← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 312 OF 313

Sashe 312

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

will he tell Abba yana son ya aureni? dama ba kallon kanwarsa yake min ba?" Usman ya dan buda ido yace "Wa yace maki shi yace yana so ya aureki?" Ta kara fashewa da kuka tace "Abba bazai taba yin haka ba idan ba shine yace ba, Abba will never think of this, me yasa bai yi tunanin ni little sis dinsa bace da har zai ce zai aureni, yanzu kenan da gaske ni ba kanwarku bace?" Usman yayi kasa da murya yace "Look Mayraah, ba shi yace ma Abba zai aureki ba, hasalima he was taken unaware too, Billah Dr bai san da batun nan ba kinji na rantse maki, kawai baya son yi ma Abba musu a gaban Dad dinki da Grandpa dinki kuma nasan da tun farko ya sani kafin ayi zaman nan bazai amince ba" Ita dai kuka kawai take don ko duk jikinta kunnuwa ne bazata yarda bai sani ba, muryarta na rawa tace "Ni dai wallahi bazan iya zama da shi as mijina ba, wanda nake ma kallon yayana fa? that is the last thing i will do on earth" Dariya sosai ta ba Usman amma ya dake bai yi ba, yana murmushi yace "Yanzu dai abinda nake son in gaya maki shine ki kwantar da hankalinki shi ma ai ba so yake ba don yace ke kanwarsa ce, amma kinga it's too early yace ma Abba haka sbda relatives dinki, beside ke da kike wajen Amminki har yanzu... ko kinji wani yace maki ai za a tafi da ke wani waje ne? Iyaka may be next week kije ki gaida grandparent dinki a kaduna ki dawo, so just put in mind that u are still Miss Mayraah ki ci gaba da harkan gabanki har sanda za a san abun yi, but for now, we all are not in support of this" Shiru tayi tana kallonsa tana goge hawayen idonta don abinda yace ya kwantar mata da hankali kam, ya dan buda mata ido yace "Ammi ma tace ai baza ayi haka ba, don haka kinga ta goyi bayanki cewar auren is wrong, so just relax and cheer up" Mayraah ta sunkuyar da kanta a ranta kuwa tana tunanin jiya da take ta tambayar Maheer waye mijin da aka aura mata yaki gaya mata, wani mugun haushin rungumeta da yayi yana lallashinta ta dinga ji, ta kalli Usman tace "To ni dai bana son ma ya sake min magana a gidan nan, nima kuma bazan masa ba" Tana magana ne amma har hawaye ya cika idonta, Usman dai murmushi yayi bai ce komai ba, can ya mike, tana goge idonta tace "Yaya fita zaka yi?" Yace "Zan je in shirya, yau Friday" a hankali tace "Ohk" Ya nufi kofa kafin ya fita ya juya ya kalleta yace "Make sure kinyi breakfast din Mimi" Ta gyada masa kai ya fita daga dakin, sai a sannan Mayraah ta dan ji ta samu relieve a ranta har tayi breakfast din dake gabanta, tana gamawa ta fita da plate din da cup din shayi, tun da ta kallesa sau daya a parlor shi ma by mistake ne don bata san shine a zaune ba, daga haka bata sake kallon inda yake ba ta nufi kitchen fuska daure, shi kam dama ko kallon inda take bai yi ba, ko da ta fito daga kitchen din ma bata gansa a parlon ba. Bayan sallan Juma'ah Maheer da Usman suna parlon Ammi, Ammi na kallon Usman tace "Maheer yace min ka saka masa 5M Allah ya sa afi haka, Allah ya kara maka budi" Usman ya dan buda ido ya kalli Maheer cause bai yi expecting zai gaya ma Ammi ba, shi kuma kawai assisting dinsa yake son yi gun kayan lefen da Ammi tayi magana jiya da daddare, Ammi tace "Allah ya bar zumunci" Murmushi kawai Usman yayi bai ce komai ba, Ammi na kallon Maheer tace "So now what is ur budget na lefen?" Maheer ya daga kai yana kallonta, bayan few seconds yace "I will add 7M to the 5M he gave" Ammi ta gyada kai a hankali tace "To Allah ya kara budi, ni kuma zan siya mata set din Gold da za a sa a kayan, Abbanku ma nasan zai bada wani abu a kara a kudin lefen, though shi ban san me zai mata ba don kakanta yace zai mata furnitures din gida gaba daya, Ceo kuma tace we shouldn't bother about kitchen wares and all electronics, sai a siya akwatuna set uku each with 6 boxes" Usman ya dan buda ido yace "That's much, 18 kenan fa" Ammi ta dan yi murmushi tace "No it's not, Autana ce ai, nima zan mata akwati biyu na kayan sa wa" Usman yayi er dariya, Shi dai Maheer ba abinda yace, Ammi na kallonsa tace "Sai kuma kudin gyaran jiki, nawa zaka bada?" Maheer ya kalleta kamar dai bazai ce komai ba sai kuma yace "Ohk" Usman yace "Shi gyaran jikin nawa ake yi" Ammi tace "Nawa za ku bada?" Usman yace "200k yayi?" Ammi ta masa wani kallo