← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 202 OF 313

Sashe 202

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

rashin cin abinci da wadatattcen bacci da kika janyo mana" Tuni Ammi ta kama hannun Mayraah suka bar wajen, Mama Ladi ta bi bayansu still. Tun da Mayraah ta shigo parlon Ammi take kallon Badiyyah dake kwance kasa tayi wani bakikirin kamar bata taɓa haske a rayuwarta ba ga wasu uban kuraje da suka cika mata fuska, Mayraah ta zauna kan kujera don Ammi da take son tambaya ko Badiyyar bata da lafiya ne tuni ta fita daga parlon, kasa daurewa Mayraah tayi tana kallon Mama Ladi tace "Mama bata da lafiya ne?" Mama Ladi tace "Wa? Wai Badiyyah? Ai Badiyyah cikin shege tayi in baki labari Mera, cikin shege dai da kika sani" Tsabar shock Mayraah bata san sanda ta mike tsaye ba, Mama Ladi tace "Aa koma ki zauna ba wani batun rikicewa don kema bamu san daga inda kike ba yanzu haka" Mayraah ta dinga kallon Mama Ladi babu ko kiftawa, Mama Ladi na kakkabe kujeran da taga Badiyyah ta zauna dazu tace "Hajja dai in gaya maki ta sallama ma duniya Badiyyah tace ko sunanta aka kira mata bata yafe ba, ta mata Allah ya isa yafi cikin kwando, ko ido suka hada sai ki ga Hajjan ta fara tari kamar zata shide yanzu haka zancen da nake maki Hajja tana can gidan Yahanasu a kaduna, sai kin ga gidan ko kiwon kare baza ayi a gidan nan ba don sai cuta ta kama karen ya mutu a banza, ni dai tun da na rakata ko minti sha biyar banyi cikin ɗan kuturun gidan ba na gudu gidan Mariya tunda dai abinda ya faru ba wai ya shafeni bane kawai zumunci nake dubawa, banda ma na kai zuciya nesa ai da sai dai ki dawo ki ga na canza wani pamilyn, don wannan pamilyn namu dai ba pamilyn nuna ma duniya bane, pamilyn mu ya zama barbadadden pamilyn, Badiyyah ta lalata mana Pamily kawai sai dai muce Allah ya isa, gidan Mariya da na gudu in samu sauki can kuma yanda kika san kasuwar kurmi tunda babban gida ne uwar mijin da uban mijin duk suna ciki da bataliyarsu, wannan karen ya shigo, wancan dokin ya fita haka dai abun ba tsari, ke in takaice maki washegari da asuba nasa aka kaini tasha na hau mota na dawo kano inda na fi wayo, to shine sabida rashin tsoron Allah aka makala ma baiwar Allah Ammi Badiyyar take ta fama yanzu haka, banda ma Mamudan mutumin kirki ne ina zai yarda wannan annobar ta zauna masa gida ta lalata masa tarbiyyar yaransa maza, ai da muna da yan uwa a kauye kyan Badiyyah kawai a turata can har sai ta haihu ta zauna tayi renon shegen a can, to bamu da kowa a kauye, Mamudan ma fa da farko kin amincewa yayi yace a fitar masa da ita daga gidansa, to kin dai san Abban naku da shegen tausayi ga kuma tausayin matarsa da yake, a haka dai daga karshe yace a kyaleta ta zauna amma ko nan da gate baya son ta je kada yan anguwa su sa shi a bakin duniya suce ga me cikin shege a gidansa, kiri kiri Mariya taki tafiya da ita aka bar Ammi da wahala, Allah dai ya isa kawai" Mayraah sai kallon Badiyyah da hawaye ke sauka idonta kawai take, kullum sai tayi kuka kamar ranta zai fita a gidan saboda Mama Ladi, da kyar ma in Mama Ladi bata daura mata depression ba saboda bad mouth dinta, Mama Ladi tace "Don haka kike baya baya da ita, mu ma duk baya baya muke da ita gaskiya, mu a zamaninmu idan mutum yayi cikin shege ma rataye kansa kawai yake ya mutu, ko kuma ya gudu ya bar garin sai bayan shekara hamsin, to ita kinga ai taki yin ko daya" Bude kofar parlon aka yi Ammi ta shigo da breakfast ta kawo ma Mayraah, ko bata bude baki tace komai ba kasan tana cikin farin ciki mara misaltuwa, she looks so happy wanda duk wanda yasanta yasan rabonta da wannan farin cikin an kwana biyu, Usman really took she and Maheer unaware don duk abinda yake yi bai gaya masu ba, Mama Ladi ta bi ta da kallo har ta ajiye tray din hannunta tana kallon Mayraah tace "Taho ki karya daughter" Mama Ladi ta rike haɓa tace "Yanzu tun safe in tashi ko ruwan shayi da ke da shegiyar sabuwar me aikinki baku bani ba sai wannan mata da bamu san daga inda take ba zaki kawo ma tray guda na kumallo jikinki na ɓari? Ni da na kwana gidan baki ban komai ba sai warce bata kwana ba?" Ko kallon Mama Ladi Ammi bata yi ba sai ma daukan tray din da tayi ta wuce dakinta da shi tace "Taho Mimi" Mayraah da duk jikinta yayi sanyi da halin da Badiyyah ke ciki ta share hawayen idonta ta bi bayan Ammi tana tafiya a hankali zuwa bedroom dinta. Ammi da kanta ta hada mata shayin ta debar mata komai sannan ta koma ta zauna tana kallonta, Mayraah ta daga kai tace "Ammi Abba fa?" A hankali Ammi tace "Na kirasa yana hanya" Mayraah ta dau shayin da Ammi ta hada mata ta fara sha, Ammi ta mike ta fita daga dakin zata je kai ma Mama Ladi nata breakfast din, Ammi na fita babu dadewa Maheer ya shigo dakin, Mayraah ta daga kai tana kallonsa har ya iso inda take ya duka yana kallonta, ta sauke idonta tace "In hada maka shayin kai ma?" Ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace "Ki rage min kawai" Tace "Sai mu sha tare..." Zaunawa yayi saman darduman yana facing dinta, bayan ta kurbi shayin hannunta ta mika masa, ya amsa ya kai baki, ita kuma ta fara cin irish din da Ammi ta zuba mata da ketchup da kwai, Ya ajiye cup din shayin bayan ya sha a hankali yace "Me yasa kika tafi Mimi?" Bata yarda ta dago kai ta kallesa ba cikin sanyin murya tace "That's bygone yayana" Ya gyada mata kai kawai still looking at her, bayan few seconds tace "Baza ka ci irish din ba?" Dauka yayi ya fara ci, ta dau cup din shayin ta sha kadan ta ajiye, daga kai tayi suka hada ido, yace "I missed you Mimi" Ta ɗan yi murmushi tace "I missed you more" A haka Ammi ta shigo dakin ta samesu, Ammi na kallonsa tace "Ba ga can naku an kai maku ba?" Mayraah ta kalleta tace "Ammi ni ce nace ya ci" Shi dai murmushi kawai yayi, Ammi ta zauna gefen gado still looking at them.
Chapter 202 · 0% Book details