← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 249 OF 313

Sashe 249

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da farko rikicewa yayi, ya kwantar da ita da sauri ya fara mata CPR a kirjinta with every of his strength dan bai san for how long pulse dinta ya tsaya ba, dai dai nan Maheer ya shigo dakin after running all the way from the chalet, zuciyarsa na bugawa ya karaso kusa da su ya durkusa ya dafe kansa yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" MD was doing all his possible best to revive her pulse.... Haseenah na makale jikin window taki fitowa sai zare ido take tun bayan da Bilkisu ta zo tana kuka ta kira Maheer, she doesn't even know weda she should be happy or otherwise, duk da ba haka ta so ba, har kasan ranta tayi bakin ciki da ba Maheer bane ya ci abincin nan, amma Mayraan ma dai da ta ci Allah Ubangiji ya sa ta mutu kawai, addu'ar da ta dinga yi kenan feeling no epitome of remorse akan abinda ta aikata, tana cikin wannan tunanin taga Ambulance ya shigo gidan, duk iya leken da take bata ga wanda ya saka Mayraah a Ambulance din ba, amma tana ta jiyo kukan Ammi, sai kuma ta juya da sauri ta koma dakinta tana tunanin inda zata yi discarding kwalban poison din don tasan ko hauka take bazata saka a bola ba.... MD har zai shiga Ambulance din bayan paramedic da suke ciki sun saka ma Mayraah oxygen with Maheer by her side, sai kuma ya juya ya kalli Ammi dake biye da shi a gigice tana kuka kamar ranta zai fita ita ma tana kokarin shiga Ambulance din, speaking calmly yace "In sha Allah she will be fine, bazai yiwu ki shiga Ambulance ba..." Bai jira cewarta ba ya shiga Ambulance din suka bar gidan, Ammi na kara rusa kuka, Sai da Haseenah ta ji fitar Ambulance din ta fito compound a rikice ta nufo Ammi da gudu tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, me ke faruwa Ammi, na fara bacci naji kamar siren, meye ke faruwa?" Hankali tashe take tambayar tana zaro ido, Ammi ko kallonta bata yi ba ta bi bayan Ambulance da sauri ko takalmi babu, Haseenah ta koma gun Bilkisu da ke kuka tace "Wai me ke faruwa Bilkisu? Me ke faruwa a gidan nan" Cikin kuka Bilkisu tace "Wallahi Mayraah ce babu lafiya har kumfa na fitowa bakin ta" Haseenah ta dafe kirji tana gwalo ido tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, kuma ta mutu?" Bilkisu bata tsaya bata amsa ba ta shiga cikin gida da sauri don dauko ma Ammi takalmanta da Hijab ganin har ta fita gate, dama kuma har ta haddace sunan asibitin da ta gani jikin Ambulance din. Maheer na zaune babban reception din asibitin ya dafe kansa da yayi masa nauyi, lokaci lokaci yake dagowa ya kalli Ammi dake reception din ita ma tare da Bilkisu dake ta kokarin kwantar mata da hankali take bata hakuri amma kamar tana kara tunzurata don Ammi tayi kuka har taji ba dadi, gaba daya ta dawo bata da wani kuzari, sun kusa awa biyu reception din a zaune amma babu likitan da suka ga ya fito har sannan, wannan ya kara daga ma Ammi hankali sosai ba kadan ba, wajen karfe sha biyu da rabi Dr Hamid ya fara fitowa, Maheer ya mike da sauri yana kallonsa don yayi recognizing dinsa as one of the doctors that went inside the emergency room with Mayraah, karasawa yayi gun sa, Ammi ma ta mike da sauri ta nufesa gabanta na mugun faduwa, Dr Hamid na kallon Maheer yace "She is been transferred to ICU...." Yana fadin haka ya bar wajen, Maheer ya bi sa da kallo, Ammi ta fashe da matsanancin kuka ta riko Maheer tace "Maheer me hakan ke nufi? ICU naji fa yace" Maheer yayi kokarin calmly dinta yace "Dama za a kai ta can ai, saboda pulse dinta da ya dauke na wani lokaci, in sha Allah she will be fine Ammi" Karfin hali kawai shi ma yake yana kokarin kwantar mata da nata hankalin. Karfe biyu saura na dare Dr Khalil ya shigo reception din daga ICU, Ammi ta mike da sauri tana goge hawayen idonta ta nufesa don taga kamar kusan duk likitocin asibitin sai da suka shiga Emergency room din, muryarta na rawa ta kamo hannunsa tace "Plss tell me how is my daughter? Kar ka boye min komai don girman Allah ka gaya min Dr, just tell me plss, is she alive?" Hawaye na sauka idonta tayi masa tambayar, Maheer da ya mike tsaye shi ma sai kallon Dr Khalil yake ganin expression din fuskarsa, Dr