tace "Meye kuma 200k?" Ya Sunkuyar da kai yana murmushi yace "Toh ai ban san kan abun ba" Ammi tace "Ku bada 1M, idan akwai canji sai a ajiye maku" Usman yayi murmushi yace "To ba damuwa" Ammi tace "Yanzu zuwa sunday za a kai ta kaduna zata yi kwana biyu don ina son ta dawo da wuri a fara mata gyaran jikin, in kuma za su mata can din to" Usman yace "Allah ya kai mu" Ammi tace "Ina son zuwa nan da kwana biyar a gama hada komai na lefen tunda kun ga kaduna za a kai masu kayan" Usman yace "A nan Abuja za a hada kayan?" Ammi tace "Eh da zan ma surkar Dr Khalil magana don muna gaisawa sosai da ita, Hajiya Safiya ma zata shigo Abujan sai su hada kayan tare kawai, Mariya kaga yau ta koma sai kuma biki zata dawo" Usman da yayi shiru yana kallon Ammi ya dan yi murmushi yace "But Ammi, Hajiya Amina dake kano ko ita ma zata iya hada kayan cause business dinta ne ba sai in involving outsiders ba" Kallonsa kawai Ammi take, can tace "To sai ka kwashi kudin ka tura mata ta hada" Usman yayi er dariya ya mike yace "Ni akwai inda zan je yanzu, sai na dawo" Ko kallonsa Ammi bata yi ba ya nufi kofa ya fita, Ammi tace "In nasa bikin ya tashi sai ya bata kudi ta hada masa kayan wannan kam bai isa ya gaya mana yanda za mu yi ba" Shi dai Maheer bai ce komai ba, can dai yayi murmushi ya mike, Ammi tace "Ka je ka ci abinci bawan Allah" Usman na fita ya yi knocking kofar dakin Mimi, Yana nan bakin kofar a tsaye har Maheer ya wuce sa ya sauka downstairs, Mayraah ta bude kofar dakin a hankali tana ganinsa tace "Yaya fita zaka kara yi?" Yace "Eh, fito ki ci abinci" Tace "Na ci abinci" Yace "Ammi tace baki ci da yawa ba" Shiru tayi bata ce komai ba, can tace "Yaya don Allah zan iya gaya ma Ammi ina son inje gidansu Ceo?" Usman yace "Ai ina jin Sunday za su tafi can kaduna, next week idan kinje kadunan za ki hadu da su a can" Bata sake cewa komai ba, yace "Fito ki zuba abincin?" Babu musu ta fito daga dakin suka sauka downstairs, ya zauna parlor yana jiran yaga ta zubo abincin kafin ya bar gidan, har ta nufi kitchen ta juyo tace "In zuba maka kai ma yaya?" Yace "Aa sai na dawo" Bata sake cewa komai ba ta nufi kitchen din, wani irin faduwa gabanta yayi bayan ta shiga kitchen din ta ga Maheer, lkci daya ta juya ta fito daga kitchen din fuska daure, Usman yace "Ina abincin?" Kin cewa komai tayi tana tahowa a hankali, yana ganin Maheer ya fito kitchen din da cup din coffee sai da abun ya basa dariya, shi dai Maheer bai kalli inda take ba balle Usman dake zaune ya nufi dakinsa, Usman ya mike kafin yace mata komai ta nufi sama, yace "Mimi" bata tsaya ba tayi wucewarta. Kamar yanda Ammi tace washegari da safe ta shirya ta tafi gidan surkar Dr Khalil bayan ta sanar ma Abba da ya koma kano jiya da yamma, Ammi bata bar gidan ba sai da ta tabbatar Mayraah tayi breakfast sanin bata son cin abincin.... Bayan azahar Usman zai fita Mayraah ta marairaice masa tace "Yaya kai ma fita zaka yi Ammi bata dawo ba" Ya kalleta da mamaki don makullin motarsa da ya bari jiya a dakinta ya shigo dauka yace "Akwai aikin da kika bani ban yi bane Mimi?" A hankali tace "To ni kadai fa a gidan" Yace "Bilkisu na nan ai, even Dr bai tafi aiki ba tukun ai sai da yamma" Bai jira cewarta ba ya nufi kofa, tace "Pls yaya zan rakaka" Sosai ta basa dariya, ya juyo yace "Ki rakani ina?" Ta sauke idonta tace "Inda za ka" Yace "Ni ai ba wani waje zan je ba Client ne ke jirana" Tace "Eh zan bi ka sai in jira a mota" Ya gyada kai yace "To je ki tambayi Dr" Tayi kasake tana kallonsa yace"Yea, in kina son bi na je ki fara gaya masa tukun" Tace "To saboda me?" Yace "Saboda ya kamata a gaya masa" Komawa tayi ta zauna alamar baza ta ba, Usman yace "Sai na dawo" Ta marairaice tace "Don Allah yaya" Ya wani hade rai yace "Ba ki ji abinda nace maki bane?" Shiru tayi tana kallonsa, ya fice daga dakin, a hankali ta mike ta dau gogaggen hijab dinta ta saka sannan ta fito, har zai fita parlon ta gansa da sauri tace "Don Allah ka jirani yaya" Ya juya yana kallonta, ita dai da ya bar ta ita kadai da Maheer a gidan gwara tayi abinda yace kawai, tana tafiya a hankali ta tafi dakinsa, kwankwasa kofar dakin ta yi sannan ta bude fuskarta babu yabo babu fallasa ta shiga, tana kallonsa tace "Wai ya Usman yace za mu fita ka kula da gidan ba kowa" Shi dai danna wayarsa kawai yake, bai daga kai ba
Chapter 312 · 0% Book details