Sashe 195
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
key ba" Yana fadin haka ya bude front seat ya shiga, Dr Khalil ya zaga ya shiga driver seat, sai da suka bar asibitin Dr Khalil yayi dialing number Mayraah, tana dagawa yace "Nan da 30 minutes zan dawo in sha Allah, ki jirani" yana gama fadin haka ya katse wayar, MD dake kallonsa yace "Wato ita wannan mannerless teenager din budurwarka ce shi yasa ka dage sai ta samu aiki a asibitin nan ku jone salon ka daina maida hankali a aikin ka ko, sannan ita wannan er mitsitsiyar yarinyar har yaushe aka haifeta tayi degree? thank God ba aikin za a bata ba, kuma baza a taɓa bata ba as far as i remain the MD in here, sannan on a serious note bana son sake ganinta a asibitin nan, she is neither a staff nor a patient don haka ban ga dalilin da zata dinga shigowa ba, i will talk to the securities not to let her in from henceforth" Dr Khalil dai bai tankasa ba driving dinsa kawai yake. Bayan tafiyar Khalil da kusan minti arba'in Mayraah dai na zaune office dinsa ta jinginar da kanta jikin kujera tayi nisa tunanin da take taji an bude kofar office din ta juya duk tunaninta shi ne ya dawo, sosai gabanta ya fadi ganin Zainab ta shigo office din fuska a murtuke kamar an jefota, Mayraah ta sauke idonta daga kallonta, lokaci daya jikinta yayi sanyi, Zainab ta karaso har gabanta tana kallonta da kyau tace "Ke don kaza kazanki duk fadin garin Abuja baki ga maza yan iska mara mafada karuwai irinki ba sai mijina za ki makale ma? Baki ga matsiyata masu zaman kansu kaman ki ba sai mijina? To wai ma ke uban wa yace maki Khalil ɗan iska ne? ko kuma ance maki shi ma daga sama ya fado bashi da iyaye kamar ki? Don in har kina da iyaye ban jin zaki dinga irin wannan kazamin rayuwar da kike kamar sakakkiyar akuya a garin Abuja, baki can baki nan, baki gidan mutane, baki asibiti, baki hotel, baki Suleja da kika kama gida kike zaman kanki ko ance maki duk ban bincika ba? to bari ki ji wallahi wallahi ina ja maki kunne da babban baƙi ki fita harkar mijina, i am warning u ki fita harkar khalil, stay away from my husband kada inyi maki abinda baki taɓa zato ba a rayuwarki don wallahi ba mutunci ne da ni ba, ba ni da kirki wallahi, sannan in ba zina iyayenki suka yi suka haifeki ba to ki bar min gidan uwata ki kama gabanki ki je can ki ci gaba da rayuwar zaman kai da kike a suleja, mu gidanmu gidan tarbiya ne, sai ki wani dinga yawo da hijabi sumi sumi kamar ta kirki nan kuma lalata mazan mutane kike yi cikin Abuja, i am cutting you this first and last warning idan kuwa ba haka ba nace maki duk abinda na maki ke kika ja ma kanki, banza kawai karuwa me zaman kanta" Zainab na kai wa nan ta fice daga office din kamar zata tashi sama, Mayraah ta jinginar da kanta jikin kujeran da take zaune. Sai bayan awa daya Dr Khalil ya dawo asibitin, Mayraah na zaune yanda Zainab ta fita ta bar ta ya shigo office din, ya karaso yana kallonta bayan ya ajiye makullin motar MD kan table dinsa yace "Ki gaya min me ya faru Mayraah, why are you crying?" Shiru tayi har sai da ya dawo gefenta ya zauna leaving enough distance tsakaninsu yace "Pls say something, an maki wani abu ne kika shigo kina kuka daxu?" Mayraah ta kallesa sannan a hankali tace "Dama idan mutum ya bar gidan su yaje wani waje sai a fara masa kallon yana iskanci?" Tana masa tambayar hawaye ya cika idonta, Dr Khalil yayi shiru yana kallonta, ta fashe da kuka ba tare da tasan tayi hakan ba, tace "Ko dai nayi kama da warce take iskanci ne?" Dr Khalil ya sauke ajiyar zuciya yace "Gaya min me ya faru?" Tace "No! answer my questions first" Dr Khalil yace "Mayraah, in our society today da kuma al'adan mu na hausa fulani duk macen da ta bar gaban iyayenta for whatsoever reason dole zata yi facing fiye da haka a rayuwa, kin ga wasu za