← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 183 OF 313

Sashe 183

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

adaidaita sahun ta shiga tace "mu tafi" yace "mu je ina?" tace "inda zan samu motar zuwa suleja zaka kai ni" yace "to bani kudin kawo ki nan da nayi tukun" dubu biyar ta kirga ta basa amma duk ta kagu su bar wajen, yana amsan kudin bayan ya ga nawa ne ya tada adaidaita sahun suka bar wajen, sai kusan magrib mayraah ta iso suleja a gajiye ga yunwa da take ji don har wani juya mata kanta yake, bayan ta sauka a daidaita sahun da ya kawota anguwan nasu don yace bazai shiga layin ba haka ta fara trekking zuwa cikin layin tana tafiya a hankali, tun daga nesa take kallon motar da ta hango anyi parking few houses before her's babu ko kiftawa. Har Mayraah ta isa dai dai inda aka yi parking motar bata daina kallon motar ba, as if tana son tabbatar da motar waye, kasa ci gaba da tafiya tayi zuciyarta na bugawa ganin an bude kofar motar alamar wanda ke ciki zai sauko, idonta na kansa har ya sauko ya kulle motar ya rungume hannu yana kallonta without blinking, ta wani hade rai ta ci gaba da tafiya kamar zata tashi sama, zata wucesa yace "Ilham" a mugun fusace ta juyo tace "Me yasa kake bibiyata? And how did u get here??" Yana kallonta directly yace "Saboda tun daga first day din da Ahmad ya kawo ki hospital baki da lafiya na gano da yawa daga maganganunki karya ne, nasan karya kike tun a sannan, u never called ur people that very night da Ahmad ya baki waya ki kirasu, wasu nambobi daban da kika san basa amfani kika yi dialing, don har yau i have the 2 numbers na karba gun Ahmad kuma ina kira inji a kashe, wacece ke? Why did u chose to say all sort of lies about so many things to me? Take a look at ur self, baki yi kama da warce tasan wani abu wai shi wahala ba a rayuwa, baki yi kama da warce ta fito daga gidan da sai an tara kudin admission kafin ki taho makaranta ba, sannan a ilimin ki da wayewarki bazan yarda cewar baki san anyi terminating admission dinki kika taho Abuja ba, show me the admission list kin ki, wani school ne kin ki fada min, ke da kika tsaya tara kudin makaranta da kyar ta yaya ma za kiyi lodging hotel me tsadan nan, har kiyi ikirarin zaki iya kama gidan dubu dari uku a Abuja, so many unnecessary lies, kin ce sunanki Mayraah kin dawo kince Ilham u think i forgot, and worst of all ke kadai kike zaune gidan da zaki shiga yanzu not with anybody kamar yanda kika yi claiming cewar gidan stepmom dinki ne, har briefing dinki labarin rayuwata nayi duk don ki zama relax and tell me a little about ur self amma kin ki, ban san mission dinki a Abuja ba, amma baki yi kama da warce ta fito daga gidan da ba tarbiya ba, you look decent and well brought up, as a medical Dr na hango depression a idanuwanki, damuwa na daga cikin abinda ke contributing na low bp dinki.... Nayi kokarin ganin kin fara aiki a hospital din ko zai canza maki thinking dinki akan abubuwa da dama da ya shafi rayuwarki amma naga ba haka bane, and kin nuna u are not even after the job, u are not desperate about it, sannan u don't mind being fired, that aside kina da enough cash a tare da ke" Mayraah ta kasa ci gaba da kallonsa nan da nan hawaye ya cika idonta, kasa daurewa tayi ta hade kanta da motar ta fashe da kuka sosai, shi dai kallonta kawai yake, can ya sauke ajiyar zuciya yace "Zan je masallaci, ana kiran sallah, ki shiga ciki kiyi sallah, idan na dawo masallaci i will call u out" Kai kawai ta gyada masa hawaye na sauka idonta ta wuce sa ta karasa gate din gidanta ta ciro makulli a jaka ta bude ta shiga ciki, sai a sannan ya dauke kai daga kallonta ya karasa masallacin da ya ji ana kiran sallah.
Chapter 183 · 0% Book details