Sashe 43
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuma kun san dai together with you all we shall make this a blockbuster💣 kawai dai daga ni har ku muyi trusting alkalamina, it won't disappoint us in sha Allah, i am assuring u it's gonna be mind blowing😁 [6/10, 10:51 AM] Khaleesat Haiydar💖: Hajja na shigowa Bedroom din Ammi ta rafka salati ta fashe da kuka a rikice ta zauna kasan carpet tace "Allah mun gode maka da wannan jarabawar" Mama Ladi da tuni tayi cilli da gyalen da ta yafa tace "Toh wai na taɓa jin inda aka fasa aure babu wani dalili ni Ladiyo? Kamata yayi ai a turkesu su fada mana uwar me aka masu za su fasa aure, ko kuma kawai a kai su caji ofis a bi mana hakkinmu, da wani ido za mu kalli jama'an da muka tara?? Ko dai yan iska ne yaron da iyayensa? A kira mana Meran mu ji ko wani sa'insa ya hadasu da yaron ne, ko kuma a kai ni gidan ni inji dalilin fasa auren" Ammi dai tayi nisa tunanin da take don tayi kukan har ta gode Allah, wai a haka ma fa bata san dalilin fasa auren ba ina ga ta sani, Aunty Mariya dama bata bi su Hajja zuwa dakin Ammi ba don ganin yayarta cikin kuka na kara karyar mata da zuciya, Abba kawai take son gani don gaya masa kar ya sanar ma Ammi dalilin fasa auren nan for her mental health, gun Maheer dake zaune parking space ta tafi, he looks so heartbroken and sad, Aunty Mariya ta fi minti biyu tsaye amma ta ma rasa abinda zata ce masa kamar yanda shi ma bai ce mata komai ba kansa a sunkuye, parlon baƙi ta nufa daga karshe duk jikinta a sanyaye, tana sallama kuwa ta tadda Abba har sannan a ciki, shi kansa kana ganinsa kasan ya shiga damuwa ba kadan ba, Aunty Mariya ta zauna saman kujera nan da nan hawaye ya cika idonta tace "Alhaji ina ga da an boye ma Ammi dalilin fasa auren nan because of her health, kar a gaya mata don Allah" tana fadin haka ta fashe da kuka, Abba dai yayi shiru yana kallonta ya kasa cewa komai, bayan few minutes Abba yace "Ina Mayraah?" Aunty Mariya ta buda ido sosai, infact duk wannan abinda ake babu ma wanda yaje ya ga halin da yarinyar ke ciki, Aunty Mariya tayi karfin halin cewa "To Allah ya sa yaron bai gaya mata ba dai, i think tana dakinta tare da kawayenta" a hankali Abba yace "Ki dubo min ita" Mikewa Maheer yayi yana kallon Hamidah da ta nufo parking space din da yake zaune, tun bata karaso ba yace "Where is she?" Hamidah tace "Wallahi na duba upstairs gaba daya bata nan, har dakin dake downstairs she is not inside" Maheer ya buda ido yace "What?" Barin ta yayi wajen a tsaye ya nufi cikin gidan da sauri. Hankali tashe Maheer ke searching all of the house for Mayraah, har kiran wayarta yayi yaji switch off, Aunty Mariya da ta shigo ita ma a lokacin duk ta gigice bayan Hamidah tace mata ai Mayraah ce bata gidan, ita dai Hamidah was so confuse at this time don bata san abinda ke faruwa a gidan ba, bude kofar parlon aka yi Usman ya shigo, babu fuskan wanda ya kalla ya wuce sama direct, Maheer ya bi bayansa yace "Wait, we can't find her in this house, she is no where to be found...." Usman da bai ma san abinda Maheer din ke cewa ba ya nufi parlon Ammi tun kan Maheer ya riskesa, yana bude kofar ya shiga yana kallon Ammi da ta daga kai tana kallonsa, yayi gathering courage yace "Su waye namu iyayen mu kuma?" Dai dai nan Maheer ya shigo parlon yayi gripping hand dinsa ya fitar da shi daga parlon, Ammi ta bi su da kallo as if trying to understand abinda Usman yace, can ta kalli Hajja da ita ma ta bi su da kallon mamaki, Mama ladi tace "Kamar yaya su waye nasu iyayen, ko dai wiwi suka bashi a kotun?" Ammi bata san sanda ta mike ta fice daga parlon da sauri ba, tsaye ta gansu corridor Usman ya hade kansa da bango Maheer was standing by his side looking confused as well, Ammi bata ce masu komai ba kamar yanda su ma basu ce mata komai ba, ta sauka downstairs Maheer ya bi ta da kallo, Aunty Mariya ta share hawayenta da sauri ganin yanda Ammi ta sauko downstairs tace "Ina kuma zaki Ammi?" Ammi bata ce mata komai ba ta fita, parlon da Abba ke zaune ta nufa, tana shiga ciki ta tsaya nan bakin kofa tana kallonsa tace "Boye min dalilin fasa auren Mayraah zaka yi?" Abba dake ta kallonta, ya ɗan sauke ajiyar zuciya, he knows she will definitely find out shi yasa ma da Aunty Mariya ta shigo tana ce masa kar a gaya ma Ammi yayi shiru don yasan wannan labarin kuma Allah kadai yasan iya inda ya tafi a yau din nan, gani