Sashe 6
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
amma ta kasa, dole tayi kokarin composing kanta kafin Mayraah ta dawo dakin, ba a dau lokaci ba sai ga ta da cup din shayin, sai kuma da ta tabbatar Ammi ta sha kafin ta fara duba magungunan da ta gani gaban Mirror, ta ajiye wani daga ciki tace "Baza ki sha wannan ba..." Maheer ne ya shigo dakin yana kallonta yace "Bazata sha wanne ba?" Mayraah ta juya ta kallesa tace "Analgesic..." Yace "To sannu Aunty Nurse da tafi Dr" Mayraah tayi murmushi tace "Ni dai ban ce na fi ka ba" ya karaso ya duka gaban Ammi yace "Ya jikin Ammin?" Ammi na kallonsa tace "Alhamdulillah na ji sauki" Yace "Toh Allah ya kara lafiya" A hankali Ammi tace "Ameen" Kallon Mayraah yayi yace "ke ba 8am kika ce kina da lectures ba?" Mayraah tace "Ina kwana yaya" Yace "Lafiya lau" Ta mika ma Ammi maganin hannunta da ruwa a glass cup, bayan Ammi ta sha maganin Maheer ya mike ya fita, A hankali Ammi tace "Mayraah tashi kije ya ajiyeki makaranta" Mayraah ta girgiza kai ta dau cup din shayin da Ammi ta rage tace "I will stay with you and make sure u are fine Ammi, bazan iya tafiya in bar ki baki da lafiya ba" Daga haka ta fita da cup din da Ammi ta sha shayi zuwa kitchen, ta ajiye cup din a sink tana kallon Usman dake hada coffee a kitchen din tace "ina kwana yaya" Yace "Lafiya" juyawa tayi ta fita ta koma wajen Ammi. Haseenah ta shigo Bedroom dinta rike da tray din lemo da cupcakes ta ajiye tana kallon Badiyya dake zaune tayi tagumi tace "Ke ba a ganinki sai idan abu ya sha maki kai ko? Yau sati na nawa da dawowa Kano amma ko sau daya baki taɓa takowa kin zo inda nake ba" Badiyya ta daga kai tana kallonta tare da sauke ajiyar zuciya tace "Ina cikin tashin hankali Haseenah, kuma bani da wanda zan gaya ma da ya wuce ke" Haseenah ta zauna tace "Allah ya rabamu da tashin hankali, gaya min menene ya dame ki kawata?" Badiyya tace "Ina wannan lecturer din namu da nake baki labari?" Haseenah ta juya ido tace "Ke samarin naki ai yawa ne da su, wanne a ciki?" Badiyya tace "Level co-ordinator dinmu mana, yawanci yanzu ai labarinsa nake maki a chat" Haseenah tace "Ohh, wannan da kika ce kike karanta a whole textbook a Library saboda course dinsa?" Badiyya tace "Allah maki albarka shi fa...." Haseenah ta dakatar da ita tace "Bari dai in fara baki nawa labarin, ba jiya sai ga Maheer ya zo nan da wannan cousin din naki bayan magriba ba, ni fa dama tun ma ban ganta physically ba naji bata min ba, ko gaisheni zata yi a waya idan Maheer ya bata da kyar nake amsawa haka kawai naji na tsaneta, sannan na lura favorite dinsa ce yana ji da ita, magana daya biyu sai ya sakota yayi misali da ita, daga haduwar mu jiya da ita har fa sai da muka samu matsala da Maheer a kanta, to in gaya maki tun jiya rabon da Maheer ya kira wayata akan ban doka tsalle da na ganta ba, har yanzu na kasa daina mamaki wai Maheer ne zai iya yini daya curr yaki kirana abinda bai taɓa min ba tun da dating dinmu yayi karfi, meaning yana fushi da ni akan gantalalliyar yarinyar kenan" Badiyya tace "Haseenah ki bar duk wannan ki ji damuwata don tafi taki wllh... Haseenah lecturer din nan dai ya turo iyayensa few days back an kawo kudi har an sa ranan bikinsa da Mayraah ina can Bichi ban san abinda ke faruwa ba, wllh Haseenah kullum da son mutumin nan nake kwana nake tashi nake yini, saboda shi na maida hankali a Nursing Science har nake coping, wai gashi yanzu cousin dita yake shirin aure ba ni ba alhalin ni ya fara noticing a department din ba ita ba, kafin ya ma mutum tambaya daya ya min uku a Class, na shiga uku wllh ji nake kamar zuciyata zata buga in huta, rabona da abinci tun jiya da safe Haseenah" Sai kuma ta fashe da kuka sosai, Haseenah ta rike haɓa cike da mamaki tace "Ikon Allah, to ke garin yaya kika bari har suke dating juna bayan kina sonsa, me yasa baki taka