Sashe 67
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tana damunka" Bai ce mata komai ba ya maida dubansa kan Mayraah yace "Je ki debo abincin" yana fadin haka ya juya zai fita tace "Yaya ka ara min wayarka don Allah" ya juyo yace "Ina naki wayar?" Tace "I lost it" Ya ciro wayarsa a aljihu ya ajiye mata gefen gado sannan ya fita daga dakin, ta karasa ta dau wayar ta zauna gefen gado ta fara dialing number Musharraf, a ranta ta fara addu'ar Allah ya sa ya kunna wayar yanzu, amma unfortunately aka ce mata a kashe, nan da nan hawaye ya cika idonta damuwarta ya karu a kan na da, what is happening? Baya son magana da ita ne yake kashe wayarsa kenan, Kwanciya tayi edge din gadon hawaye me zafi na sauka idonta. Karfe biyar Mayraah ta shigo parlon Ammi ta dalilin kiranta da ta yi, tun da ta shigo Ammi ke kallonta, ita kanta Ammin ta kasa samun nutsuwa har sannan a zuciyarta daurewa kawai take duk abin nan, Mayraah ta durkusa gabanta a hankali tace "Ammi ga ni" Ammi tace "Me za ki girka ma Abbanku?" Mayraah tace "In masa tuwo da vegetable?" Ammi tace "To je kiyi" mikewa tayi ta nufi kofa zata fita suka kusa cin karo da Maheer, ta koma gefe ba tare da ta kallesa ba tace "Sannu da zuwa" daga haka ta fita daga parlon ya bi ta da kallo kafin ya karasa ciki yana kallon Ammi dake kallonsu... Cikin awa daya da wani abu Mayraah ta gama girkin tunda ɗan kadan zata yi dama, Ta dawo parlon Ammi tace "Ammi na gama" Ammi tace "To sannu da aiki" juyawa tayi ta fita, Maheer ya mike yace "Bari in je masallaci in dawo" Ammi tace "Daga can ka wuce gida Maheer, ya zaka fara barin yarinya ita kadai a gida daga kai ta, ai zaka bari ko sati tayi tukunna" Maheer dai bai ce mata komai ba ya fita daga parlon, dakinsa ya tafi ya dau ledan da ya ajiye sannan ya fito ya tafi dakin Mayraah, tana tsaye jikin window tana kallon waje ya sameta, Mayraah ta juya jin an bude kofar dakinta, ya karasa ciki ya zauna gefen gado yace "Ga sakon ki Mimi" Tana kallonsa tace "Na mene?" Yace "Amsa ki duba" Ta sauke idonta sannan ta nufesa ta amshi ledan da yake mika mata, tun bata bude ledan ba ta gane waya ce, tana kallonsa da murmushin karfin hali a fuskarta tace "Nagode sosai yaya" Ya girgiza kai yace "That smile is fake" Dariya ya bata wanda bata san sanda tayi ba, tace "Allah da gaske naji dadi yaya" Yace "Toh kinga wannan is not fake" Murmushi kawai take ta bude wayar taga wanda yafi nata na da ne ma, a hankali tace "Nagode sosai, Allah ya kara budi" yace "Everything for my Mimi" shiru duk suka yi, bayan few seconds a hankali yace "And... sorry about what happened dazu a gidana Mimi, you know i will neva let that slide...." Da sauri Mayraah ta katse sa tace "Aa ni ai ya wuce a wajena har na manta ma" kallonta kawai yake, ta fara bude kwalin wayar, yace "Za a san min tuwon Abban?" Ta kallesa tace "Ohk amma halve, sai in ba Ammi sauran halve din, dama leda uku ne nayi" Yace "Toh bari in dawo masallaci, ki ajiye min a daki" Tace "Toh" Mikewa yayi ya fita daga dakin, Mayraah ta dinga kallon wayar bayan ta bude, sosai yayi mata kyau ba kadan ba and she is so happy about it, taga har da sim card ya siya mata, ta jona wayar a caji sannan ta ajiye kwalin ta tafi bandaki don yin alwala.... Bayan Magrib tana zaune kan darduma aka bude kofar dakin ta daga kai tana kallon wanda ya shigo, ya karaso dakin ya ajiye ledan hannunsa gefen gado, tana kallonsa tace "Ina yini" Yace "Lafiya lau" Tace "Ana ta kiranka a waya" Tana fadin haka ta mike ta tafi ta dauko masa wayarsa da ya bata tun da yamma, ya amsa ya juya ya fita, Mayraah ta dau ledan da ya ajiye mata taga kwalin waya ne a ciki, ta buda ido da mamaki tana juya kwalin, exactly irin wanda Maheer ya siyo mata dazu color ne kawai daban da wancan, ajiyewa tayi gaban mirror ta fita dakin ta sauka downstairs, abinci ta saka ma Maheer kamar yanda yace mata, ta kai dakinsa, zaune ta gansa dakin yana kallo a laptop, yayi pausing movie din ta karaso ta ajiye masa abincin a gabansa tace "A kawo maka tea ne?" Yace "No... thanks Mimi" Ta mike zata fita yace "Ke kin ci abincin?" Tace "Aa anjima" zata fita dakin sai ga Ammi, Ammi tace "Wai Maheer baka tafi ba har yanzu?" Maheer yace "Ammi wai korata kike ne?" Ammi tace "Eh koranka nake, wannan wani irin abu ne haka? Kai in kanwarka aka ma haka zaka ji dadi?" Ya kalli Mimi dake tsaye yace "Aa bazan ji ba gaskiya, bari in gama cin abincin in tafi Ammi" Ammi tace "Gaskiya bana son