su mata kallon warce tafi karfin iyayenta, wasu su mata kallon er iska warce idonta ya bude tunda an san dai tafi karfin iyayenta ne ya sa ta shiga duniya, don babu iyayen da za su ba ma er su go ahead ta tafi tayi zaman kanta, wasu za su mata kallon warce ke karuwanci, bazan boye maki ba Mayraah at first da na ga take taken ki nayi maki kallon warce ta zabi ta shigo Abuja tayi rayuwar shashanci ne, even the hotel u lodged in na sa maki question mark a lokacin, but at the same time u look innocent" Goge hawayen dake sauko mata tayi tana kallonsa, yayi kasa da murya yace "Tell me what happened" Cikin rawan murya tace "Shi yasa Ahmad yake min kallon er iska har yake tunanin zan iya bin sa hotel mu kwana?" Khalil ya zaro ido yana kallonta, yace "Ahmad??" Ta fashe masa da kuka sosai, mikewa Khalil yayi ya ma kasa ce mata komai gaba daya jikinsa yayi sanyi Ahmad bazai taɓa canzawa ba kenan, bayan few seconds ya sauke wani ajiyar zuciya ya duka gabanta yana kallonta a hankali yace "Only this is enough for you kiji hankalinki ya koma gida Mayraah, mace in ba gaban iyayenta take ba kowa ma kallon da yake mata kenan to be frank.... You have given dem enough space na sati biyu yanzu, nasan duk hankalinsu ba a kwance yake ba na rashin ki" Mayraah tayi murmushin takaici tana share idonta bata son tace masa komai game da abinda matarsa ta shigo tayi mata bayan fitarsa, bazata so ta dalilinta happy family din su samu issues ba, tunani ne iri iri a ranta a lokacin, daren ranan a nan asibitin Khalil ya sa ta kwana, with d hope that as early as possible kafin zuwan MD zai je yayi dropping dinta, amma sai suka tashi da wani aiki da asuba tare da sauran likitocin asibitin, zuwa karfe tara Mayraah ta gama shawaran abinda zata yi a zuciyarta, tun cikin dare take tufka da warwara a ranta ko baccin kirki bata yi ba sai bayan sallahn asuba ta samu bacci ya dauketa, yanzu kuwa tana tashi ta tafi bandakin office dinsa ta wanke bakinta da mouth wash ta wanke fuskarta sannan ta fito ta dau Handbag dinta ta nufi kofa ta fita har sannan kuma su Dr Khalil basu fito theatre ba, tana sauka stairs tayi ido hudu da MD da shigowarsa reception din kenan da wasu turawa biyu sai bakin fata daya duk sanye da suit, a tare da su wata dattijuwa ce warce bata da maraba da halfcast coporately dressed in black suit with skirt da iyakarsa gwiwa, dai dai nan su Dr Khalil ma suka fito theatre da likitoci kusan hudu, gaba daya nurses gaida matar suke da ladabi, har ma da Dr's din tana amsa su cikin fara'arta da turancinta me cike da phonic, MD gaba daya attention dinsa na kan Mayraah bayan ya wani hade rai kamar bai taɓa dariya ba da ya hangota, wato a asibitin ma ta kwana kenan, Mayraah ta karasa saukowa downstairs ita ma ta gaida matar, Matar ta sakar mata murmushi tace "Helloo" Har tayi gaba ta sake juyowa tace "Are you a staff here young lady?" Mayraah ta ɗan kalli MD da ya kafeta da ido, a lkci daya ta kalli Dr Khalil taga ya nodding mata kai alamar ta ce eh, da sauri ta gyada ma matar kai kamar kadangariya, matar ta kalli baƙin mutumin dake cikin fararen fatan tace "Dr Yemi, you remember my Late moslem frnd Hajiya Amina?" Yace "Oh yes, Late Professor Amina, exactly i remembered Ma" Matar ta nuna Mayraah tace "Her replica, she just reminded me of her, may her soul rest in peace" Duk suka amsa da "Ameen" Matar tace "Ba don nasan yaranta ba kuma bata da karamar yarinya da nace ke yarinyar ta ce..." Mayraah dai sai murmushin karfin hali take tana kallon kyakkyawan dattijuwar don bata taɓa zaton tana jin Hausa ba sai gashi tayi hausa, amma Hajiya Amina da tace take replicating ya tsaya ma Mayraah cak a rai, to ko dai she is related to the Hajiya Amina tunda tace suna kama, MD na kallon Ceo din tasu da ladabi yace "Ma, You've stood for so long"