← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 262 OF 313

Sashe 262

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ur evidence via 07087865788 Har bakin mota MD ya rako Maminsa, tun da suka fito asibitin Mami ce ke ta magana shi kam yayi shiru kansa a kasa yana biye da ita ba tare da yasan ma me take cewa ba, bayan Mami ta bude back seat tana kallonsa tace "Take care of ur self Daddy" Yayi murmushin karfin hali yace "Sure Mami, Allah ya tsare" Tace "Ameen" Daga haka ya juya ta bi sa da ido har ya shiga cikin asibitin, gaba daya ta kasa gane dalilin wannan sanyin da jikinsa yayi lokaci daya, let it not be what she is thinking fa, tunanin hakan yasa taji hankalinta ya tashi, a sanyaye ta shiga bayan motar tana kallon Musharraf, sai da suka kusa Airport Mami tace "Where will u be spending the night Musharraf?" Yace "Hotel" Mami tace "Aa, kaje gidan yayanka.... kuma bana son musu" Musharraf ya kalleta ta madubi yace "Kin fa san halinsa Mami baya son sharing komai nasa da kowa, kawai bata min rai zai dinga yi mu samu issues a gidan nan, ni kuma i don't want to have any issues with him, " Mami tace "Baza dai kayi abinda nace ba kenan" Musharraf yace "To na ji" Mami tace "Yaushe zaka dawo?" Idonsa na kan titi yace "Ko gobe da safe in sha Allah" Mami tayi kasa da murya a hankali tace "Plss Musharraf bana son ka kara zura jiki zuwan ka Abujan nan don Allah, kaga u are yet to recover fully, kar kaje ka kara shiga wani damuwar bazan ji dadin hakan ba, you know what u went through da yanda ka fita hayyacin ka for the past few months, banda ma rashin lafiya ne kaga da bazan bari ka taho Abuja ba har ma in biyo ka, infact i will prevent anything da zai sake hada ka da yarinyar, amma rashin lafiya ya wuce komai, kuma dukkanmu musulmai ne..." Musharraf ya ɗan yi murmushin karfin hali a hankali yace "Mami ni yanzu tsakanina da Mayraah ai sai zumunci, i gave up long ago cause babu hope din aure tsakanina da ita, ta riga da ta min nisa, and with the way things are going bana tunanin za a bari outsider ya aureta, sai ki ga kilan daya daga brothers dinta za a hadata aure da tunda da aure tsakaninsu, so i will keep on nurturing my heart to forget about everything, in kuma rabona ce ita baxan ce bazan aureta ba i will gladly get married to her, amma da kamar wuya" Mami ta sauke ajiyar zuciya tace "Na ji dadin da ka fahimci haka, Allah Ubangiji yayi maka zabi mafi Alkhairi a rayuwar ka, idan ma ita din ce Allah ya baka ita cikin ruwan sanyi, in ko akasin haka Allah ya baka warce ta fi ta" A hankali Musharraf yace "Ameen" MD na komawa office dinsa ya zauna ya rike kansa da yayi masa nauyi duk ya rasa tunanin da zai yi, it was something he never saw coming, bude kofar aka yi ya dago da sauri, Dr Khalil ya shigo ya karaso gaban table dinsa yana kallonsa yace "Are you okay?" MD ya mike yace "Sure... Pls akwai patient ward 5, ka ɗan dubasa zan je office din Ceo ne" Dr Khalil yace "Ohk...." Juyawa yayi ya fita, MD ya dawo kan sofa din office din ya zauna ya tallabi chin dinsa, ya fi minti sha biyar zaune a haka, daga karshe ya mike duk jikinsa ba kwari ya nufi kofa yana tafiya a hankali har ya fita ya kulle office dinsa, yana isa office din Ceo yayi knocking gently, sau uku yayi knocking din jin bata yi responding ba ya juya ya bar wajen kawai... Dab da Magrib Musharraf ya shigo dakin da Mayraah take, ya ajiye fruits da ya siyo mata, Umar kadai ne dakin sai Ammi, Ammi na kallonsa tace "Sannu da kokari Musharraf" Mayraah dai na rungume jikin Ammi tana bin sa da kallo, Ammi tace "Idan anyi sallah sai ku tafi can gida da Omar ka ci abinci" Musharraf da ya koma kusa da window ya tsaya yayi murmushi a hankali yace "I am okay Ammi" Ammi tace "Aa don Allah kaje gida ku ci abinci" Bai sake ce mata komai ba, ana kiran sallah shi da Umar suka fita zuwa masallacin dake cikin asibitin, ana idar da sallah Musharraf ya fita daga masallacin tun kan Umar ya mike, duk don kar yaje gidan cin abinci. Bayan Magrib MD na office dinsa ya daura forehead dinsa saman table ya ji wayar sa na vibrate, a hankali ya dago ya ga Ceo ce ke kiran sa, dagawa yayi tace ya sameta office, yace "Ohk Ma'am" Katse wayar yayi ya ajiye, sannan ya mike ya bar office dinsa, har ya iso office dinta he was absentminded don tafiya kawai yake tunaninsa na wani wajen daban, gently yayi knocking kofar sai da ta masa izini sannan ya shiga, yana isa bakin table din office din ya tsaya, bata yarda