← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 218 OF 313

Sashe 218

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"I will try" The rest of the journey was silent har suka iso gida, bayan yayi parking tace "Idan nayi sallah zan maka girkin" Yace "Toh Nagode Mimi" Tayi murmushi ta bude motar ta sauka ta nufi cikin gidan. Mayraah na shiga parlon Ammi ta tadda Mama Ladi kwance ta lullube da bargo, Mayraah ta karasa kusa da ita ta duka tana kallonta da mamaki tace "Baki da lafiya ne Mama?" Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Ae tun asuba da na tashi naji kafafuwana sun kasa daukata nasan da matsala, to ilai kuwa gashi" Mayraah tace "Ayya, to Allah ya sauwake, kin sha magani?" Mama Ladi tace "Wa zai bani er nan? Ai yanda kika gan ni a nan tun dazu a haka nake" Mayraah tace "To zuwa anjima sai in fita in amso maki maganin idan nayi sallah" Daga haka Mayraah ta mike ta karasa dakin Ammi, kaya ta sameta tana ta hadawa a akwatuna, Ammi tace "Ya hanya Mimi?" Mayraah tace "Alhamdulillah, ina yini Ammi" Ammi tace "Lafiya lau, ina yayan naki?" Mayraah tace "Kamar ya shiga gida" Ammi tace "Toh kiyi sallah ga abinci can na maku ki duba kitchen" Mayraah tace "Toh Ammi" Ta juya ta nufi kofa Ammi tace "Ki fito da kayanki gaba daya daga press din dakin ki ajiye kan gado, zan jera maki a akwati, amma sai kin ci abinci in kinyi sallah" Mayraah tace "Toh Ammi" Daga haka ta fita daga dakin, tana komawa dakinta tayi wanka sannan ta dauro alwala, bayan ta idar da sallah ta sauka downstairs ta shiga kitchen, duba abinda Ammi ta girka masu tayi, sai kuma ta fita ta koma ta dauko wayarta ta dawo parlon ta zauna tayi dialing number Maheer, yana fara ring Maheer dake kwance ya mike zaune ya daga yace "Mimi" Tace "Yaya me kake son ka ci?" Yace "Koma me kika girka zan ci" Tace "Ohk" Daga haka ta katse wayar, Haseenah dake kitchen din dake Chalet zata zubo masa abinci duk da tasan ba ci zai yi ba, tana jin wayar da yayi da Mayraah ta ɗan yi wani murmushi ta mayar da abincinta cikin warmer ta fito daga kitchen din ta wuce daki, dama girkin da Ammin tayi ne taje kitchen ta debo ba wai ita ta girka ba, Mayraah na kitchen tana ma Maheer girkin da tasan ya fi so wajen karfe biyar da wani abu aka bude kofar kitchen din ta juya, suna hada ido tace "Ina yini Yaya" Yace "Lafiya lau" Karasawa cikin kitchen din yayi yace "Babu abincin ne?" Tace "Aa akwai, Ya Maheer nake ma girki" Ya gyada kai ya dau plate zai debi abinci tace "Ko zaka ci wannan da nake yi" Yace "Aa akwai me shi ae" Tayi dariya tace "Ai zan iya tsam maka kaɗan a ciki" Bai sake kallonta ba ya debi abincin da zai diba ya fita daga kitchen, Ammi na shigowa kitchen zata hada ma Mama Ladi shayi tace "Mimi baki son abincin ne?" Mayraah ta kalleta tace "Aa Ammi yaya nake girka ma favorite dinsa" Ammi tace "Tohh ai shikenan nawa bai yi dadi ba kenan" Dariya Mayraah tayi tace "Aa ko ɗanɗanawa bai yi ba fa Ammi, kawai favorite dinsa nake masa saboda nasan ya gaji" Murmushi kawai Ammi tayi, ta hada shayin da ya shigo