Sashe 281
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
inda Aaria take, bude kofar dakin tayi ta shiga, Mayraah dai na makale jikin Ammi ta ma ki kallon kalan dakin, Nurse din dake zaune tare da Aaria tana nuna mata hotunan flowers masu kyau a Tablet din hannunta ta mike tsaye daga gefen gadon ganin su, Ceo tayi murmushin karfin hali tace "You can leave Farida" Nurse din tace "Alright Ma" Daga haka ta fita daga dakin, Aaria dai sai bin dukkansu take da kallo kamar bata saba ganin mutane da ɗan yawa ba, Ceo ta karasa ta zauna kusa da ita ta kamo hannunta tace "Do not be afraid my love, you know what i bring to you today?" Aaria ta girgiza mata kai, Mayraah dai har sannan taki kallon matar dake dakin sai makalewa jikin Ammi take, Cikin sanyin murya Ceo tace "I brought to you ur baby gal, kin tuna dama na taɓa ce maki na kai maki ita ajiya ne?" Aaria dai sai kallonta take, Ceo na kokarin danne kukan da ke taho mata tace "To yau naje na amso maki ita, ur 22 year old baby girl that u named after you.... remembered you try telling me that her birthday is in few weeks time? You remembered? To yau naje na amso ta tare da bayin Allahn da suka rike maki ita har ta girma" Aaria dai bata ce komai ba kamar tana kokarin processing maganganun yayar tata, Ceo ta mike ta juya tana kallon su Ammi babu ko kiftawa, karasawa tayi kusa da Ammi tana tafiya a hankali tana share idonta kafin tace komai Ammi ta janye Mayraah daga jikinta a hankali, cikin sanyin murya tana kallonta tace "Go to her daughter...." Mayraah ta gyada ma Ammi kai, trying hard not to cry, sai kuma ta kalli Ceo wasu sabbin hawayen da take ta avoiding na taruwa idonta, Ceo ta sauke idonta ta kama hannunta ta nufi kusa da gadon da ita, sai da suka isa gadon Mayraah ta iya kallon matar dake zaune tana kallonta ko kiftawa babu, Ceo tace "Aaria this is ur baby gal, this is ur Maryam" Zaunawa Mayraah tayi kusa da ita tana kallonta, bata san sanda ta fashe da kuka ba a hankali ta daura forehead dinta saman shoulders dinta hawaye na sauka idonta, Aaria ta dinga kallon ceo dake hawayen ita ma, gently Aaria ta dago kan Mayraah tana kallonta, rungumeta Mayraah tayi sai a sannan ita ma ta rungumeta gam tana kallon yayarta, as if counting her words tace "Maryam dita ce?" Ceo ta gyada mata kai tana murmushin karfin hali tace "Maryam din ki ce" Kuka ta fashe da tana kara rungume Mayraah jikinta, Ammi ta sunkuyar da kanta tana share hawayen dake sauka idonta ta juya ta fita daga dakin Abba ya bi ta da kallo, bin bayanta Usman yayi, Maheer dai ya jingina jikin bangon dakin, cikin kuka Aaria dake kallon yayarta tace "Don Allah kar ki sake rabani da ita Aunty, na ce maki ina sonta a haka, wallahi ina son ta" Ceo ta zauna kusa da su tana girgiza kai tace "Bazan sake rabaki da ita ba Aaria, amma su ma wanda suka rike maki ita ai iyayenta ne, kin ga su ma baza ki rabasu da ita ba" Aaria dai kuka kawai take tana rungume da Mayraah tana kallon yayar tata, juyawa Abba yayi ya fita daga dakin MD ya bi bayansa, Maheer kam kukan da yake jin Mayraah take ne ya sa ya kasa fita daga dakin, after a while dai kawai ya juya ya fita. Abba suna zaune parlor yana kokarin calming Ammi dake kuka duk da bai ma san takamaiman kukan abinda take, Usman da ya zauna gefenta dai kansa na kasa, Maheer