← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 277 OF 313

Sashe 277

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*_SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA_*👌🏽👌🏽👌🏽 A cikin babban compound din gidan Abba yayi parking bayan mai gadi ya bude masa gate, MD yayi leading dinsu har cikin parlon gidan don tun basu iso ba Maheer ya kirasa ya sanar masa suna hanya, Ammi dai ta rasa dalilin da yasa gabanta ke ta faduwa tun da suka baro gida, MD ya kara gaida Abba a parlon, Abba ya amsa da fara'a yana kallonsa, ita dai Mayraah na zaune kusa da Ammi sai da suka hada ido da Ammi ta sauke idonta ta gaishesa, amsawa yayi ya tambayeta ya jiki, tace "Alhamdulillah" Kamar yanda MD bai kalli direction din Usman ba balle su gaisa haka shi ma Usman ko kallon inda yake bai yi ba, ita dai Ammi ta kagu ayi godiyar da Abba yace su koma gida, ba a wani dau lokaci ba Ceo ta sauko downstairs sanye da doguwar riga sai rosary dake wuyarta, Mayraah dai sai kallonta take har ta karaso cikin parlorn tana tafiya a hankali, tun da Ammi ta kalleta sau daya ta dauke kai, cikin sanyin murya Ceo ta gaisa da Abba sannan suka gaisa da Ammi ma, Maheer da Usman ma suka gaisheta ta amsa da murmushi fuskarta, tana hada ido da Mayraah, Mayraah ta gaisheta, Ceo ta sauke idonta ta amsa cikin sanyin murya sannan ta zauna parlon, tana kallon Ammi tace "Ya ta kara ji da jiki?" Ammi tace "Alhamdulillah, ta ji sauki" Ceo tace "Toh Allah ya kara mana lafiya gaba daya" Ammi tace "Ameen" Ceo tace "Ko a kawo breakfast, since it's still early" Da sauri Ammi tace "Alhamdulillah, mun yi breakfast" Ceo tayi shiru bata sake cewa komai ba, daga Abba har su Maheer da MD kallonta suke, ita kuwa Ammi tana ta jira ayi godiya su fita parlon, kuma taji duk an yi shiru, Bayan few seconds a hankali Ceo tace "Nasan Aliyu ya kai maku wata magana me ban al'ajabi ko kuma ince that is confusing but not hard to believe, don da hakan bai yi making any sense a wajen ku ba baza ku fara zuwa gidana ba, amma it made a lot of sense because..." Sai kuma tayi shiru kanta a kasa Abba da su Maheer dai kallonta kawai suke, Ammi taji gabanta ya yanke ya fadi ita duk zaton ta zargin da tayi jiya na cewa ko an gano wani illan da poison din yayi ma Mayraah ne ya tabbata, ita kanta Mayraah jin abinda Ceo tace sai da ya daga mata hankali a lokacin, Calmly Abba yace "Muna bukatan more highlight on that, yes it made sense but we need explanation" Ammi ta kalli Abba hankali tashe tace "Yallabai me ke faruwa?" Abba na kallonta cikin kwantar da murya yace "Ki kwantar da hankalin ki, kuma ina nema alfarman kar ki sake cewa komai a parlon nan, just listen" Ammi ta sunkuyar da kanta gabanta na faduwa, Ceo na kallon Abba a hankali tace "Ranan 5 ga watan 5 a garin Adamawa, shekaru ashirin da biyu da suka wuce an ajiye jaririya a cikin kwali ɗan nesa da wani rijiya kusa da masallaci me koren fenti" Ammi ta daga kai da sauri ta kalli Ceo bata ko kiftawa, sai kuma ta kalli Abba da sauri taga kallonta yake, Mayraah ita ma sai kallon Ceo take babu ko kiftawa, Ita dai Ceo bata yarda ta dago kanta ba ta ci gaba a hankali tace "Zai iya kasancewa ku ba a nan ku ka sameta ba, probably ko an kai ta gidan Marayu ne, or anything of such dai, but nasan dole za ayi keeping wannan record din ko ma ina ku ka sameta" Tana magana ne hawaye na sauke idonta tana gogewa da karamin towel din hannunta kuma har sannan taki daga kai ta kallesu, Abba yayi karfin halin cewa "Dr, amma don Allah ke wacece, kiyi mana bayani yanda za mu fahimta plss, how did u know all this" Ceo ta daga kai a hankali tana kallonsa tace "Ina son in fara sanin a inda ku kuka sameta kafin in ci gaba" Abba ya gyada kai da sauri yana kallon Ammi da idonta ya cika da hawaye ko kwakkwaran motsi bata yi a inda take zaune tana kallon Ceo, sai kuma ya maida dubansa kan Ceo yace "Dai dai yanda kika fada, haka ne" Ceo na goge idonta muryarta na rawa tace "To Mahaifiyarta na sama" Mikewa Ammi tayi zata bar parlon Abba ya dakatar da ita, har sai da ya mike ya nufota sannan ta koma a hankali ta zauna hawaye na sauka idonta, kamar yanda yake sauka idon Mayraah da jikinta ke bari jin abinda Ceo ke cewa, Abba bai koma kujeran da yake ba ya zauna kusa da Ammi yana share zufar dake keto masa a goshi da handkerchief din hannunsa yace "Don Allah Dr har yanzu a duhu muke, plss we need a better explanation, date da rana da kika ambata da ma exact spot duk haka ne we are not disputing that, ni ne nan na fara ganinta that very early