← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 313

Sashe 112

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ur evidence via 07087865788 [7/4, 7:37 PM] Khaleesat Haiydar💖: Usman ya mike bayan Maheer yayi parking, ya kalli Mayraah yace "Sae da safe" Daga haka ya nufi inda motarsa take, ita dae kawai ta bi sa da kallo, Maheer bai sauko ba har sae da yaga Usman ya tafi sannan ya bude motarsa ya fito, ya nufeta ya zauna inda Usman ya tashi yace "Hope kin ci abinci" ta kallesa ta gaishesa, ya amsa yana mika mata ledan hannunsa, tana karba bayan taji abinda ke ciki tace "Yaya ya kawo min, but i will give my roommate this" Maheer yace "Ohk, me kika dafa?" Ta girgiza kai tace "Roommate dina ta ban shinkafa" yace "Kuma kin ci?" Duk da ko spoon biyu bata ci ba a shinkafar da Ummi ta zuba mata kawai sae ta gyada masa kai, ya mata murmushi yace "Good, gobe za ki shiga school ae?" Ta girgiza masa kai kawai, bai sake cewa komai ba, ita ma tayi shiru, Allah ya sani kawai daurewa take and she is trying to act she is okay, but deep down she is soo heartbroken and sad, gashi gaba daya ta kasa kuka ko zata ji sauki a ranta, tun kukan da tayi da safe bata sake ko digon hawaye ba har zuwa yanzu, ji take kamar hawayen nata sun ƙafe ne, babu irin tunanin da bai zo zuciyarta ba bayan sun ajiyeta dazu, da ta tashi zata yi abinda zuciyarta ke raya mata sae ta tuna da furucin Mamin Musharraf ta koma ta zauna a dakin, did she really want her 5 years to go in vain, idan ma ta bar shi ya tafi in vain din zata iya farawa daga farko kuwa? Ƙwaƙwalwarta zai iya daukan karatun nan gaba ma kuwa? All this thought ke sa wa ta kawar da abinda ke running a mind dinta, amma minti goma yayi kadan tunanin zai sake ringing a head dinta, ita kadae ce dakin don roommate din nata ta shiga school wai zata yi karatu, a haka kiran Usman ya shigo wayarta ta fita ta samesa, sae kuma Maheer da ya zo yanxu, ita kanta bata san she is this strong ba sai yau, firgit ta dawo daga tunanin da ta tafi bayan Maheer ya dafa ta cause magana yake mata amma bata san yana yi ba, ta juya da sauri ta kallesa, da damuwa yace "Mimi tunani kuma? I tot u promise me not to, i just caught u now" Tayi resting kanta a shoulder dinsa cikin sanyin murya tace "Yaya tunanin exams nake, i don't know where to start reading from, all the courses are bulky...." Maheer bai taɓa zama uncomfortable with Mimi leaning on him ba sae yau, ya kasa ce mata komai sae gyada mata kai kawai yayi, for almost 5 minutes babu wanda yace komai cikinsu, ita dae kanta na shoulder dinsa, can dai yayi karfin halin cewa "Erm naga kamar ba wuta hostel din ko? let me go and get u rechargeable flashlight yanzu in dawo" Ta daga kai ta kallesa tace "Yaya Usman ya kawo min with fan" Maheer yace "Good, yanzu za ki shiga ciki ki fara karatun ne? i will be calling u every now and then to know how far you've gone" A hankali tace "Ohk" yace "Good gal, go inside and start reading" Mikewa tayi tana rike da ledan da ya kawo mata tana kallonsa tace "Nagode yaya" Murmushi kawai ya sakar mata bai iya cewa komai ba, ta juya ta shiga ciki, sai a sannan ya sauke ajiyar zuciya, for some minutes ya kasa tashi a wajen daga karshe ya mike ya nufi motarsa, his intention was to be with her har zuwa 10 bai yi niyyar tafiya da wuri ba. Yana isa gida wajen karfe tara da wani abu bayan yayi parking ya shiga ciki, Haseenah na zaune parlon sanye da kayan bacci ga fruits da ta aika Musa ya siyo mata ta yanyanka ma Maheer ta rufe tana jiran dawowar sa, yana shiga parlon tun da ya lura ita ce a parlon bai ko kalli inda take ba yayi hanyar corridor ya bude dakin da Badiyyah take, Haseenah ta mike ta bi bayansa, tsaye tayi corridor din ganin dakin da ya shiga, Badiyyah na zaune ta kusa tashi da kazar da ya siya mata tana siɗe hannu yace "Baki bukatar komai?" Tace "Ba a kawo min ruwa ba" Juyawa yayi ya fita, ya wuce Haseenah dake tsaye ya tafi kitchen, Haseenah ta karasa dakin Badiyya tana kallon ciki, Badiyyah na lashe hannunta tace "Ke naga kamar yaya bai siya maki kazar ba ko?" Haseenah ta dinga jin zuciyarta na wani tafarfasa taki ce ma Badiyyah komai sai kallonta take, Badiyyah tace "Ga yanka daya nan ki shigo ki dauka" Sai ga Maheer ya bi gefen Haseenah ya shiga dakin ya karasa kusa da Badiyyah ya duka ya bude bottle water din ya zuba mata a cup ya dauka ya mika mata yana kallonta yace "Hannun ya maki sauki yanzu?" Ta wani marairaice tace "Har yanzu yana min ciwo wllh" Juyawa Haseenah tayi ta bar bakin kofar ta koma