Sashe 297
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
kan kujera, hakan yasa ta karasa ta tada sallah... Sosai Mayraah ta sake da Mom dinta few hours da zuwanta gidan, don har tambayarta tayi me zata girka mata, tana gaya mata kuwa ta sauka downstairs ta samu masu aikin gidan suka yi leading dinta zuwa babban kitchen din gidan, Ceo kuma na study room dinta, sai da aka yi Magrib sannan Mayraah ta kai ma mahaifiyarta girkin da tayi mata, ta sake dawowa downstairs ta yanka mata fruits ta kai mata, Aaria na kallonta bayan ta ajiye fruits din a hankali tace "Amma a nan zaki ci kema ko?" Mayraah tayi murmushi tace "Ban yi serving din Aunty ba, she is downstairs" Aaria tace "Ohk, i will wait for you" Daga haka Mayraah ta fita ta sauka downstairs don Ceo na can a zaune, ita ma ta kai mata abincin dining area da fruits, ta sanar mata sannan ta tafi sama gun Mahaifiyarta suka ci abincin tare. Karfe takwas da rabi Mayraah ta sauko downstairs bayan mahaifiyarta ta sha drugs dinta ta kwanta don bata wuce time din bata yi bacci ba, kuma tana gefenta har tayi bacci sannan ta fito daga dakin, Ta karaso cikin parlon tana kallon Ceo ta zauna don ita ce tace mata idan Mom dinta tayi bacci ta sameta downstairs, Ceo na kallonta tace "Tayi baccin ko?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Eh tayi" Ceo tace "Come closer" Mayraah ta mike ta isa kusa da ita ta zauna, Ceo na kallonta tace "Akan maganar aurenki, ki gaya min gaskiyar abinda ke ranki dear, nasan tun bayan da aka yi calling off din aurenki wancan lokacin kin cire ranki da wannan auren, so now tell me the truth are you still interested in that guy after all what that happened? Sannan if i am not mistaken akwai wani magana da naji kawun nasa yayi kan cewar shi ma yana da wata maganar a kasa, i don't know ko ni kadai naji hakan a parlon ranan...." Ceo ta kalli kofar shigowa parlor sannan ta kalli mai aikinta da ta fito daga wani bangare a parlon da sauri ta karasa ta bude kofar, tun da ya shigo Mayraah ke kallonsa kafin ta sunkuyar da kanta, ya karaso cikin parlon da ladabi ya gaida Ceo, tace "How are you Aliyu, why are you coming this late?" Da ladabi yace "Ma'am i just arrived not long ago" Ceo ta sauke ajiyar zuciya tace "Ohk, what is it you want to discuss with me?" Ya ɗan kalli Mayraah suna hada ido tace "Good evening" Yace "Evening how are you" Ceo ta nuna masa kujera tace "Have a sit" Ya karasa ya zauna, tana kallon Mayraah tace "Get him water" Mikewa tayi ta nufi kitchen, Ceo ta cire glasses din idonta ta ajiye, shi dai kansa na kasa, bayan some minutes Mayraah ta fito rike da tray me dauke da ruwa da lemo da glass cup, ta karasa har gabansa ta durkusa ta ajiye masa sannan ta mike zata bar parlon Ceo tace "Ai bamu gama magana ba, zo ki zauna" Mayraah na tafiya a hankali ta karasa inda take zaune da farko ta zauna, Shi dai MD bai dago kansa ba, Ceo tace "I am listening Aliyu" Sai a sannan ya dago kansa yana kallonta cikin nutsuwa yace "Ma'am i think, i can discuss it with you at the second parlor" Ceo na kallonsa tace "Why not here?" Sai kuma ta dafa Mayraah tace "Does she look like a stranger? C'mon Aliyu" Mayraah ta ɗan kallesa suka hada ido, shi ya fara dauke idonsa, a hankali yace "Ma'am, dama ba wani abu bane, kawai na zo in sanar maki zan ajiye aiki ne...." Da sauri Mayraah ta daga kai tana kallonsa kamar yanda Ceo ma ke kallonsa, Shi dai bai dago kansa ba, calmly ya ci gaba yace "I will be going back to Canada to work as a Medical Doctor" A hankali Ceo tace "Why Aliyu?" Sai a sannan MD ya daga kai ya kallesu ya ɗan yi murmushi a hankali yace "I am glad i had the privilege to serve u and ur great hospital, i will forever be grateful, and i will love you to honor Dr Khalil..." Ya sunkuyar da kansa yace "Don ta dalilinsa Mayraah ta fara aiki a asibitin, he did all he can na ganin ta fara aiki, wanda sanadiyar haka yasa tayi reuniting da iyayenta da mu relatives dinta" A hankali Ceo tace "Aliyu" Ya daga kai yana kallonta, tace "Iyayenka suka ce ka ajiye aiki ko?" Girgiza kai yayi murya can kasa yace "Not at all Ma'am, babu wanda yace in ajiye aiki, ra'ayina ne ajiye aiki" Yana kai wa nan ya mike ya isa har gabanta ya ajiye mata letter of resignation dinsa politely, Mayraah dai sai kallonsa take....