Khalil yayi kasa da murya amma hakan bai boye damuwarsa ba yace "Zata samu lafiya in sha Allah Mama, ki kwantar da hankalin ki" Dr Khalil ya Kalli Maheer da ya nufosa yace "Dr Maheer?" Maheer ya masa nodding, Dr Khalil yace "Mu je office Dr" Ammi ta fashe da wani sabon kuka ta rikosa tace "Ni ma zaka iya gaya min koma menene Dr, mu tafi office din" Tana fadin haka ta fara tafiya kamar tasan office din nasa, Dr Khalil ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, ya kalli Maheer dake tsaye gabansa yace "How comes Maheer? Waye yayi mata haka?" Damuwa karara a fuskarsa yayi tambayar, Maheer yayi kasa da murya yace "Wani irin poison ne pls? And how is she? Is she responding? can i see her? Plss?" Zuciyar Maheer na bugawa yayi request din, Dr Khalil ya zauna kan kujera cause he was exhausted ya rike kansa, Maheer ya zauna kusa da shi don gaba daya hankalinsa ya gama tashi, Ammi kuwa tayi gaba ba tare da ta waigo ta ga ko Dr Khalil din na biye da ita ba, Dr Khalil yace "Don Allah garin yaya wannan abu ya faru? Su waye da waye a gidan? Ko taje wani waje ne aka bata abincin?" Maheer yace "Yanzu baza a min alfarma in shiga in ganta ba?" Dr Khalil yace "She is in a critical condition now, we've tried our best, her body is failing, she is on life support" Maheer yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Dr Khalil bai iya ya dago kansa ba har bayan kusan minti daya, a hankali yace "We are trying our very best, akwai manyan likitoci biyu ma from another hospital da suka zo" Yana fadin haka ya mike ya bar wajen Maheer ya bi sa da kallo. Maheer bai taɓa shiga kalan tashin hankalin da ya shiga a lokacin ba, he felt like the world is coming to an end, ji yake kamar komai ya tsaya masa cak a duniyar, he wish mafarki yake, he wish shi ne ya ci abincin nan ba Mimi ba, yasan don shi aka yi poisoning abincin not Mimi, fita yayi daga reception din yana ganin building din na juya masa a kai ya jingina jikin bangon asibitin ya runtse ido zuciyarsa na bugawa da karfi, lokaci daya ya bude ido ya nufi outside of the hospital. Wajen karfe hudu Dr Khalil ya shiga ICU for the countless time, tun karfe uku likitocin ciki suka fita MD kadai ya rage a ciki, Dr Khalil na kallonsa don tun dazu yake tsaye a position din da yake, Dr Khalil ya karasa yayi kasa da murya yace "Kana bukatan ka huta MD, I will stay, go get some rest...." MD dai kallonsa kawai yake bai ce komai ba, Dr Khalil could see how confused and disappointed he is, ya juya a hankali yana kallon Mayraah dake kwance on life support feeling so heartbroken, Sunkuyar da kai MD yayi a hankali yace "I wish we could do more than this, i wish..." Sai kuma yayi shiru, Dr Khalil yace "It's not our fault MD, we tried our best, kawai mu ci gaba da addu'a ba mu cire hope ba in sha Allah" Zaunawa MD yayi ya jinginar da kansa jikin wajen ya rufe ido. Karfe hudu na asuba Abba ya shigo asibitin hankali tashe after driving all the way from kano. Kallonsa kawai Ammi dake zaune reception take yi hawaye na sauka idonta, yanda taga rana haka taga daren nan tare da Bilkisu dake gefenta, Abba ya karasa hankali tashe yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ina likitocin suke.. where is the Drs office, suyi transferring dinmu outside of the country kawai" Kuka kawai Ammi take kamar ranta zai fita ta kasa cewa komai, Abba ya nufi Nurse dake zaune reception din da sauri yace "I want to speak with any of the doctor in here pls" Nurse din ta zagayo tace "Ohk sir" Office din Dr Khalil ta tafi don ko minti biyu ba ayi ba ya tafi sama bayan ya fito ICU. Bayan Dr Khalil yaji bukatan Abba yayi kasa da murya yace "Sir our hospital is among the best here in Nigeria, kwararrun likitoci gare mu a nan, ko an fita da ita iyakar abinda muke yi a nan din za ayi mata, likitoci turawa biyu where among us today, so kawai addu'a za mu mata Allah ya tashi kafadunta, in sha Allah she will be fine...." Cikin rashin gamsuwa Abba yace "Na fi gane kuyi referring dinmu any best hospital in the world za mu je plss, ku min haka" Shiru Dr Khalil yayi yana kallonsa. ICU Dr Khalil ya samu MD ya sanar masa abinda Abba ke cewa, MD dake ta kallonsa yace "Ceo tana hanya with 2 Dr's"
Chapter 249 · 0% Book details