Sashe 123
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yace "Ya aka yi Badiyyah?" Badiyyah ta dawo gefensa ta langwabar da kai ta marairaice murya tace "Yaya dama don Allah akwai wani abu da nake son siya ne, kuma bani da kudi wllh" Yace "Ohk nawa ne kudin" ta sunkuyar da kai tace "Dubu hamsin" Yace "To zan tura maki" Da sauri ta kallesa ta wani washe baki tace "Nagode sosai yayana, Allah ya kara maka budi" Yace "Ameen" Juyawa tayi cike da farin ciki ta koma dakinta, Haseenah ta dinga kallon Maheer da yaki kallonta ya kulle kofarsa, kofar ta nufa a fusace ta bude ta shiga ta tsaya tana kallonsa tana huci tace "Maheer tun yaushe nake ce maka ina bukatar kudi kaki bani shine yanzu zaka dau har dubu hamsin ka ba ma wancan gantalalliyar da sae dae ta siya kwaya da kudin? dama da ni da ita wanene haƙƙinsa ke rataye wuyanka? wanene yafi cancanta ka ba ma kudi tsakanina da ita?" Maheer ya daga kai ya kalleta yace "Ita ma haƙƙin nata ya kusa dawowa wuyata gaba daya kamar yanda naki haƙƙin ke wuyata, daga sannan zaki ga ita ma ta cancanci a bata kudin" kallonsa Haseenah ta dinga yi babu ko kiftawa as if trying to understand what he meant by saying so, can dai tana stammering tayi karfin halin cewa "Ban fahimci abinda kake nufi ba Maheer" A takaice yace "Zaki fahimta nan ba da dadewa ba, dama bana son ki fahimta da wuri sae lokacin yayi" Yana fadin haka ya mike ya fita daga dakin ya bar ta tsaye tana bin sa da kallo kamar idanuwanta za su fito tsabar kidimewa. Daren ranan nan Haseenah bata yi baccin kirki ba, da tayi zata farka a firgice saboda mafarkin Badiyyah, daga karshe ma parlor ta dawo ta zauna, ita ba sallah ba balle salati, da asuba tana jin Maheer ya fito daga dakinsa, tsaye yayi corridor yaki karasawa parlon ganin wutan parlon a kunne, can dai ya ɗan leka ya hango Haseenah zaune tayi tagumi, tun da aka kawota gidan bai taɓa ganin ta tashi da asuba ba, ko ya tasheta tayi sallan asuba bata tashi, yawanci sai gari ya waye tar take sallan asuban ta, yana ganinta a parlon ya nufi dakin Badiyyah ya fara knocking kofar dakin, Haseenah ta daga kai da sauri jin yana kwankwasa kofar dakin Badiyyah, mikewa tayi tana lekan corridor din taga ya bude kofar dakin yana kallon ciki yace "Ki tashi kiyi sallah lokaci yayi" Haseenah ta koma kan kujera ta zauna da sauri, ita kanta bata san wani kalan abu take ji a ranta ba tun daren jiya, har wani heartburn ke damunta tsabar tashin hankali, Maheer ya fito Parlon yayi mata kallo daya ya wuce masallaci, ta mike ta hau zaga parlon tana jin zuciyarta na mata tukuki, maganganun da ya gaya mata jiya a dakinsa ne kawai ke yawo mata a ka, daga karshe ta shige dakinta tana wani murmushi. Karfe goma saura Badiyyah ta fito daga dakinta, baccinta tayi har da minshari daren jiya tun bayan da Malam Dauda ya bata assurance babu wanda ya isa ya koreta a makarantar, sanye take cikin riga da skirt sai ɗan figigin mayafinta da handbag alamar fita zata yi, Haseenah na zaune dining area abun duniya ya taru ya mata yawa tayi nisa cikin sake saken da take a zuciyarta na nema ma kanta mafita, bata san ma sanda ta fito parlor daga cikin dakinta ba har ta zauna kan dinning chair tsabar tunani, ɗaga kai tayi jin kamshin turare ya baɗe parlon, suka hada ido da Badiyyah, sai da taji wani mugun faduwan gaba, Badiyyah ta nufeta tace "Ina breakfast din Haseenah?" Wani bacin rai da takaici ya zo ma Haseenah har wuya ta dinga jin zuciyarta na wani tafarfasa tayi mata banza ta ki cewa komai, Badiyyah ta bude coolers da ta gani kan dinning taga babu komai ciki, ta wuce kitchen nan ma taga ko ruwan zafi Haseenah bata dafa a gidan ba, Badiyyah ta fito a fusace tana kallonta tace "Amma dai gaskiya baki kyautawa Haseenah, wannan ai mugunta ce da baƙin hali, yanzu haka kike son in fita ban karya ba kenan? mutum na gidanki amma ki dinga barin sa da yunwa saboda ke muguwa ce" still Haseenah ta mata banza sae girgiza kafa take, juyawa Badiyyah tayi a mugun fusace ta nufi corridor zuwa dakin Maheer kamar zata tashi sama, ta kwankwasa kofar tana jiransa ya bude, yana bude kofar tace "Yaya wai kana ganin yau ma Haseenah bata yi ma mutane breakfast a gidan nan ba ko? Haka jiya ta sa na tafi exam hall ban ci komai ba nayi exam din ina jin yunwa da jiri na gama na fito, yanzu kuma zan je gidan Hajja na je zan dau breakfast naga ko kunna gas din matar nan bata yi ba" Duk Haseenah na jin abinda Badiyyah ke cewa saboda cikin daga murya take maganar, Maheer ya fito daga dakin ya dawo parlor Badiyyah na biye da shi a baya, kallon Haseenah dake zaune