Sashe 227
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ur evidence via 07087865788 Mayraah na isa kofar dakin tayi knocking, after a while ya bude kofar, shi in dai aka masa knocking baya bada izinin shigowa sai dai ya tafi da kansa ya bude kofar don bai fiye son ana shigo masa daki ba, she is already used to that, tana ganin ya bude kofar ta bi gefensa ta shiga ciki ya bi ta da kallo sai kuma ya kulle kofar ya karasa ciki yace "But i said later in the night" Mayraah ta zaro ido tace "To yanzu yaushe ne yaya? Everywhere is dark already" Zaunawa yayi yana ci gaba da abinda yake yi a laptop yace "Ai ba ayi isha ba" Ta turo baki tace "Yaya ni dai i am eager in ji maganar me zaka min, is it about my dressing dazu?" Ya kalleta yace "Ai Ammi tace dressing din ya maki kyau" Murmushi tayi tace "In dai shine ni dai kayi hakuri, nace maka bazan kara ba" Yace "Ba shi bane" Tayi shiru tana kallonsa, ya kashe laptop din ya ajiye yace "I just want to know what ur next plan is.... 2 years back kinyi saukan Al-qur'ani, this year kin yu graduating from university, immediately after graduation kin samu aiki, so what do u have in mind next?" Ta ɗan yi murmushi ta sunkuyar da kai tace "Kamar me fa yaya?" Yace "Ko iyakar burinki kenan a rayuwa?" Ta daga kai a hankali ta kallesa, she wish zai gane yanda ta zama desperate ta hadu da nata relatives din ko da guda daya ne, bata son ta zama an ingrate shi yasa take kauda tunanin nan ko da yaushe a ranta bata basa mafaka ba balle ya dameta, amma God knows in this few months har cikin zuciyarta tana son sanin ko da mutum daya ne a jininta, sauke idonta tayi bata ce masa komai ba, a hankali yace "Kinyi shiru" Tayi gathering courage tace "Duk wani abun Alkhairi will always be among my wish everyday Yaya, ba ni kadai ba kowa ma ina masa fatan abun alkhairi ya same sa kullum" Yace "Mayraah" Ta daga kai ta kallesa yace "So in ur wish there is nothing like marriage?" Ta ɗan buda ido, sai kuma tayi murmushi ta sunkuyar da kanta tace "Ai lokaci ne yaya, idan Allah ya kawo lokacin za ayi" Yace "Tell me the truth, is there anything between u and that Dr? I mean Dr Khalil" Mayraah ta zaro ido tace "Not at all wallahi, shi da yake da mata da yaransa biyu" Usman yace "Ohk ba a auren me mata?" Tayi dariya tace "Aa nima ban sani ba" Yace "Baza ki iya auren mai mata ba kenan?" Ta sunkuyar da kai tace "Ni dai ba ruwana" Yace "Abokina me mata ya ga hotonki yace yana so yanzu baza ki iya aurensa ba kenan?" Ta daga kai ta kallesa, sai kuma ta turo baki bata ce komai ba, yace "Am serious" Shiru tayi tana kallon sa, ya sauke idonsa yace "Wasa nake bai da mata, he is single, a Barrister too, are u interested? maganar da za mu yi kenan dama" Nan da nan jikinta yayi sanyi don Musharraf ne ya fado mata, Shi dai Usman kallonta kawai yake examining her reaction at the same time, bayan few seconds tace "Yaya i don't think i will love again...." Hawaye ya cika idonta ta fara gogewa da sauri, shi dai yayi shiru yana kallonta, can yace "Mayraah" ta daga kai ta kallesa tana share idonta, yace "Why won't u love again" Ta fashe da kuka tace "I don't want to remember the pass, ko ma waye zai aureni yanzu dole sae ya fara sanin ko ni wacece, after that no parent will want their blood to marry me" Yana kallonta a hankali yace "Har Ammi da Abba?" Daga kai tayi ta kallesa as if trying to apprehend what he meant by so saying, Bai bata wannan space din ba yayi saurin cewa "Forget that pass u are talking about and concentrate on the future Mayraah" Ita dai bata ce komai ba sae kallonsa take, yace "So i will want you to give this guy a chance" Nan ma dai bata ce komai ba, yace "Banda kula kowa kuma" Tayi murmushin karfin hali bata dai ce komai ba, yace "Promise me that" Ta kallesa kamar yasan abinda ke running a mind dinta yace "Kin dai san bazan yi abinda zai cuceki ba ko?" Ta sauke idonta, yace "So now make that promise baza ki kula wasu ba" Ta gyada masa kai tace "In sha Allah" Yace "You can leave" Mikewa tayi ta nufi kofa ta fita wasu hawayen na taruwa idonta ta koma dakinta. Wajen karfe tara bayan tayi wanka ta kira Maheer, Haseenah dake parlon ta mike jin wayarsa dake ajiye kan kujera na ring, shi kuma yana kitchen yana hada shayi, kallon screen din wayar ta dinga yi taga an sa Mimi with love emoji, ta dinga kallon wayar babu kyaftawa har ya fito daga kitchen, ta juya ta shige daki, ko kallon inda ta bi bai yi ba ya dau