Sashe 21
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
masa fada ne da taga yana jibga kayan nan ta tsawatar masa, Musharraf baya jin maganan kowa babu wanda ya isa ya saka shi ya hanasa a duk cikin mu, kuma ba kowa ke mara masa baya yake abubuwan nan ba sai uwarsa, ta dauki son duniya ta dora masa, duk ya bi ya raina mutane baya ganin kowa da gashi, yarinyar da aka ce a can wajajen kurnan ɗan asabe take kafin a karasa mil tara can hanyar Daura shine za a hada ma uban kayan nan? Local girl irin wannan ne za ayi ma wannan kaya fisabilillahi jama'a kuyi alkalanci fa?" Aunty Fatima da ranta ya riga ya gama baci tace "Gaskiya Aunty Halima babu abinda za a rage a kayan nan tunda babu sisin kowa a ciki, in ma akwai to nasan bazai wuce na mahaifiyarsa ba ko yayansa, don haka yanda kayan nan suke a nan haka za mu dauka mu kai su..." Aunty Halima ta mike a fusace ta dakatar da ita tace "Ke kar ki gaya min magana Malama, yanda kike ganin kuna da iko da Musharraf to mu mun ma fi ku iko da shi, bar ganin kunyi bake bake kan lamarinsa kun mayar da mu bare, to wannan karan bari kiji sai abinda mu dangin uba muka ce za ayi ba dangin uwa ba, ku kun gama playing part dinku kuma haka, wannan zancen aure ake ba na wasan yara ba don haka mune tsaye kyamm akan lamarin nan ko mutum ya so ko ya ki, kuma ni Hajiya Halima nace baza a fitar da duk kayan nan daga parlon nan ba sai an rage su tunda ba fashi da makami Musharraf din yake ba" Mami that was calming herself down tace "Yanzu ke meye ribar yin haka Hajiya Halima? Idan aka kai ma Farrah kayan nan dama ba da hannu bibbiyu zaki amsa ba?" Hajiya Halima tayi wani shewa tace "Of course da hannu bibbiyu zan amsa saboda Farrah tayi deserving dinsa, ita kuwa yarinyar da za a kai ma er talakawa ce bata yi deserving ba bata san value dinsu ba, iyaka ma ta walakanta su ta kashe su kafin shekara daya, ni nan da kike gani bana shakkar fadin gaskiya a ko ina wallahi ko a mutu ko ayi rai, yau da Yaya yana da rai ai shima bazai bar ɗan sa yayi wannan almubbazzarancin ba da sunan hada kayan aure, kayan auren ma na yar talaka" Tana fadin haka ta fara rage laces da atamfofin da suka fi tsada tana jefawa kan kujera a fusace, Aunty Baby ta rike haɓa tana ganin ikon Allah, Mama Harira warce ita ce yayar Abbansu Musharraf tace "Kinyi kuskure babba Maryam da har zaki bari yaron nan ya kashe kudi haka wajen hada kayan aure, yo wannan ko er gidan sarauta ai sai haka, banda an ware mu bama sanin duk abinda ke faruwa ai baza mu bar wanna abu ya kasance ba, don haka dole ne sai an rage kayan nan, kuma ko da mun kai kayan ba tare da an cire ko daya ba bana tunanin za su iya bamu tukuicin da ya kamata tunda naji Halima tace a Kurna yarinyar take, banda rashin tunani irin na Musharraf ina shi ina ita? Ga er uwarsa Farrah kowa yayi masa sha'awa amma yaron nan yaki, dama gida bai koshi ba a ina aka taɓa kai wa waje? To dai duk kece me babban laifi tunda baki nuna masa haka ba" Mikewa Mami tayi ta fice daga parlon ta wuce sama, Hajiya Halima da su Ruma'isa suka bi ta da harara, Daya dattijuwar Mama Karima tace "Sam abun dai babu tsari, an raina mu ba a dauke mu bakin komai ba, duk ku cire abinda ku ka ga ya kamata a cire ai ba er gwal bace" Friends din Mami gaba daya where speechless and shock, suka dinga kallon yanda Hajiya Halima da Rumaisa ke kwashe kayan lefen ba tsoron Allah, mikewa Aunty Fatima tayi ta bi Mami zuwa sama, zaune ta ganta a parlonta tana waya, Aunty Fatima ta rungume hannunta tana tsaye jikin kofa kana ganinta kasan she is boiling from inside ita ma, Mami tace "Ni bance ka kirasu ba Daddy amma wllh idan na tashi rashin mutuncina kare bazai dauka ba wllh, na gaji da abinda dangin babanku suke min, akan me? After so many years baza su bar ni in huta ba sai bibiyata suke da sharri?" Daga daya bangaren Daddy yace "Mami pls kiyi hakuri kar ki ce masu komai, ko kayan nawa suka cire ni zan tura kudi ayi replacing ko washegari ne sai a kai sauran kayan, and pls don't say anything to Musharraf kinsan halinsa" Mami tace "Wallahi na gaji, wannan ai cin mutunci ne da cin fuska a gaban kawayena fa" Daddy ya sauke ajiyar zuciya yace "Pls kiyi hakuri, everything will be okay in sha Allah" Musharraf yayi parking ya sauka daga cikin motarsa yana kallon machine (Bike) din da yayi zoom off leaving the security guy a tsaye da envelope a hannunsa, Musharraf ya karasa gun security man din yace "Na meye wannan?" Mai gadin yace "Yanzu wani me babur ya bani wai a kai ma su Hajiya" Musharraf yace "Okay" Daga haka ya amshi envelope din ya shiga cikin compound din yana unsealing dinsa ya ciro takardan ciki ya warware yana jujjuyawa, he was surprise to see rubutu jikin takardan, babu bata lokaci ya fara karanta content din, ko 30 seconds bai yi da fara karantawa ba yaji ya kasa ci gaba da tsayuwa, yayi saurin jawo farin kujeran dake kusa da dakin mai gadi ya zauna, lkci daya yaji zufa na taho masa, kan kace me har ya gama karanta content din takardan sai kuma ya fara kokarin apprehending abinda ya karanta, after few seconds of trying to apprehend yayi squeezing din paper din a hankali ya cusa a aljihunsa.....