parlor ta zauna tana jin zuciyarta na tafarfasa..... Mayraah na zaune kan darduma da handout a gabanta tayi tagumi, tun tafiyar Maheer ta dauko handout din amma ko layi biyu ta kasa assimilating gashi yanzu har kusan karfe sha daya, gaba daya taji kanta ya tushe ga wani ciwo da yake mata, wayarta dake gefenta ya fara vibrate ta kalli screen din ganin Dr Musharraf ke kiranta tayi silencing kiran, yana katsewa ya sake kira nan ma ta kara silencing kiran daga karshe ta sa wayar a flight mode, ta tattara handout din ta ajiye gefe tayi kwanciyarta kan darduman, kuka take son yi amma ta nemesa ta rasa gaba daya, a haka roommate dinta ta dawo daga cikin school ta sameta kwance, Mayraah ta kulle ido kamar bacci take, bayan roommate din nata ta gama shirin kwanciya ta fara tashinta a hankali tace "Sis ki tashi ki hau kan gado" Mayraah ta bude ido tace "Ina son tashi inyi karatu ne anjima kadan ne" Ummi tace "Ki gaya min sanda kike son tashi zan sa alarm in tashe ki, kin ga kasa akwai sanyin tiles" Mayraah tayi shiru, can ta mike zaune a hankali tace "Toh Nagode" Komawa saman gadon tayi tana kallon Ummi ta nuna mata ledojin kajin da su Maheer suka kawo mata tace "Ki dauki daya naki ne, yayana ya kawo mana" Ummi tayi murmushi tace "Toh Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi, karfe nawa zan sa maki alarm din" Mayraah tace "Sha biyu da rabi" Ummi tace "To in sha Allah zan tashe ki lokacin" Mayraah tace "Nagode" sannan ta kwanta ta lumshe ido amma har karfe sha biyu idonta a bushe yake babu alamar bacci, sha biyu da rabi nayi Ummi da bata kai ga kwanciya ba tana revision ta fara tashin Mayraah, duk Mayraah na jin ta amma tayi shiru, daga karshe ta mike zaune da kyar, Ummi tace "It's time" Mayraah ta sauko daga kan gadon ta sake dauko handout dinta ta zuba masa ido kamar hoto, tana ta zaune har karfe biyu saura kawai daga karshe ta tashi taje ta dauro alwala ta dawo.... Sai kusan karfe hudu Mayraah ta kwanta kuma har a sannan ko line uku bata fahimta ba a handout. Ummi ce ta tasheta sallan asuba bayan ta idar ta koma ta kwanta, bata farka ba sai kusan karfe takwas da rabi, sosai kanta ke mata ciwo ta mike zaune da kyar tana bin dakin da kallo, Ummi ta gyara ko ina ta share har wanke wanke tayi, takarda ta gani gefenta ta dauka taga note Ummi ta bar mata kan cewar ga breakfast ta ajiye mata a warmer, akwai ruwan lipton ma a flask ita ta tafi school... Mayraah ta ajiye takardan ta dafe kanta, can ta jawo wayarta da ta sa flight mode tun jiya, bude wayar tayi ko minti daya ba ayi ba sai ga kiran Usman ya shigo, ta daga kiran ta kai kunne, daga daya bangaren yace "Me ya sa kika kashe wayarki?" A hankali tace "Ina kwana?" Yace "Ko ba ki da caji ne?" Tace "Akwai, bacci nayi ne" Yace "To kar ki sake kashe waya malama" Cikin sanyin murya tace "Toh" Yace "Kin yi breakfast?" Tace "Yanzu na tashi" Yace "To yi breakfast din ki fito" Ta daga kai tace "Ina?" Yace "Waje... Kar ki wuce tara da rabi zan tafi aiki" a hankali tace "Toh" katse wayar tayi ta mike ta shiga bandaki, kafin karfe tara tayi wanka ta saka kaya, ta bude warmer din da Ummi ta ajiye mata taga irish ne da kwai, ko kamshin abincin bata son perceiving, ta bude dayan taga kazan jiya ne tayi masa kamar pepper soup, lipton kawai Mayraah ta sha ta saka hijab dinta ta fita waje, zaune ta gansa cikin motar, he was on suit, ya ajiye wayarsa bayan ya ga ta fito, ta karasa jikin motar ta bude tana kallonsa a hankali tace "Ina kwana" Yace "Lafiya lau, how was ur night?" Tace "Alhmdlh" yace "Kinyi breakfast din?" Tace "Nayi" Yace "Karatun fa?" Kai kawai ta gyada masa alamar tayi, ya ɗan yi shiru, ita dai kallonsa kawai take, can yace "Baki bukatan komai?" Tace "Ba komai" Yace "If there is anything ki kirani, zan je aiki yanzu" Tace "To Allah ya tsare" Yace "Ameen, sai anjima" ta gyada masa kai ta juya ta koma ciki. Maheer na kwance parlor idonsa a lumshe kamar me bacci amma ba baccin yake ba, yana jin Haseenah a kitchen tana ta soye soye tun karfe takwas, jin an bude kofa ya bude idonsa, Badiyyah ce ta shigo parlon kamar ba ita ke dingishi jiya ba, ta dawo garas abinta, ta ɗan sosa kai tace "Ina kwana yaya?" Yace "Lafiya lau..." Sai ga Haseenah ta fito daga kitchen da tray din breakfast tayi ma Maheer, kallo daya tayi ma Badiyyah ta dauke kai ta isa dai dai inda yake kwance ta ajiye duk da tun jiya bata ga fuskarsa ba tana murmushi tace "Honey ga breakfast nayi maka" Bata jira me zai ce ba ta bude cooler din ta fara debar
Chapter 112 · 0% Book details