wayarsa bayan yayi picking Mayraah ta gaishesa, ya zauna yace "Ina kika shiga?" Tace "Kai dai zan tambaya, bayan tun dazu nake ta kiran wayarka" Yayi murmushi yace "Wayar na silent kika kira dazu, ya kike?" Tace "Alhamdulillah, ya aiki" Yace "Cool, kin je interview din yau?" Tace "Na je" Yace "No issues?" Kai ta gyada masa kamar yana ganinta, sai kuma tace "Ka fara processing transfer din naka yaya?" Yace "Not yet" ta ɗan hade rai tace "Do it soon pls, ko baka missing dinmu" Yace "I will try Mimi, ina missing dinku mana, ina Ammi?" Tace "She is in her room, Mama Ladi ta tafi ne?" Er dariya yayi yace "Jiya na kai ta har karayen wai bazata iya zaman motar haya ba" Mayraah tayi murmushi tace "Ayya, yanzu yaya idan ina son magana da sis Badiyyah ta ina zan sameta?" Maheer yace "I don't really know" Tace "I tried calling her lines severally amma duk a kashe" Yace "May be ta kashe wayar ne" Mayraah tayi shiru, shi ma haka, bayan few seconds tace "Pls try and request for the transfer kaji yaya" Yace "I will do so starting from tomorrow in sha Allah Mimi" Tana murmushi tace "Yauwa yayana, i want to go to bed now" a hankali yace "Alright Dear, sleep tight" Tace "Bye" Daga haka ya katse wayar, ya ajiye ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido, tun da suka koma Abuja sai dai ya sha tea ko coffee, idan ya fita kuma ya biya restaurant ya ci abinci, kana ganinsa kasan he is not himself, a da yayi niyyar ko zai nemi transfer din sai zuwa nan da wata biyu ko uku, amma yanzu kam yaji bazai iya ba, damuwa yayi masa yawa, ganin daga shi sai Haseenah na kara saka masa damuwar nan, don haka dole ma ya nemi transfer din nan ko ta yaya ne ya koma wajen family dinsa soon. Ranan Sunday da yamma Mayraah ta gama shiryawa ta fito daga dakinta zuwa parlon Ammi, Ammi dake zaune tana kallon TV ta kalleta tace "Ko dai mu bari zuwa gobe ko da daddare ne in kin dawo aiki mu je daughter?" Mayraah ta zauna gefenta tace "Aa Ammi mu je yau pls kin ga fa na riga nayi girkin, nasan goben a gajiye zan dawo" Ammi tace "Toh shikenan, mu je kawai..." Mikewa tayi ta shiga daki ta dauko gyalenta da jaka, sannan suka sauko downstairs, sai da Mayraah ta fara shiga kitchen ta dau warmer din tuwo da miyar ganyen da tayi ta kai mota, driver na compound yana jiran fitowarsu, Mayraah ta sanar masa inda zai kai su sannan ta bude ma Ammi back seat ta jira har ta karaso ta shiga ta kulle motar sannan ta tafi front seat ta zauna, tafiyar kusan minti talatin da biyar suka yi suka iso gidan, Drivern yayi parking bakin gate, Mayraah ta sauka ta dauko warmers din biyu, Ammi ma ta sauko daga motar ta sanar masa jiransu zai yi sannan suka shiga cikin gidan, Karime ce ta bude masu kofar parlon tana ganin Mayraah ta rungumeta cike da farin cikin ganinta tace "Sannunku da zuwa... Ku shigo" Mayraah na murmushi suka shiga parlon da Ammi, ta ajiye warmers din hannunta, bayan Karime sun gaisa da Ammi ta mike tace "Bari in yi ma Hajiyar magana tana daki" Ba a dau lokaci ba sai ga ta tare da Ummi, shigowa parlon Ummi tayi da fara'arta tana masu sannu da zuwa, Mayraah ta koma kusa da inda Ummi ta zauna ta gaisheta, Ummi ta amsa da fara'a tace "Kwana biyu ko leko mu kin ki yi Ilham, shine ranan Khalil ke ce min ai mamanki sun dawo Abujan ma gaba daya, ina jin ko kwana biyar ba ayi ba da ya gaya min haka" Mayraah na murmushi tace "Ai naje kano nayi sati biyu ne shi yasa Ummi" Ummi tace "Maa sha Allah, Maman taki ce wannan ko" Ammi dai murmushi kawai take, Mayraah ta gyada kai tace "Ita ce" Suka kara gaisawa da Ammi, Ammi ta mata godiyan rikon Mayraah da tayi, Ummi tace "Kai haba babu komai, ai yi ma kai ne" Mayraah tace "Inna na daki?" Ummi tace "Tana ciki, ku shiga ku gaisa" Mayraah tace "Nayi mata girki ne" Ummi tace "Ai ko kin kyauta wallahi, Allah maki albarka" Mayraah ta mike tana kallon Ammi tace "Ammi mu je ku gaisa da Inna" Mikewa Ammi tayi ta bi bayan Mayraah zuwa dakin inna, karime ta dau warmers din ta bi su a baya zata kai dakin, Sosai inna tayi farin cikin ganin Mayraah bayan sun gaisa da Ammi tace "Kai amma wannan er taki er albarka ce warce bata mance alkhairi, na dade ban ga yarinya me hankali kamar ta ba, ki ji fa har da girki ta min abun sha'awa, yaushe ma na samu haka a gidan nan, doya ce fa yanka hudu suka hadani da shi dazu kamar a fursin wallahi" Ammi dai murmushi kawai take tana kallon Inna, su da suka yi niyyar barin gidan da wuri sai da inna ta