da ita ta fita daga kitchen din, Mayraah na gamawa ta fito parlor ta dau wayarta tana kallon Usman dake zaune kan kujera yana kallo a laptop, Maheer ta kira ta sanar masa ta gama, a hankali yace "Ki kawo min nan Chalet Mimi" Ta ɗan buda ido tace "Chalet kuma? Aa yaya kawai ka daure ka zo ka amsa" Yace "Na gaji ne" Ta ɗan yi shiru, sai kuma yace "Ki bar shi kitchen din idan na shigo zan dauka" Tace "Bari in kawo maka yaya" Daga haka ta ajiye wayar ta nufi kitchen, Usman ya bi ta da kallo, daukan abincin tayi ta dawo parlor tace "Yaya kace baza ka ci ba ko?" Yace "Eh" Kofa ta nufa ta fita zuwa Chalet, tana knocking kofar yace "Come in" Ta bude ta shiga sannan ta karasa inda yake kwance, tun da Haseenah ta ji yayi waya da Mayraah ta kawo masa abinci ta sake fitowa Parlon ta zauna, Mayraah bata yarda ta kalli direction dinta ba balle har hakan yasa sai ta gaisheta, she pretends bata ma san tana wajen ba a zaune, tana ajiye masa abincin tace "Ga abincin yaya" Yace "Thank you Mimi" Tayi murmushi ta mike ta nufi kofa ta fita, Haseenah ta bi ta da ido. Ko da Mayraah ta koma sama ta tarar Ammi na ta hada mata kayanta cikin set din akwatunanta, Mayraah tace "Ammi ki bari in karasa" Ammi tace "Aa bar shi ai na kusa gamawa kije kiyi alwala kawai, it's almost Magrib" Bandaki Mayraah ta shiga don yin alwala.... Da daddare Ammi na dakinta tare da Mayraah, Mama Ladi kuma na kwance har sannan cikin bargo Maheer ya shigo parlon, ya zauna ya gaida Mama Ladi ta gyada masa kai kawai, yace "Mama ba lafiya ne?" Mama Ladi tace "Ai tunda na tashi da asuba na ji jikina na rawa nasan da magana, to ilai ga ni nan rai a hannun Allah" Maheer yace "Subhanallah, to kin sha magani?" Mama Ladi tace "Mera ta samo min wani gantalalle na hadiya dazu, amma ba sauki" Maheer yace "Zuwa karfe sha daya kafin kiyi bacci sai ki kara sha, in sha Allah za ki ji sauki" Daga haka ya mike ya karasa Bedroom din Ammi yayi sallama, sai da ta amsa ya shiga, Ammi tace "Ya gajiyan hanya?" Ya zauna yace "Alhamdulillah, ina wuni" tace "Lafiya lau" Wayarsa ya mika mata yace "Aunty Mariya zata maki magana" Sai da gaban Ammi ya fadi, tun barin su kano da safe ta kashe wayarta har yanzu ta ki kunnawa, dazu ma sai wayar Usman ta amsa ta kira Abba, Ammi ta amshi wayar, yace "Ki kirata" Daga haka ya mike ya fita daga dakin, Ammi tayi dialing number Aunty Mariya yana fara ring Aunty Mariya ta daga, Ammi tayi mata sallama, Aunty Mariya ta amsa ta gaisheta sai kuma ta ja wani dogon numfashi tace "Ammi Hajja fa tana gidana yanzu haka" shiru Ammi tayi don tasan kwanan zancen dama, Aunty Mariya tace "Yanzu fisabilillahi ina take son Badiyyah ta tafi? Ta dai san ba zaman kanmu muke ba balle ace lallai mu rike Badiyyah a wannan halin da take ciki, wata dayan da tayi gidanki ma abun a jinjina ma Alhaji ne wllhi, Sanda muke kokarin saita Badiyyah ba duk ita ke tabarbara komai ba take goyon bayanta akan duk wasu mugayen halayyan da take, saboda me kuma yanzu har da ita a gudun Badiyyah? Ai in kowa ya guji Badiyyah to banda Hajja