← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 313

Sashe 68

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

uba a can" Haseenah tace "Haba gobe fatiha zata sameni a Zarian ai, yanzu dai zanje gidan wata Coursemate dinmu ne tukun" Badiyya ta tabe baki tace "Toh Allah ya tsare" Haseenah tace "Ameen" Daga haka ta bar layin da sauri, Badiyya ta koma cikin gida, Hajja na ganinta tace "To kiyi sallah bari in zuba maki kunun" Badiyya ta taɓe baki ta zauna tana kallon Hajja tace "Hajja kin san matar Maheer ce ta zo muka shiga gidan Maman Bala kuwa?" Hajja ta kalleta tace "Matar Maheer? Wani Maheer din?" Badiyya tace "Wallahi kuwa in gaya maki, wai ya korata gida daga dai Mayraah taje gidan ta mata rashin kunya tace bazata dauka ba" Hajja ta dinga kallonta tace "Mayraah ta mata rashin kunya?" Badiyya tace "Wallahi nake gaya maki, ko gaida Haseenar ma bata yi ba da taje gidan tana ta abu Isa isa da gadara, shine Haseenah abun ya ɓata mata rai tace to gaskiya ita bata son haka ya za ayi ta shigo mata gida babu gaisuwa sai kallon walakanci, kar ki dada karki raga Maheer kawai ya dauketa ya maidata gidansu, shine fa ta shiga tashin hankali bata shiga gidan nasu ba ta yo nan hankali tashe" Hajja na tafe hannu tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Badiyya tace "Ace Mayraah bata zama annoba ba? Dubi tashin hankalin da take hadawa a family dinmu duk tana neman tarwatsa kanmu ta lalata mana zumunci" Hajja na gyada kai a hankali tace "Wannan gaskiya ne" Badiyya tace "To wannan magana tsakaninmu ne dake, kar ki ce ma kowa komai babu ruwanki, kinga dai ni ga abinda ta sa Usman yayi min don ma Allah ya so da sauran kwanana a gaba, Aunty Mariya na ji tana gani bata kwace ni ba kuma har yanzu ai kinga bata zo gidan nan ba balle ta duba halin da nake ciki, ita kanta Ammin bata kira taji ya jikina ba kuma ya kamata ita ma ace ta zo ta duba ni ai, ai kinga duk babu wanda ya zo, balle Mama Ladi dake ta goyon bayan abinda aka min duk akan wata banza wai Mayraah, yanzu gashi sabon auren da Maheer yayi tana nema ta kashe masa, ai wannan badluck ce a family dinmu wllh, ashe dama babu abinda muka hada da ita shi yasa tun farko na tsaneta jinina bai hadu da ita ba, Ammi tayi ta fifitata a kaina komai ace Mayraah, a gabana Aunty Mariya zata kira sai dai tace a ba Mayraah...." Hajja dai bata ce komai ba tayi shiru, Badiyya ta tabe baki ta mike da kyar ta shiga bandaki... Washegari da safe Mayraah ta gama shiryawa don tana son shiga school ba don kowa ba sai don Dr Musharraf kilan zata gansa a school din, fitowa tayi zata sauka downstairs taje kitchen don hada ma Ammi shayi, babu wanda yasan zata school a gidan don dama so take sai ta kai ma Ammi shayi kafin tace mata zata je makaranta, a stairs ta hadu da Hajja dake haurowa, tayi murmushi ganinta tace "Ina kwana Hajja" Ko kallonta Hajja bata yi ba, Mayraah ta koma gefe ta bi ta da kallo in shock, Hajja ta nufi parlon Ammi ta bude kofar babu ko sallama, Ammi da Mama Ladi sai Aunty Mariya duk suka daga kai suna kallonta, shiga parlon tayi tana kallon Ammi da kyau tace "Hajara" Ammi ta kasa cewa komai ta dinga kallonta gabanta na faduwa don Hajja bata kiran sunanta kai tsaye sai dai ta kirata da Ammi, Hajja tace "Ina ce dai da yardata kika dau yarinyar nan kika rike har zuwa yau ko? Ina ce Mamuda ƙin amincewa yayi da farko, ni ce nan na karfafa masa gwiwa na rokesa Allah da annabi ya barki kiyi rainon yarinyar tun tana tsumma ko? To a yau nake son ki zabi ko ni ko yarinyar"
Chapter 68 · 0% Book details