← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 236 OF 313

Sashe 236

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tace "Nima ban sani ba yaya" Yace "Ask around you" tace "Ni kadae ce a gida, sun tafi conference, i am not too fine saboda muran da nake...." yace "Hotel ne?" Tace "Aa gidan ceo, idan sun dawo i will ask for the address" ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "Gidan Ceo? How comes?" Bai jira tace komai ba ya kara da cewa "Ok then, I will be waiting for the address" a hankali tace "Ohk" katse wayar yayi ta ajiye, gaba daya mura ya sa ta gaba and it's making her feel sick, tana ganin lkcn sllh yayi ta tashi taje tayi alwala, tana idar da slln ta kwanta, cikin bacci ta ji an bude kofar dakin ta bude ido taga Ceo, mikewa zaune tayi, Ceo tace "Baki yi lunch ba Mary Ann" Ta murza ido tace "I slept off" Ceo tace "This is pass 3, ki fito ki ci abinci" Daga haka ta juya ta fita, Mayraah ta sauka daga kan gadon ta tafi parlor. Karfe biyar saura Mayraah ta fito daga dakinta tana kallon Ceo dake parlor tace "Ma ya iso, yana waje" Ceo tace "Ohk, ba kince Yayanki bane?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Yayana ne" Ceo tace "Let him in, it's cold outside" Mayraah tace "Ohk Ma" Fita tayi daga parlon, inda ta hangosa tsaye ta karasa, idonsa na kanta har ta karaso ta kara gaishesa tana murmushi tace "Yaya kai ma ashe kana jin sanyi naga ka sa Jacket?" Yace "Kema kika ji sanyi balle ni" Er dariya tayi tace "To ai ni dama kowa yasan bana son sanyi, kai kuma baka bacci sai da AC" Yana kallon rigar jikinta yace "I see, where did u get this designer jacket u are putting on?" Mayraah ta kalli Jacket din MD dake jikinta da sauri, sai kuma ta kirkiri murmushi ta dawo gefensa tace "Ceo ce ta bani" Ya daga kafada yace "Ok, but ai na maza ne, yana da tsada sosai" Mayraah dai sai murmushin karfin hali take, Ya rungume hannunsa yace "But why did she decide to lodge u in her home? Na zata hotel zata biya maku...." Mayraah tace "Eh sauran maza ne duk suna hotel, ni ce kawai a nan, yaya tace fa mu shiga ciki akwai sanyi... She said u are welcome" Ko rufe baki bata yi ba, Ta yi ido hudu da MD da yayi parking ya sauka daga mota wanda da alama tasa ce, Usman ma kallonsa yake ganin he is walking toward them, shi ko bai sake kallonsu ba har ya wucesu, Usman ya bi sa da kallo ganin gidan da Mayraah ta fito zai shiga, sai kuma ya kalleta da sauri yace "Who is he?" Ta ɗan buda ido tace "MD dinta ne, he is the MD of the hospital" Usman yace "MD?" Mayraah ta gyada masa kai, yace "Shi ma a gidan nata ya sauka kenan??" Da sauri ta girgiza kai tace "Aa fa yaya, kilan ta kirasa ne ta aikesa amma ba nan ya kwana ba wallahi" Usman dai yayi shiru yana kallonta, can yace "Why did u do as if baki san sa ba, shi ma haka?" Da mamaki ta zaro ido tace "Yaya ai ni ban wani san sa ba fa, ka manta ni new staff ce a asibitin? We are not use to each other" Yace "You are never meant to get use to ur boss ai dama, do u know who a boss is? but i am surprise yanda zaki ga boss dinki and not greet him just like that in dai ba akwai wani abu ba, ga dukkan alamu ya sake maki fuska da yawa ko kuma akwai wani abu between u two...." Mayraah ta turo baki tace "Wani abu kuma yaya? To yaushe ma na fara aiki a asibitin, abinda ma zan iya kirga sau nawa na gansa a asibitin, office dinsa ma fa ba kowa ke zuwa ba, and his office is at the last floor of the hospital building, kawai dai ya fiye takura ne da masifa shi sa nake avoiding dinsa, baka ga dauke kai nayi ba kar ma ya gan ni" Usman ya jingina da brick wall din wajen yana kallonta as if not convince, ita dai ta sunkuyar da kanta, bayan few seconds yace "Yaushe tace zaku koma Nigeria?" Mayraah tace "She said gobe ko jibi" Yace "An gama conference din ai?" Tace "Aa gobe ne last day" Yace "Shi kuma da ya zo yanzu sai yaushe zai bar gidan?" Mayraah ta zaro ido tace "Yaya ai nima ban sani ba, kilan aiki zata sa shi.... And na manta tace mu shiga ciki saboda sanyi" A takaice yace "Bazan shiga ba, do u need anything?" Ta girgiza masa kai tace "Aa" Yace "I will be on my way" A hankali tace "Da wuri haka yaya?" Yace "In kina bukatan wani abu ki kirani" Ta gyada masa kai, Juyawa yayi har ya fara tafiya ya sake dawowa yace "Why don't u tell her u prefer hotel?" Ta zaro ido tana kallonsa, yace "Ohk kin fi son zama under same