kiran kenan dama" Mayraah na tsaye kitchen that same night tana dafa ma Ammi shayi ganin bata ci abinci ba taji an bude kofar kitchen din, juyawa tayi tana kallonsa har ya karaso cikin kitchen din yace "Are you making tea for Ammi?" Mayraah ta gyada masa kai, yace "Ohk, take ur time..." Juyawa yayi zai fita ta bi sa da kallo tace "Me zaka yi yaya?" Ya juyo yace "I want to make coffee" Tace "Okay let me make you" Yace "Thank you..." Kokarin fara making masa coffee din take, shi dai kallonta kawai yake, ta juya ta kallesa ya ɗan buda ido yace "Alas baki ci abincin nan ba dai Mama Ladi ta ci" Ta ɗan ɓata fuska tace "Ba nace ka kawo min daki ba ka ki kawo min" Yayi murmushi yana shafa beard dinsa yace "Bayan masifar da kika min na tashe ki bacci" Buda baki tayi tana kallonsa, ya karasa ya kashe gas din da shayin da take yi ma Ammi yake kai, ta nufesa tace "Yaya yaushe na maka masifa?" Ba tare da ya juyo ba yace "Cikin mafarki, har da murguda min baki" Daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita kitchen din ya kullo kofar, haka dai ta zuba ma Ammi shayin a karamin flask, sannan ta gama yi masa coffee din, zata fita kitchen din Usman ya shigo tana kallonsa ta mika masa flask din hannunta a hankali tace "Yaya pls ka ɗan taya ni kai ma Ammi upstairs" Yana kallon coffee din hannunta yace "Wancan kuma na waye?" Tace "Yaya" Yace "Ke bakya differentiating yayas din, which of the Yaya" Murmushi tayi tace "To kace in maka coffee ne? Beside ai kai baka shan coffee ai naga" Ya ɗan buda ido yace "Sai kice min Doctor" Daga haka ya amshi flask din hannunta ta fita daga kitchen din, ya dau cup ya tafi sama zuwa bangaren Ammi dama daga can din yake, Mayraah na zuwa kofar dakin Maheer tayi knocking a hankali, sannan ta bude kofar ta shiga, har ya sa Pajamas dinsa zai kwanta ta karasa ta ajiye masa Mug din tace "Gashi Yaya" Yace "Ohk thank you" Ta daga kai tana kallonsa sai kuma ta marairaice tace "Yaya yaushe na murguda maka baki?" Maheer ya ajiye wayar hannunsa yace "Kin kai ma Ammi shayinta?" Ta turo baki tace "Ai ba ruwan ka da wannan kuma" murmushi yayi yace "Tunda haka kika ce let me go and check for my self" Yana fadin haka ya mike ya nufi kofa ta bi sa da ido, tana ta durkushe inda take bayan fitar sa, can ta mike ta dau Coffee din da ta ajiye masa ta fita daga dakin ta koma kitchen ta zubar a sink ta wanke mug din ta kife sannan ta fita daga kitchen din ta wuce sama, a stairs ta hadu da shi yana saukowa, taki kallonsa zata wuce ya ɗan bi ta da kallo, can yace "Mimi" Ta ki juyowa balle ta tsaya, hakan yasa ya kamo hannunta yace "Are you angry?" Kamar jira take ta fashe da kuka, ya zaro ido yace "Me kuma ya faru Mimi?" Taki cewa komai tana kuka sosai, ya jawota kusa da shi yana bin ko ina na stairs din da kallo, sai kuma ya daura kanta saman kirjinsa a hankali yace "Ohk, i am sorry...." Muryarta na rawa tace "Ni yaushe na maka masifa na murguda maka baki?" A hankali yace "A dakin ki mana, yanzu ma a dakina ai kin min" Ta daga kai hawaye na zuba idonta tana kallonsa, ya ja dogon hancinta yana murmushi yace "Baki san kin yi ba ko?" Sauke idonta tayi tana tunani, sai kuma ta fara sabon kuka tace "To me nace maka ka tuna min" Getting her more closer to himself yace "Shikenan, ya wuce...." Muryar Usman suka ji duk suka juya da sauri, Mayraah ta matsa daga kusa da Maheer, yana tsaye jikin rail din stairs din supporting himself with his hands yace "Ammi's wrapper or Aunty Mariya's Wrapper?" Maheer that was confuse yace "Wrapper?" Usman yace "Eh, wai ka goyata yanda zata ji lallashin da kyau mana tunda bata da aiki sai kuka" Turo baki Mayraah tayi tana kallonsa kamar zata fashe da kuka, Maheer dai ɗan murmushi kawai yayi ya fara sauka downstairs, Usman yace "Silly gal" Daga haka ya juya ya bar wajen, Mayraah ta bi Maheer da kallo sai kuma ta bi sa downstairs da sauri tace "Yaya na fa shanye coffee din sai dai