yake har makota yanzu sun samu wannan labarin tunda ba a san ta inda ya billo ba, ya mike ya nufeta ya kama hannunta making her seat down kan kujera ganin she is palpitating, yayi kasa da murya yace "Ki kwantar da hankalinki Ammi, komai zai daidaita in sha Allah" Ammi na girgiza kai da kyar, hawaye na sauka idonta tace "Ka gaya min me ke faruwa, ina son ji daga bakin ka, menene yasa aka fasa auren Mayraah?" Abba ya dake yace "Allah ya ga zuciyar mu, bamu yi abinda muka yi don cutar da kowa ba, we did this out of our good heart, we only wanted the best for Mayraah, we didn't mean to be deceitful to anyone, Allah ya san intention dinmu...." Ya kasa ci gaba ya dinga kallon Ammi cike da tausayinta, he wish rana me kama ta yau bazai taɓa zuwa ba, the secret they kept for almost 23 years is now no longer a secret, ya dafa Ammi ganin she is more than shock, yace "Our main priority now is Mayraah, kada mu bari ta shiga damuwar da zai iya mata illa because it won't be easy mutanen da kake gani a matsayin iyayenka rana daya a tashi ace ba su ne iyayenka ba, she needs us the most in this trying time, and in sha Allah we will continue being the parent figure we are to her" mikewa Ammi tayi hawaye na sauka idonta a hankali tace "Zuwa yanzu duk an san ba mu muka haifi Mayraah ba kenan?" Bata jira cewar Abba ba ta juya zata fita daga parlon amma tun kan ta kai bakin kofar taga kofar da ma parlon na juya mata gaba daya, Abba ya nufeta da sauri... Mayraah ta dinga bin sa da kallo har ya kashe motar ya sauka, bata taɓa jin tsoro irin na wannan lokacin ba, ya zaga side din da take zaune ya bude motar, duk da yanda gabanta ke mugun faduwa ta marairaice cikin rawan murya tace "But i don't understand the meaning of this sir, ina ne nan ka kawo ni plss? This i almost 8pm, nasan ana ta nemana a gida" Tana kai wa nan ta fashe masa da kuka sosai, Musharraf dake ta kallonta yace "Kin zata son da nake maki iya baki kadai ya tsaya? An gaya maki na taɓa yi ma wata mace irin son da nake maki banda mahaifiyata? You think i have d strong heart to loose you just like that? You think bazan yi duk wani abu da zai sa in mallake ki ba?" The way he is talking kadai ya isa ya kara tsoratata, ita dai ta kasa cewa komai sai kallonsa take da manyan idanuwanta, kawai taga ya kamo hannunta ya sauko da ita daga cikin motar ya kulle, bugun zuciyarta ya tsananta she was so afraid of him a moment din nan, he doesn't look the gentle Dr Musharraf she knows, bin sa kawai take yana rike da hannunta, she don't think he is even okay, sai da ya fara kunna solar din gidan sannan suka iso entrance din parlon gidan, ta ga ya ciro makulli ya bude kofar, suna shiga ya sa ma kofar key ya zare, bata san sanda ta fashe masa da matsanancin kuka ba ta durkusa gabansa tana girgiza kai tace "Na shiga uku, sir don girman Allah tell me the meaning of this? Ina ce gobe ne fa daurin aurenmu, menene ya sa kuma zaka kawo ni wani waje da daddaren nan daga ni sai kai?" Musharraf ya girgiza mata kai yace "They are not prepared su daura mana auren gobe...." Yana fadin haka yayi hanyar dakunan dake parlon, Mayraah that was so confused ta bi sa da kallo zuciyarta na bugawa, gashi ya amshe mata waya ya kashe tun suna hanya, tayi zaman dirshan a wajen ta hade kai da gwiwa tana kuka cikin tashin hankali, ko dai dama ba sonta Dr Musharraf yake ba kawai yaudaranta yayi, sai kusan karfe takwas da rabi ya fito daga dakin da ya shiga, yanzu kam wani mugun tsoronsa take ji har cikin ranta, yana kallonta yace "Tashi ki je kiyi sallah" Ta kasa kallonsa tsabar tsoro kuma bata motsa daga inda take ba, yace "Ba ki ji me nace bane" Mikewa tayi zuciyarta na bugawa, ya nuna mata daki da zata shiga, kamar munafuka ta shiga inda ya nuna mata tana waigensa. Har Mayraah ta idar da sallah hawayen dake sauka idonta bai tsaya ba, ta takure waje daya saman darduman da take zaune wasu sabbin hawayen na saukowa idonta, what will she tell her parent and her brothers, ina zata ce masu ta je tun wajen karfe biyar har gashi yanzu tara ake nema na dare, kafin su zo nan tafiyar kusan awa daya da rabi suka yi a hanya, yanzu idan yace zai maidata gida ai sai wajen goma da rabi kilan za su isa ko sha daya, is he even ready to take her back home today? Tunanin hakan ya sa ta fashe da kuka sosai, bude kofar dakin aka yi, ta hadiye kukan da take ta koma baya a tsorace taki