tunda ita ce root din duk abinda ya samu Badiyyah" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Ban san me zance ba Mariya, bana son magana shi yasa ma kika ji wayata a kashe, i am tired wllhi" Aunty Mariya tace "To kuwa wallahi Baaba Yahanasu bazata yarda a makala mata Badiyyah ba tana fama da kanta tunda ga Hajjan har ta bar gidan ta dawo nan, ina me tabbatar maki in dai Baaba Yahanasu ce gobe zata kamo hannun Badiyyah ta kawo ta gidan nan ba wai karamin aikinta bane, kuma Ammi kece babba ke ya kamata ki gaya ma Hajja bata da wani Hujjan gudun Badiyyah don ita ce silar duk abinda ya sameta, wallahi ita ce sila, da ta bar mu mun mata tarbiyan da ya kamata da duk haka bai faru ba amma tayi kane kane kan lamarin Badiyyah tana ga kamar ba sonta muke ba, ta dauki kalman maraici ta hure kunnen yarinyar da shi yarinya tayi ta iskancin da ta ga dama babu me ce mata don me, kuma yanzu tace bata da makiyiya sama da Badiyyah, ai bazai yiwu bane, a gabanta ya kamata Badiyyah tayi jinya ba a wani waje ba" Ammi tace "Rufa min asiri, kema zaki iya gaya mata hakan Mariya ba kince tana gidanki ba, sai ki buda mata komai babu boye boye" Aunty Mariya tace "Wai kin ma ji maganganun da ta dinga yi ne ma kuwa, cewa tayi fa mun tura Badiyyah gidan Yahanasu ta karasa ta, idan bamu yi hankali ba wallahi Nijar zata shiga gun er uwarta, wai Bilkisu ce er uwarta yau, ni gaskiya ina ga zan kira kawu Rabi'u in sanar masa duk abinda ke faruwa, kawai Hajja tayi hakuri ta rungumi kaddararsu ita da Badiyyah ta dauketa su koma kaduna su ci gaba da zamansu har Allah ya sauketa" Ammi tace "Kirasa ki sanar masa...." Aunty Mariya tayi mata sallama ta katse wayarta. Washegari Mayraah ta shirya da wuri zata shiga school ta amso statement of result dinta, flight din nasu na karfe hudun yamma ne, so bata san how long zata gama clearance before collecting the result statement ba shi yasa ma ta shirya da wuri, tana shiga parlon Ammi ta tadda Usman zaune yana kallon Mama Ladi dake hadiyan paracetamol, ta karasa ta duka gaban Mama Ladi tace "Ina kwana Mama?" Mama Ladi tace "Ke ban cika son magana ba fa" Mayraah tace "To Allah ya sauwake" Kallon Usman dake kallonta tayi tace "Ina kwana?" Yace "Ina za ki je?" Tace "Zan shiga School inyi clearance ne sai in amshi statement of result, ko zaka yi dropping dina yaya?" Ya mike yace "Mu je" Tace "Toh bari in gaya ma Ammi" Daga haka ta shiga dakin Ammi shi kuma ya fita daga parlon, Usman na dropping dinta a school din yace "Ki kirani idan kin gama" Tace "Toh" Daga haka ya bar school din, sai kusan karfe sha biyu Mayraah ta amshi result din nata sannan ta kirasa, bai wani bata lokaci ba ya shigo school din ya dauketa suka koma gida. Maheer na zaune parlor wajen karfe biyu yana jiran Ammi da ta kirasa sai ga ta ta sauko downstairs, ta zauna tana kallonsa tace "Maheer ya zan yi da wancan tsohuwar?" Maheer ya ɗan yi dariya yace "Wai har yanzu tana kwancen ne?" Ammi tace "Wallahi sai kara lullubewa take fa" Maheer yace "Kar ki damu
Chapter 218 · 0% Book details