dining yayi yace "Ke me yasa baki girka breakfast din ba?" Haseenah ta masa wani matsiyacin kallo tace "Ko kai yau baka isa in maka breakfast a gidan nan ba balle wata katuwa can" Badiyyah ta nufeta tana huci tace "Shi yayan nawa kike gaya ma magana haka saboda baki da tarbiya??" Haseenah dai taki ce mata komai don tana buda baki bata san kalan tereran da Badiyyah zata mata ba a wajen shi yasa tayi mata shiru tun daxu, Maheer na kallon Badiyyah yace "Ki shiga dakina ki dauko min makullin mota in ajiye ki gidan Hajjan, idan kin je can sai kiyi breakfast din" Badiyyah ta galla ma Haseenah wani harara ta bar parlon, Haseenah ji tayi kamar numfashinta zai dauke don takaici, wai Badiyyah taje dakinsa?? to ko Mayraah da ta zauna gidan nan bata taɓa tsayawa bakin kofar dakinsa ba balle ta shiga dakinsa, wasu hawaye ne suka cika idonta ba tare da ta sani ba, a haka Badiyyah ta dauko makullin motarsa ya amsa tayi ma Haseenah gwalo ta bi bayansa suka fice daga parlon, Haseenah ta fashe da matsanancin kuka ta zamo kasa ta zauna tace "Na shiga uku na lalace ta ina zan fara ni Haseenah" Maheer na ajiye Badiyyah kofar gidan Hajja ta sauka tana kallonsa tana washe baki tace "Baza ka shigo ku gaisa da Hajja da Ammi ba Yaya" Ya dake yace "Sauri nake" Daga haka ya ja motarsa ya bar wajen ta dinga daga masa hannu kafin ta shiga gidan cike da farin ciki, sai da ta tsaya jikin kofar parlon ta kasa kunne, Hajja dake zaune parlorn rike da cup din kunu tana kallon Ammi dake linke kayanta cikin akwati tace "Hakuri kawai za ki yi, ko don yaron nan Maheer, dubi yanda ya daga hankalinsa kullum sai ya zo gidan nan yaro ɗan albarka me gudun zuciyar uwarsa, ga kuma Umar da ke hanya gobe, kin ga bai kamata ya dawo ace baki gidan ba tunda shi bai san abinda ke faruwa ba har yanzu, gwara kuma da ba a gaya masa ba kar aje karatunsa ya samu matsala, amma wannan yaron naki Usman kam ki binkita ko canja maki shi akayi a asibiti gaskiya" Ita dae Ammi bata ce komai ba hada kayan nata kawai take, Hajja tace "Duk ɗan kwarai baxai banzatar da uwarsa yanda Usman yayi ba...." Ammi ta katseta tace "Yana fa kirana a waya ke ce dai baki sani ba Hajja" a fusace Hajja tace "Kiran banza kiran hofi, shi Maheer kiranki yake ba zuwa yake ba da yake yana son gamawa da duniya lafiya, kawai kin haifi jaraba kawai, azzalumin yaro, wllhi yana nan sae yayi mamakin matsayin da Badiyyah zata kai a rayuwar nan, kuma sae yayi da ya sanin duk abinda yayi mata, da na dauki duk jikokina daya a zuciyata amma yanzu kam kowa da matsayinsa wallahi, ko da wasa kada Usman ya nuna yasan Badiyyah wataran" Ita dae Ammi bata sake cewa Hajja komai ba, Badiyyah ta bude kofar parlon ta zube kasa ta rushe da kuka sosai ta kwanta, tsabar gigicewa sae da Hajja ta kusa zubar da kunun hannunta ta mike da sauri ta nufeta tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, lafiya Badiyya, me ya faru" Ammi ma ta nufeta hankali a tashe, Cikin kuka Badiyyah tace "Hajja jiya za mu yi jarabawa a aji na manta na shiga da wani takarda a hannuna shine Mayraah ta kira wata malama a ajin tace mata gani can na shigo da satan amsa, kuma wallahi ba satan amsa bane wani takarda ne daban, yanzu an koreni a makarantar gaba daya Hajja" Hajja ta juya ta kalli Ammi da ta nemi waje ta zauna tana kallon Badiyyah da mamaki jin abinda take cewa, ita dai Badiyyah rusa kuka kawai take duk ta cika parlon da kururuwarta tana cewa ita fa an koreta a makaranta saboda Mayraah, Hajja tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ita Mayraahn ta maki wannan sharrin? kuma ke baki da bakin da zaki ce masu ba satan amsa bane a hannunki Badiyyah? Yau ga matsiyaciyar yarinya, sai yanzu na kara tabbatar da karin maganar nan na Hausa da suke cewa tsintattciyar mage bata mage, In da can suna mata kallon er uwarki a makarantar ke baza ki buda baki kice masu babu abinda kika hada da ita ba yanzu ba ma ta gidanku? Iyye Badiyyah?" Cikin kuka Badiyyah tace "Babu wanda ya saurareni wallahi Hajja, kawai korata suka yi" Ammi da duk jikinta yayi sanyi ta mike ta shiga daki tayi dialing number Maheer har ya katse bai daga ba, ta sake kiransa nan ma no response, ta fi minti biyu tsaye parlon kafin ta dawo parlor, taga Hajja zaune ta cika famm kiris ya rage ta fashe, Ammi ta kwantar da murya tace "In sha Allahu ma ba a koreki ba Badiyyah, na kira Maheer ina jin ba ya kusa da waya da sai in ji yanda za ayi ko zuwa makarantar za ayi a samu malaman in ya kama ko nawa ne a basu su yi hakuri, kuma ke ma ai tun jiya kuna fitowa daga exams din ya kamata ki zo ki sanar da