ta hada ido da shi ba duk da har sannan glasses na idonta but he could see how swollen her eyes were alamar ta yi kuka sosai, tace "Pls idan dad din Mary Ann ya zo ka kawosa office dina, i want to speak with him" MD yace "Ohk Ma'am" Daga haka ya juya ya fita wondering why she wants to speak to him directly, on a norms in ma wani bayani ne shi zata sanar ma ya gaya masa amma ba wai tace a kawosa office dinta ba, ba kasafai ake zuwa office dinta ba sai in baƙi tayi, downstairs ya tafi zuwa dakin da Mayraah take, bayan yayi sallama ya shiga, Ammi da Usman ne kadai dakin Mayraah na shan fruits din da Musharraf ya siyo mata a hankali don har sannan kirjinta na mata zafi da ciwo, Ammi na kallon MD tace "Hajiya ta isa kanon kuwa Doctor" MD yace "Aa basu sauka ba" Ammi tace "To Allah ya kai su lafiya" Yace "Ameen" Kallon Mayraah yayi, ita dai kanta na kasa tana shan fruits din gabanta, Ammi tace "Kaga jikin Alhamdulillah yau har tana shan kayan marmarin da kanta" MD yace "Haka ne... Sun shigo yi mata alluran?" Ammi tace "Eh nurse din ta shigo da taga tana shan fruits din sai tace zata dawo..." MD yace "Ohk, Alhajin zai shigo yau?" Ammi tace "Yana ma hanya yanxu" MD yace "Ohk, Ceo ke son ganinsa" Ammi tace "To yana shigowa zan gaya masa in sha Allah, dama dazu da safe yake maganar Bill, tun da har yanzu ko deposit ba a ajiye ba...." MD ya ɗan yi murmushi wanda iyakarsa lips, shi dai Usman bai kalli direction dinsu ba danna wayarsa kawai yake, MD ya juya ya fita daga ward din, yana fita ba dadewa Abba ya shigo, bayan ya ajiye ledan hannunsa yana kallon Mayraah yace "Ya jikin?" Ta gyada masa kai a hankali tace "Da sauki" Abba yace "Maa sha Allah, gashi har ana jin maganar taki ba kamar dazu da safe ba" Mayraah ta ɗan yi murmushi, Abba ya juya ya kalli Ammi yace "Ki sameni waje za mu yi magana" Mikewa tayi ta bi sa suka fita corridor din dakin, Abba na kallonta yace "Wa ya kira yaron nan zuwa asibitin nan?" Ammi tace "Wani yaro?" Yace "Wanda na gani zaune reception" Ammi tayi kasa da murya bayan ta gano wanda yake nufi tace "Wai Musharraf? Dubiya kawai ya zo yi yallabai" Abba ya wani hade rai yace "What for? Sannan wa ya gaya masa bata da lafiya har ya zo Dubiya?" Ammi da jikinta yayi sanyi ta kasa cewa komai, a fusace Abba yace "Am asking wa ya gaya masa bata da lafiya har ya zo asibitin" A hankali Ammi tace "Maheer ne ya kirasa saboda hankalinta ya kwanta, dazu da safe ta dinga cewa a kira mata shi ta nemi yafiya, kasan in mutum na jin jiki babu abinda bazai zo ransa ba...." Abba ya dakatar da ita yace "Can u hear ur self speaking? For what reason za ku yanke hukunci ba tare da sanina ba, shi bashi da hankali ne Maheer din da zai kirasa? ko ya manta rashin mutunci da tijaran da suka yi mana a police station ne?" Ammi tace "Aa yallabai ku ka yi ma juna dai, kar ka manta mu fa musulmai ne, meye amfanin keeping grudges, ai ba haka addininmu ya koyar da mu ba, beside don ya zo dubata naga ba laifi bane sannan tare ma da mahaifiyarsa suka zo wallahi har ta ba Mimi 50k, to meye laifinsu? Kar fa ka manta ku kuka fara saka yan sanda suyi arresting yaron, to tunda har suka iya mance hakan su zo har Abuja dubiya daga kano don me mu ma baza mu manta ba?" Cikin fada Abba yace "Ohh haka kike gani ko? To wallahi idan wani abu ya kara billowa ke zan yi blaming, shi kuma Maheer banda bashi da tunani sam ko ita tace a kira mata yaron sai ya kira, inda Usman ya fi sa kenan don nasan da shi ne bazai kirasa ba wallahi, ana ƙoƙarin yarinya ta mance sa completely a rayuwarta shine ku ke kara gayyato mata shi, iyayen yaron nan su ne root din duk abinda ke faruwa da ita a yanzu" Ammi tace "To dai wannan MDn dake tsaye kanta ba dare ba rana yayan Musharraf din ne, uwarsu daya ubansu daya, sai mu yi yaya kenan?" Kallonta Abba ya tsaya yi baya ko kiftawa, bayan few seconds yace "Yayan Musharraf kuma? How?" Ammi tace "Mu ma duk haka muka yi mamaki kamar yanda ka yi, yayansa ne uwarsu daya ubansu daya" Shiru Abba yayi alamar he is completely speechless, Ammi tace "Atoh, kuma kai kanka ka fadi kirkinsa, dubi fa duk da matsayinsa na MD yanda yake mana a asibitin nan, yanzu ma bai dade da fita ba ma ka shigo, wai CEO dinsu na son magana da kai, kilan maganar Bill dinsu ne...." Abba ya sauke ajiyar zuciya bai sake cewa komai ba, Ammi ta juya ta koma cikin ward din, Office din Dr Khalil Abba ya tafi, Dr Khalil dake shirin zai tafi gida don ba shi
Chapter 262 · 0% Book details