Sashe 309
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
komai ba da ya wuce "Ga abinci Mayraah" Daga haka ta fita daga dakin, Kasa cin abincin Mayraah tayi duk da ko yunwan ma bata ji, wasu hawayen suka cika idonta taji gaba daya ta rude ta rasa wani tunanin zata yi, kallon wayar Ammi dake gefen gado tayi ta dau wayar tayi dialing number Maheer, yana fara ring with some seconds ya daga, a hankali tace "Yaya" shiru taji hakan yasa tace "Hello Yaya" Calmly yace "Mimi" ta fashe masa da kuka tace "Yaya nobody is saying anything to me, why is everyone not saying anything, don Allah kai kace min wani abu mana" Maheer yace "Me zan ce maki Mimi?" Tace "Abba's Decision" Shiru Maheer yayi, tana kuka a hankali tace "Yaya kayi shiru" A hankali yace "kiyi hakuri Mimi, i pray it's the best for you both in sha Allah" Mayraah ta zaro ido tsabar bugun da zuciyarta ke yi sai da taji kamar zai fito daga kirjinta, ta fashe masa da matsanancin kuka tace "Na shiga uku, Yaya don girman Allah ka gaya min waye Abba ya aura min" a hankali Maheer yace "Ammi zata gaya maki, yanxu dai za mu sallami baƙi za su tafi, stay calm, kiyi ta addu'a a zuciyarki it will help" Daga haka ya katse wayar, Maheer ya dinga kallon screen dinsa kafin ya ajiye wayar a gefen kujeran da yake zaune a dakinsa, jinginar da kansa yayi jikin kujeran zuciyarsa na bugawa yana kallon Ac din dakin baya ko kiftawa, Mayraah ta hade kanta da gadon Ammi ta dinga rusa kuka kamar an aikota, even Ya Maheer ma baya son ya gaya mata mijin da aka aura mata, kasa daurewa tayi ta mike ko dankwalinta da ya fadi kasa bata bi ta kai ba ta fita daga bangaren Ammi gaba daya, parlon Abba ta nufa inda taji Ammi tace Mom dinta taje ana nemanta, tana isa parlon ta bude kofar ta shiga, Aaria na zaune da Abdallah dake mata magana a parlon, duk suka daga kai suna kallonta, Abdallah ya mata alamar ta zo, duk da wajen uwarta tayi niyyar nufa kawai dai ta nufesa hawaye na sauka idonta, zaunar da ita yayi kusa da shi ya rungumeta yana kallonta da murmushi fuskarsa yace "It's the best for you in sha Allah daughter..." Ta fashe da wani sabon kukan sai ta kasa tambayarsa waye mijin, haka ya dinga lallashinta ita dai Aaria kallonta kawai take bata ko kiftawa nan da nan ita ma hawaye ya cika idonta. Karfe daya da kusan rabi Abba ya raka Alhaji Saminu bakin mota inda Driver ke jiransa zai kai sa airport immediately, da fara'a Alhaji Saminu ya dinga yi ma Abba godiya sosai yace "Mun gode kwarai da gaske Alhaji, mun gode da karamci, Allah ubangiji ya bar zumuncin mu, nayi farin ciki kwarai da gaske da wannan lamari na yau, Allah ubangiji ya basu zaman lafiya da zuri'a dayyaba, mun gode Alhaji, Allah ya kara girma...." Abba na murmushi yace "Ameen ya Allah Honorable, zuwa nan da kwana biyu in sha Allah sai a kai maku ita kadunan tunda tarewan mun saka sai nan da sati biyu in anyi biki" Alhaji Saminu yace "Kwarai kuwa sati biyu, Allah ya kai mu lokacin lafiya, mun gode kwarai da karamci Allah ya saka da alkhairi" Alhaji yace "To yanzu Kadunan za ayi taron bikin ko ya ku ke son za ayi?" Alhaji Saminu yace "Ai duk yanda ku ka tsara dai dai ne Alhaji, mu ai kun gama mana komai" Abba yace "To in sha Allah za mu yi waya" A haka suka rabu da Abba ya koma cikin gida. Bayan tafiyar Alhaji Saminu su Hajiya Ramatu da Mami duk suka shirya za su bi train zuwa kaduna, tare za su koma Kaduna da Mama Ladi zata je sanar ma su Hajja Mayraah dai an mata aure duk su tarkato su dawo Abuja biki nan da sati biyu, Ammi ta so su Hajiya Ramatu su kwana amma suka ce ai har an siya ticket, Ammi dake murmushi tace "Bari in taso Mayraahn ku yi sallama ina ga bacci take" Mama Ladi tayi karaf tace "Su da za a kai masu ita har kadunan ma meye kuma sai an taso ta, ai kawai bari mu tafi kar jirgin ya tafi ba mu" Hajiya Ramatu tayi murmushi tace "Haka ne Mama a bar ta tayi baccinta kawai" Ita dai Mami murmushi kawai take.... Karfe biyar saura Mayraah taji ana tashinta a baccin da ya dauketa parlon Abba kusa da Mahaifinta, bude ido tayi a hankali ta mike zaune tana bin parlon da kallo ganin bata ga Mom dinta ba balle Baban nata, Ammi na kallonta a hankali tace "Baki yi sallah ba, tashi mu je kiyi" Mikewa tayi tsaye Ammi ta kama hannunta suka fita daga parlon, kasa tambayar Ammi tayi ina mom dinta bayan sun koma can bangaren taga wayam ba kowa, a haka dai taje tayi alwala, bayan ta idar da