na zaune tare da MD ko wannensu da tunanin dake ransa, after a While sai ga Ceo ta sauko downstairs tana rike da hannun kanwarta sai Mayraah dake tare da su, Mayraah na shigowa parlon ta nufi Ammi tana tafiya a hankali, ta zauna daya side dinta ta jinginar da kanta jikinta ta lumshe ido, Ammi ta ja ta jikinta, Ceo ta sa kanwarta ta zauna two sitter sannan ta zauna gefenta, gaba daya idanuwan Aaria da hankalinta na kan Mayraah, Ceo na kallon Aaria tace "Say hi to them, su ne iyayenta da suka rike maki ita" Aaria ta dinga bin su da kallo wasu hawayen na taruwa idonta, sai kuma ta kalli yayarta cikin rawan murya tace "Yanzun ma tafiya za su yi da ita? Amma kin ce min watarana za ki dawo min da ita gaba daya" Ceo ta kasa cewa komai, kuka sosai Aaria take tana bin su da kallo gaba daya a parlon, Ceo ta goge hawayen idonta cikin sanyin murya tace "Appreciate them Aaria, they look after ur Maryam for 22 years now, in ma sun tafi da ita ai tun da har suka kawo maki ita nasan zata dinga zuwa ganinki, kema zaki dinga zuwa ganinta ko da yaushe, kin san karatu take yanzu..." Aaria dai sai hawaye take tana kallon Mayraah da taki bude ido a jikin Ammi, Calmly Abba na kallon Ceo yace "Sai dai baki karasa mana labarin ba...." Ceo tayi murmushin karfin hali tace "Mary Ann's father ko?" Abba ya sauke ajiyar zuciya don abinda yake son ji kenan, gaba daya su Maheer kallonta suke, Ammi ma kallonta take, A hankali tace "I will prefer in dauke ku gaba daya mu je har gidansu a garin da yake, kuma har da Aaria za mu je..." Abba yace "Me yasa kika ce haka?" Ceo tace "Hakan zai fi Alhaji, zan yi booking flight for us gaba daya, gobe da safe za mu je har gidansu, i don't want to call his name" Abba ya sauke ajiyar zuciya thinking if hakan dai dai ne, Bayan few seconds yace "Amma kina tunanin hakan bazai haifar da wata matsalar ba? Do u think it's necessary sai mun je har gidansu" Girgiza kai tayi tace "Not at all, ai har bibiyata yake a Uk, he wants me to connect him to Aaria ban kuma san dalilinsa ba, sai da na kira masa police wani lokaci suka ja masa boundary da ni sannan ya hakura ya daina bi na, don can kawai muke haduwa, tun bayan Incident din bamu kara haduwa da shi ko family dinsa a nan Nigeria ba" Abba yace "To shikenan, Allah ya kai mu goben" Aaria dai sai kallon Mayraah take bata ko kiftawa, Ceo ta kamo hannunta a hankali tace "Za su tafi da Maryam don za ta je makaranta yau, amma na maki alkawari zaki kara ganinta gobe" Aaria ta fashe da kuka a hankali tace "But that wasn't what u promise Aunty" Ceo na shafa girarta murya can kasa tace "I know my love, for now allow her to go to school, za ku kara haduwa gobe" Har suka Isa gida babu wanda ya iya cewa komai a motar, Mayraah dai na rungume jikin Ammi, bayan Abba yayi parking Ammi ta bude motar ta sauka tare da Mayraah suka nufi cikin gida, Daga Usman har Maheer dai na cikin motar basu sauka ba kowa da tunanin dake yawo a zuciyarsa, Calmly Abba yace "Ina son duk abinda muka ji yau ya zamana sirri a tsakaninmu duka, duk da nasan halin ku, nasan abinda za ku aikata da wanda baza ku aikata ba, da Umar na nan nasan shi ma bazai taɓa fitar da maganar nan ba har a tashi duniya, amma duk da haka tunda baya nan ko shi bana so ya ji, ita ma mahaifiyar ku zan mata magana idan mun shiga ciki"