in maka wani" Ya juya yana kallonta yace "Kin dai zubar Mimi" Ta zaro ido tana kallonsa, sai kuma da sauri tace "Ba wani nan, let me make u another one in just 2 minutes" Yana ci gaba da tafiya yace "Tun da kika zubar kawai kije ki kwanta don't bother ur self" Ta marairaice tace "Plss ni dai bari zan je in maka wani" Still bai juyo ba yace "Kwanciya zan yi, kawai ki bari tun da kin zubar" Tsayawa tayi ta bi sa da kallo har ya wuce dakinsa ya kulle, a hankali ta juya ta wuce sama lkci daya duk jikinta yayi sanyi, sai tayi da ta sanin zubarwan da tayi. Washegari da safe wajen karfe goma da rabi Ammi ta shigo dakin Mayraah, ta zauna gefen gado tana kallonta a hankali tace "Mimi ki hada kayan naki, in kin gama sai ki zo in gyara maki gashinki" Mayraah ta sunkuyar da kai ta kasa cewa komai, Ammi ta mike tace "Be careful kar ki manta komai" Daga haka ta nufi kofa Mayraah ta bi ta da kallo har ta fita, nan da nan hawaye ya cika idonta, sai bayan kusan minti talatin ta mike ta fara hada kayan nata a akwati, bayan ta gama ta fita, tana tafiya a hankali ta nufi part din Ammi, sai kusan azahar Ammi ta gama yi mata gyaran gashin, Ammi na kallonta tace "Kije ki fara cin abinci sai kiyi wanka kiyi sallah...." Mayraah tace "To Ammi" Mikewa tayi ta nufi kofa, Ammi ta kalli Usman da shigowarsa kenan a hankali tace "Wa zai kai ta?" Usman yace "I will drop her" Ammi tace "Ohk, zuwa karfe uku sai ku tafi" Yace "In sha Allah" Kamar yanda Ammi tace karfe uku Usman suka bar gidan tare da Mayraah, ko sallaman kirki Ammi bata iya tsayawa sun yi ba ta shiga dakinta, tun da suka baro gidan Mayraah ke hawaye, lkci lkci Usman ke kallonta yana driving dinsa, can ya ɗan yi murmushi a hankali yace "Ke da za ki yi aurenki ki koma Familyn Dad dinki shine za ki fara kuka tun yanzu" Mayraah ta kallesa da idanuwanta da suka yi ja bata taɓa tunanin akwai ranan da zai zo a kira wani ba Abba ba da Dad dinta, Usman yayi kasa da murya yace "Mimi zaki yi aure kiyi nesa da Ammi da mu kanmu gaba daya, may be say once in a blue moon za mu dinga ganin ki" Mayraah dai sai kallonsa take, Calmly yace "Gradually bond din mu zai ragu, daga karshe ma ya zama tarihi.... that beautiful bond of 22 years.... gradually za ki mana nisa and we will have no lil sis to look upon, Ammi will have no daughter to show to the world anymore" Mayraah na share hawayen dake zuba idonta ta ɗan yi murmushi tace "You think so yaya?" Shi dai bai ce mata komai ba, ta girgiza kai cike da karfin hali kar ta fashe da kuka tace "Har cikin zuciyata nasan bani da familyn da za su fi min ku a duniya, a cikinku na taso na ga kaina, nothing can ever change the fact that ku ne family members dina a ko da yaushe, and i am sorry to say any other family member will only be a counterfeit" Usman yace "I need a favor from you Mimi, nasan tunda mu ke ban taɓa tambayarki wani abu ba sai dai ke ki tambayeni ko?" Mayraah ta juya tana kallonsa, haka kawai taji gabanta na faduwa ta rasa dalili, yace "Bazan samu favour din ba kenan" Ta hadiye abu da kyar tace "Zaka samu in sha Allah" Yace "Ohk bari in samu waje in tsaya sai mu yi magana" Mayraah bata sake cewa komai ba gabanta dai sai faduwa yake, har dai ya samu wajen wani siyar da Ice cream me kyau ya shiga yayi parking, ya juya yana kallonta yace "Let go in" Bata iya ta ce komai ba ta bude motar ta sauka kamar yanda shi ma ya sauka, tana biye da shi suka shiga cikin wajen, direction din da babu kowa ya nufa Mayraah ta bi sa har ya nemi waje ya zauna ita ma ta zauna, yayi order din masu ice cream duk da he is not a fan of ice cream, ita dai Mayraah ta kagu taji wannan favor din da yake so daga gareta, yana facing dinta gently yace "Mayraah" Ta daga kai da kyar tana kallonsa cikin karfin hali tace "Na'am" Yace "Tell me a little about Yaya Maheer" At this point Mayraah was confuse, tana kallonsa tace "Ban fahimta ba"
Chapter 294 · 0% Book details