sallahn ta juya tana kallon Ammi dake zaune tayi nisa cikin tunanin da take, mikewa tayi ta koma kusa da Ammi ta zauna a hankali tace "Ammi sun tafi ne?" Ammi ta mata murmushi tana shafa eyebrow dinta wanda baza ace ba zana mata shi aka yi ba a hankali tace "Duk sun tafi kina bacci Mimi" Mayraah tayi shiru tana kallon Ammi, she is just wondering why Ammi isn't saying anything to her har yanzu, Ammi ta sauke idonta tace "Abincin dazu ma baki ci ba, bari in kawo maki wani ki ci" Bude kofar parlon aka yi duk suka juya, Maheer ne ya shigo parlon, Ammi ta maida dubanta kan Mayraah tace "Let me get the food for you daughter" Daga haka ta mike ta nufi kofa ta fita, Mayraah ta kalli Maheer da ya zauna kan kujera ya ciro wayarsa ba tare da ya kalleta ba, mikewa tayi ta nufesa tayi relaxing jikin kujeran da yake zaune tana kallonsa tace "Yaya" Ya daga kai ya kalleta yace "Mimi" Ganin yanda idonta ya kumbura yace "Kuka kike ta yi kenan?" Ta bata fuska zata fara wani sabon kukan ya mike ganin fita zai yi ta riko hannunsa da sauri cikin rawan murya tace "Yaya ba fa wanda yake son yace min komai har yanzu...." Ya juya ya kalleta yace "Me kike son ace maki Mimi?" Hawaye na sauka idonta tayi shiru tana kallonsa, ya juyo gaba daya yana facing dinta, ganin yanda hawaye ke sauka idonta ya kai finger dinsa yana goge mata hawayen a hankali yana kallonta, ta fashe masa da kuka sosai, ya sauke idanuwansa, sai kuma rungumeta a hankali yana patting bayanta slowly amma ya rasa abinda zai ce mata yana jin kukan nata har cikin ransa, bude kofar parlon aka yi ya saketa da sauri ya koma baya amma tuni Aunty Mariya ta shigo, tayi masu kallo daya ta tafi ta dau abinda zata dauka, daga shi har ita basu yarda sun kalleta ba, ita dai ta fita daga parlon, Juyawa Maheer yayi ya nufi kofa Mayraah ta bi sa da kallo har ya fita daga parlon, zaunawa kasa tayi ta hade kanta da gwiwa tana shesshekan kuka. Mayraah na zaune parlon Abba bayan magrib bayan Ammi taje ta taho da ita daga bangarenta, banda faduwa babu abinda gabanta yake a inda take zaune duk ta takure waje daya, Abba na kallonta ya nuna mata kusa da shi, ta mike a hankali ta nufesa ta zauna kasan carpet kusa da shi, Bundle din kudin da ta gani gefensa ya kara distablizing dinta gaba daya a parlon ta kalli Usman da Maheer dake zaune kasan carpet waje daya su ma, sai Ammi dake zaune one sitter, babu abinda ya fado ranta sai ranan da Abba ya tara su Parlonsa a kano bayan an kawo kudin aurenta da Musharraf, bayan few seconds Abba ya sauke ajiyar zuciya ya dau bundle din kudin yana kallon Maheer calmly yace "Maheer ga wannan ka ajiye a account dinka" Maheer ya daga kansa dake kasa yana kallon Abban nasa, don wannan shine exact kalmar da yayi masa ranan da aka fara kawo kudin Auren Mayraah da Musharraf, Mayraah dai ta sunkuyar da kanta hawaye cike idonta, a hankali ya mike ya nufi Abba ya amshi kudin, Ammi dai sai kallonsa take har ya koma ya zauna, Abba yace "Ko ba yanzu ba wani lokaci sai ka tambayeta abinda zata yi da kudin kayi mata, be it in future...." Mayraah ta daga kai ta kalli Abba, sai kuma ta kalli Maheer da yayi shiru bai ce komai ba unlike wancan lokacin da sai da ya tsokaneta ma, murya Abba ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi, calmly yace "Mimi" Ta daga kai a hankali ta kallesa, sai kuma ta sunkuyar da kai zuciyarta na bugawa sosai, Abba yace "Kinsan a rayuwar nan bazan yi abinda zai cuce ki ba, a kaf fadin duniyar nan wanda yasan zafinki bayan mahaifiyar da ta haifeki to a bayan ni da Amminki da brothers dinki yake" Mayraah dai ta kasa dago kanta tana sauraron Abba, Abba ya nisa yace "Nasan kuma ko ba a wannan moment din ba cause i believe u might be taken unaware, but wataran zaki yi alfahari da abun nan da na maki, one day one time in sha Allah u will be proud of this, i am quite sure Maheer will be their for you till death do u both apart, he will make a great partner, you have him as a brother and Husband now" a hankali Mayraah ta daga kai tana kallon Abba, can ta juya da sauri ta kalli Maheer that was looking at a different direction, ta kalli Usman da ya ɗan mata murmushi, ta kalli Ammi da hawaye ke zuba idonta, muryan Abba ta sake ji tsakiyar kanta, calmly yace "Allah Ubangiji ya maku albarka, ya baku zaman lafiya da zuri'a dayyaba" Mikewa Ammi tayi ta karasa ta daga Mayraah that was soo shock ta fita da ita daga parlon.