roof da katti ko? U are comfortable" A hankali tace "Yaya ni da ita kadai ne a gidan wallahi, kuma ai it's a privilege ajiyeni da tayi a gidanta a matsayina na karamar staff" Bai sake ce mata komai ba ya juya ya bar wajen ta bi sa da ido, sai kuma ita ma ta juya tana tafiya a hankali ta nufi cikin gidan, tana shiga parlor ta kulle kofa, MD kadai ne zaune parlon zata wuce dakin da ta sauka yace "Hey come back here" Juyawa tayi ta kallesa, ko damuwa da hade ran da yayi bata yi ba, ta dawo parlon tana kallonsa, ya mike yace "Halan an gaya maki wasa ya kawo ki UK? Idan kina son haduwa da wani namiji me yasa baki biya kudin jirgi kin biyosa ba? Wato ga opportunity kin samu? ko kin zata yawon bude ido kika zo nan? Saboda kin ga Ceo na lallabaki ta kawo ki gidanta ta ajiye ki ko conference din ma baki je ba shine bari ki kira saurayinki, to let me give u this last warning har mu bar kasar nan bana son in sake ganinki da wani namiji don ba abinda ya kawo ki ba kenan, any body that wants to meet with u should follow u to Nigeria" A takaice ta juya ido tace "Har yayana? Kuma ai dai ban fita ba sai da na nemi permission daga wajenta kuma ta bani izini, why didn't u ask her before waiting for me?" Shiru tayi jin ana saukowa downstairs, Ceo tace "Ya tafi yayan naki ne?" Mayraah ta juya ta kalleta tace "Eh ya tafi" Ceo ta shigo parlon ta karaso ta mike ma MD takardun hannunta tace "Here" Juyawa Mayraah tayi ta nufi hanyar daki, magana ceo take masa amma hankalinsa na kan Mayraah har ta shiga daki. Da daddare Mayraah na kwance wajen karfe sha daya Maheer ya kirata, tana daga wayar ya ji muryarta yace "Me ya faru?" Ta mike zaune da kyar tace "Cikina" Maheer ya mike zaune daga kwancen da yake yace "When did it start?" Kamar zata yi kuka tace "Not long ago?" Yace "Did u take any drug?" Ta girgiza masa kai tace "Since 8 na bar parlon, ita ma kuma tace she will be going to bed early.... " Yace "Ko za ki je ki mata knocking, if not nasan baza kiyi bacci ba" Tace "Ni bazan iya tashinta ba, though it's not as if the pain is that much for now, kilan sai zuwa gobe da safe, i will try and sleep now" Yace "Are you sure" Tace "Yeah, yanzu ma ai na fara bacci ka kirani" Yace "Toh kiyi baccin Mimi, Allah ya sauwake, i pray bazai matsa maki ba anjima...." Ta ɗan yi murmushi tace "Bye" ta katse wayar ta koma ta kwanta, ba a wani dau lokaci ba bacci ya dauke ta, can cikin dare axaba ya tasheta ta sauko daga saman gadon duk da mugun sanyin da ake sai taji kamar zufa ma take, ta jawo wayarta da kyar ta duba agogo taga karfe biyu saura, ajiye wayar tayi, tun tana kokarin ganin ta jure kawai daga karshe ta mike zumbur ba tare da tasan ma tayi haka ba, ta murda makullin kofar ta bude da sauri ta fita, hasken reading lamp da ta gani study room dake parlon ya sa ta karasa can da sauri, tana isa ta durkushe wajen ta fashe da kuka ta ma kasa cewa komai, matsar da littafin gabansa yayi ya mike da sauri yana kallonta yace "Menene?" Cikin kuka tace "Wallahi cikina ciwo yake min ka taimaka min" Ya kunna wutan wajen ya durkusa gabanta da sauri yace "Ya yake maki?" Ta kasa ce masa komai, keenly yake kallonta seeing how she is reacting to the pain yace "Dysmenorrhea?" Gyada masa kai tayi da sauri, ya mike ya bar wajen, magani ya yafi ya dauko mata da ruwa a glass cup, hannunta na rawa ta amsa ta sha, shi dai yana duke gabanta yana kallonta, don bata daina kukan da take ba, bayan kusan minti goma yace "Tashi ki koma daki..." Ko rufe baki bai yi ba cikin rawan murya tace "Aa wallahi bai daina ba, kilan allura zaka min, dama allura ake min" Daga sama har kasa ya kalleta seeing how confident she still is in between pains, Bai yi niyyar mata alluran ba saboda ta riga da ta sha drugs, but ganin she is still in pain har karfe uku kawai ya hada alluran ya mata, nan parlon ta fara bacci ya tasheta ta wuce daki. Washegari har karfe takwas bata tashi ba, har sai da ceo ta shigo ta tashe ta, bayan ta fito daga wanka ta shirya sannan ta dau wani jacket dinta dake akwati ta sa sannan ta fita parlor, Ceo na kallonta tace "Breakfast yana dinning table" Mayraah ta nufi dinning din ta zauna. Wajen karfe goma na safiyar Mayraah na waje tare da Usman da zuwan sa kenan, yana kallonta yace "Hope you are better now?" Ta gyada masa kai tace "Na ji sauki" yace "Me yasa baki kirani jiyan ba, though
Chapter 236 · 0% Book details