morning" Ceo dai kallonsa kawai take bata ko kiftawa kamar bazata ce komai ba hawaye na sauka idonta, sai kuma ta sunkuyar da kanta da kyar tace "Labarin me tsayi ne Alhaji" Abba yace "We have all day pls" Usman dai ya sunkuyar da kansa duk yana sauraron abinda take cewa, unlike Maheer da MD dake kallonta all waiting to hear what she have to say eagerly, Cikin sanyin murya Ceo tace "I will make it brief...... My dad was a Muslim, Mahaifiyata kuma came from a Christian home, so she is a christain, my father was a military personnel wanda aiki ya kai sa kudu har ya hadu da Mahaifiyata a can ya aureta without the consent of her parent that were strictly against the marriage because her father was a devoted pastor, infact she came from a reputable Christian family, ta dalilin haka har disowning dinta iyayenta suka yi amma bata damu da hakan ba saboda son da take ma mahaifina da ya rufe mata ido, babu dadewa da aurensu aka ma dad dina transfer zuwa Adamawa wanda nan ne asalin garin sa, sai dai he lost his parent at a very young age amma yana da yayyi mata hudu sannan shi, sai kuma sauran relatives dinsa, a Adamawa aka haifemu ni da kanwata warce na bata tazaran kusan shekara 7, babu tsanar da dangin Mahaifinmu basu nuna ma Mahaifiyarmu ba duk don kasancewar ta Christian, mind you Abbanmu bai taba forcing dinta ta amshi addininsa ba don tana Christianity dinta tana zuwa coci shi kuma yana addininsa na Islam, i have my muslim name that is Aisha as at then, kanwata Aaria kuma Maryam, kawai dai Abbanmu bai yarda ta kai mu church ba don islamiyya muke zuwa ma sannan, babu dama mom din mu ta shiga dangin Abbanmu ko yaya ne sun dinga kyara da tsangwamarta kenan a fili babu boye boye, tsana suke mata me tsanani, wasu suce mata warce bata kallon gabas, wasu su kira ta da kafura, wasu su ce mata arniya, wasu su ce mata karuwa, gashi bata da kowa nata a Adamawa sai Abbanmu wanda shi kuma ake yawan masa transfer gari gari don wataran sai mu yi wata shidda bamu sa shi a ido ba sai dai ya mana aiken kudi da kayan abinci, tsanar da ake ma Mom din mu a familyn Abbanmu ba iya ita kadai ya tsaya ba, har mu hakan ya shafa kiri kiri suke nuna mu ba jininsu bane, ko mun je inda suke sai su kore mu, ko sunanmu basa kira sai dai su kira mu da 'ya yan kafura ko 'ya yan Arniya, don sun ce kaf zuri'arsu wai babu kafuri kuma baza a fara ta kan kaninsu ba, infact basu ma yarda mu din 'ya yan Mahaifinmu bane, his relatives made life a living hell for our mother and us in Adamawa, mun sha wahalansu sosai" Shiru tayi tana goge hawayen dake sauka idonta trying hard to control her self, bayan few seconds ta ci gaba da kyar tace "Ba iya family din Abbanmu ba, hatta anguwan da muke mutanen cikinsa basa wani son hulda da mu saboda Mahaifiyarmu ba musulma bace tana zuwa coci don a sannan ana yawan samun religious crises a arewacin Nigeria, kuma anguwan da muke duk majority musulmai ne unlike now da akwai Christians da yawa a Adamawa with different languages sannan civilization ya bazu ko ina yanzu ana zaune lafiya da juna sai dai abinda baza a rasa ba, all this while mom dinmu bata waiwayi garinsu a kudu ba ko da wasa sanin yanda ta rabu da iyayenta da danginta, i was 12 years old Allah yayi ma Mahaifinmu rasuwa bayan harbesa da aka yi a wani operation da suka fita, our mother was depressed and shattered after receiving this bad devastating news of our fathers death, ya zamana bamu da kowa kuma a garin Adamawa, ana 40 days da rasuwan Abbanmu yayyinsa mata da danginsa suka zo suka dauke duk wani abu da ya bari na dukiya wai basu yarda cewar mu 'Ya yansa bane dama, kawai ya dauko Mahaifiyarmu ne a kudu suna zaune ba tare da aure ba don haka bamu da gadonsa islamically, we were left with nothing sai gidan haya da muke ciki wanda Abbanmu bai jima da biyan rent din ba ya rasu sai foodstuffs da shima bai dade da aiko mana ba" Ceo na goge hawayen dake zuba idonta ta ci gaba tace "Ina jss3 a lokacin a wani private school Aaria kuma tana primary school, tun bayan rasuwan Abbanmu mom dinmu ta rasa lafiyar ta saboda shock din da ta shiga, yau ciwo gobe lafiya duk ta fita hayyacinta, a haka cikin ruwa cikin zafin rana zata fita duk inda zata samu aikatau tayi duk don ta kula da mu, wani lokacin ma haka zata dawo bata samu aiki ba sai dai mu kwana da yunwa, I have my class mate then a makarantar da Abbanmu ya saka mu kafin ya rasu duk da mun daina zuwa makarantar saboda babu halin biya don ta abincin da za mu ci ma Mom din mu
Chapter 277 · 0% Book details