mata burki ba tunda kince tana shakkar ki sosai" Badiyya tace "To wllh daga ita har shi munafukai ne, ni ban ma taɓa ganin munafukai irin su ba, ko kallon juna fa baza ki ga suna yi a department din ba, ita ma ko kallon inda yake bata yi, kai ya sha koranta idan tayi lattin zuwa ajinsa sannan bai taɓa yi mata tambaya a aji ba, kinsan idan lecturer na ji da student zaki ga yana yawan yi masa question a class, to i am among the students da yake yi ma question, wllh baza ki taɓa cewa akwai abu a tsakaninsa da Mayraah ba komin abunki in har dai ba shegen lura ke gare ki ba kamar Asma'u don ita ta fara ankarar da ni, kin san tana da Asthma din karya ita Mayraan, to ranan sai tayi pretending Asthma dinta ya tashi a class wai an goge ƙura kusa da ita, kuma lectures dinsa mu ke yi, u need to see the care and attention she got from him that day, lectures din da bamu yi ba kenan, ya kai ta dai office dinsa ya dubata har da bata magani, shi da baya sake ma yan mata fuska, wasu student din ma sunce shi ya mayar da ita gida ranan, to bayan haka kuma ni ban sake ganin ya kalli inda take ba a department din balle ya mata magana, ko sunanta ban taɓa jin ya kira ba wllh, Haseenah baki ga yanda na ke karatu ahead of this guys lectures ba tsabar sonsa da nake kuma don in burgesa, duk wani textbook din course dinsa sai na san yanda na takura a siya min a gida, tambaya kuwa idan yayi a class ina daya daga cikin masu bashi amsa, ni ban taɓa sanin ina da ƙwaƙwalwa ba sai da nayi arba da mutumin nan, kokarin da yaga nake yi ne ma ya sa fa ya fara noticing dina a department din lokacin muna level two 1st semester...." Haseenah dake danne dariyarta tace "Noticing dinki as how?" Badiyya tace "Like idan yayi tambaya sai ki ga yana kallona ko zan bada amsa tunda ina yawan basa amsan duk tambayoyinsa, a haka dai ranan bayan yayi tambaya na bada amsa ya tambayi sunana a gaban kowa da kowa a ajin wllh...." Kawai sai ta fashe da kuka saboda wani abu da ya tsaya mata a makogwaro, Haseenah ta sauke ajiyar zuciya tace "Toh ke tun daga sannan zaki yi using privilege din ai" Badiyya dai ta kasa cewa komai sai kuka, Haseenah tace "Toh ita kuma cousin din taki ta yaya har suka fara soyayya baki sani ba" Badiyya na share idonta tace "Shine har yau nake son sani, don yanda kika san statue haka take a class ba um ba um um, infact clique din nata ma kauyawa ne yan ghetto fa wa enda da kyar ake biyan tuition fee dinsu per session, haka zaki gansu da Hijab zumbula zumbula wata er kauyen waratallawa ce fa kawarta a department din ana kiranta Hamidah, to a haka zaki gansu sun samu kujera can bayan class sun zauna ba um ba um um sai yan idanuwa kamar mayu, ni kuma dama front seat nake zama duk ranan da muke da lectures dinsa kinga dole dole ya san ni ko bana answering question balle ni kadai ce mace me bashi amsa a kaf ajin" Haseenah tace "To daga tambayar sunan naki ba abinda ya sake shiga tsakaninku?" Badiyya tace "Wa yace maki? Ai duk inda muka hadu a makarantar na gaishesa to haka zaki ji yace how are you *Badiyyah*, kaff matan department din babu sunan warce yake kira kai tsaye sai ni, ke kya ce shi ya rada min sunan, har fa haushina wasu yan matan suka fara ji a department saboda yanda yake amsa min gaisuwa" Haseenah tace "Ni ko zan so in ji yanda suka fara soyayya da cousin din nan taki" Badiyya ta share hawayen da yaki tsaya mata tace "Kilan da na yarda na zauna gidansu kamar yanda Ammi ke takurani da zan fahimci wani abu, amma ni rainin hankalin Maheer da Usman ne bana so, barin ma Usman din nan, shi yasa naki zaman gidan wllh, shi dama Umar ba ruwansa" Haseenah tace "Kin ga mu tashi mu tafi gidansu Zaliha bazata rasa shawaran da zata bada ba, ni kam gaskiya ban san me zance ba, da ma dai ba a kai kudin bane, amma wannan ai zance yayi nisa" Badiyya ta mike tace "Tashi mu je don Allah"