haka, kar ka sake zuwa min gidan nan kwana kusa, ya zaka fara barin er mutane ita kadai daga kai ta jiya? Don't u have conscience" Muryar Mama Ladi suka ji tana cewa "O'o Allah, O'o Allah, ba fa yarinya bace amaryar nan da zaki wani daga hankalinki haka a kan an bar ta ita kadai a gida Ammi, jiya fa da muka je na kalli idonta da kyau wllh ba yarinya bace, da kyar in ma bata girmi Mashir din ba, ni dai nayi ta mamakin a inda ya samota har yaji sha'awan aurenta, ke fa baki mata kallon da na mata ba jiya, don haka kawai ki ja bakinki kiyi shiru in baki san abu ba" Ammi dai bata ce mata komai ba ta juya ta fita daga dakin Mayraah ta bi bayanta, Mama Ladi na kallon Maheer dake cin abincin da Mayraah ta kawo masa tace "Kai ko kamar wanda aka ma rufa ido, maimakon ka samu yarinya er dai dai warce bata wuce Mera ba zaka kare da uwar mata haka Mashir? Ko kai baka ganta ba wani saɓar saɓar da ita sai uban mazaunai, kyan fuska kawai gareta fa shi ma kamar mai ta shafa, wannan haihuwa daya biyu zata sukurkurce ta fashe, don irin kiɓan kazantar nan zata yi da tayi haihuwa daya, wanda da ta gifta zaka ji doyi" Mama Ladi ta kyabe baki tace "Allah dai yasa kada Usuman yayi irin wannan zaben tumun daren, ya samu yarinya er dai dai abunsa kamar Mera" Murmushi kawai Maheer yayi yana cin abincinsa, Mama Ladi ta juya ta fice daga dakin. Sai da Mayraah ta fara zubo ma Ammi abinci ta kai mata parlonta sannan ta tafi dakin Usman. Ya ajiye wayar da yake yace "Ya aka yi?" Tana jan fingers dinta tana tsaye jikin kofar dakin tace "Thank you so much for the phone yaya, Allah ya saka da alkhairi" Yace "Ameen, any other thing?" Ta girgiza masa kai tace "Kawai godiya zan maka dama" Yace "Accepted Mimi" Tayi murmushi ta juya ta fita daga dakin. Da gudu Haseenah ta shige bandakin yaran Maman Bala jin muryar Hajja tana sallama a tsakar gida, Maman Bala ta fito tana amsa sallaman tace "Sannu da zuwa Hajja" Hajja tace "Allah sa dai nan Badiyya ta shigo Sahura" Maman Bala tace "Ehh gata can dakinsu Bala kuwa" Hajja ta nufi dakin, Badiyya ta hade rai tace "To ke Hajja meye na biyoni don Allah kamar wata er yarinya" Hajja tace "Ayya naga kunun har ya huce kin san flask din nawa ya fashe balle in juye maki a ciki" Badiyya tace "Toh ki tafi gani nan zuwa ni dai" Hajja tace "Toh" Daga haka ta juya ta fita, Haseenah ta fito tana zare ido kamar warce tayi ma sarki karya, Badiyyah tace "Yanzu da magariban nan kice zaki kama hanyar Zaria Haseenah, to wai ma wani waya kike da baza kiyi a gabana ba sai kin wani fita tsakar gida, in haka ne meyasa baki je wajen wanda ku ke wayan da baki son in ji ba, ina fama da kaina na fito saboda ke amma don munafurci sai ki wani dinga fita kina kus kus a saya" Haseenah ta marairaice tace "Wallahi ba haka bane Badiyya, duk bayanin da na maki nake yi a wayar da kika ga ina yi, Coursemate dita ce Fatiha fa" Badiyya dai ta kara kyabe baki ta dauke kai, Haseenah tace "Kuma ai da ban yarda dake ba bazan zo wajenki ba Badiyya, yanzu dai bari in maki transfer ki dauko Atm dinki ki cire kudin ki bani inyi maza in tafi" Badiyya ta mika mata hannu babu yabo babu fallasa tace "Haseenah bani sarkan nan da dankunne zanje kasuwan da kaina in siyar" Haseenah ta hadiye wani abu da kyar tace "Yana fa wajen me siyarwan account number kawai zan tura masa ya saka maki kudin wllh, hidimar bikin nan da ake ta yi ne yasa aka samu delay, yanzu dai don Allah gobe za mu yi maganar gold din ta waya, ki tashi muje ki ciran min kudi a account dinki inyi maza in tafi, zan tura maki dubu talatin yanzu" Badiyya na girgiza kai irin ba mutuncin nan tace "Gaskiya idan goben yayi da kaina zan je shagon me gwal din na gaji kuma haka, aban gold din ko kuma aban kudin" Haseenah tace "Ehh goben sai in baki kwatancen wajen mutumin ki je, ai sananne ne a kasuwan" Mikewa Badiyya tayi tana dingishi suka fita daga dakin Haseenah na biye da ita, Badiyya tayi ma Maman Bala sallama suka bar gidan, suna isa gate din Hajja Badiyya tace "Kinga kawai muje gun me POS din ki masa transfer ya baki kudin don ina shiga gida yanzu Hajja zata iya biyoni waje idan nace zan sake fitowa, kuma kince baki son tasan komai" Haseenah tace "Gaskiya kam, wannan sirri ne tsakanina da ke" Suna karasawa gun me POS Haseenah tayi transfer din aka bata cash, Tace "To sai mun yi magana Badiyya, ina isa Zaria zan kira ki" Badiyya tace "Amma dai wajen wa zaki a Zari'a ke da baki da dangin uwa balle na