Sashe 175
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*MUNA MARABA DA KU, MUNA GARIN SOKOTO MUNA AIKE KOWANI GARI KOWACCE QASA CIKIN AMINCI* Mama Ladi dake zaune Parlon Ammi ta maida cup din shayin gabanta gefe da sauran bread din da ya rage tana kallon Hajja da ta kasa daina kuka kamar ranta zai fita, ta marairaice tace "Yaya ki sa ma ranki salama don girman Allah, wallahi kukan nan naki ya sa na kasa nutsuwa in ci abinci in koshi duk hankalina ya rabu, tunda Mamuda ya ce zai yi duk iya bakin kokarinsa don ganin an sakota ai kema kinsan zai yi hakan, kwanaki da suka tafi dake ba waya kawai yayi aka sako ki ba ko kin manta ne...." A fusace Hajja tace "Ladi ki shiga hankalinki ki fita harkata kar ki sake cewa za ki min wata magana, ai da er ki ko jikarki aka shigo har gida aka dauke baza ki samu damar hada katon kopin shayi da bredi ki sa a gaba kina ci ba, rayuwa ce fa Ladi, kuma kowa yayi da kyau zai ga da kyau" Mama Ladi ta saki baki tana kallon Hajja da mamaki, can tace "Ka ji yaya da wata magana dai, sai in ki cin abinci ina jin yunwa saboda yan sanda sun tafi da Badiyyah?? ayi magana fa ta gaskiya domin Allah? Shi ciki ina ruwansa da abinda ke faruwa shi dai ba kawai a fita hakkinsa a sallamesa ba, ita kanta Badiyyar yan sandan baza su bar ta haka ba sai sun bata abinci a celf balle ni da nake gida, kaji fa yaya da wata magana jama'a, shi ciki meye nasa a wannan lamari da za a tauyesa?" Ammi dai dake Parlon zaune sai kallonsu kawai take bata ce komai ba, a fusace Hajja tace "Ga ki ga abinci Ladi... Kiyi ta ci ba komai rayuwa ce" Mama Ladi ta mike ta dauke shayinta da sauran bredi ta nufi dakin Ammi tana cewa "Ji min dai fadan rashin gaskiya kiri kiri wai kar in ba cikina haƙkinsa don an tafi da Badiyyah, a ina aka taɓa haka, ba sai mutum ya ci ya koshi zai samu karfin jajanta lamarin ba, ni dai ba ruwana" Daki ta shige don har Hajja ta bata mata rai, murya can kasa tace "Ina ruwana da wata Badiyyah ma dai tukun, ban da dai neman magana irin na Hajja, Mera ma da bamu san inda take ba bai sa mun hana cikinmu abinci ba balle wata Badiyyah da muka san inda aka kai ta" Ammi na kallon Hajja cikin sanyin murya tace "Kiyi hakuri Hajja, tun da yace zai yi duk yanda zai yi in sha Allah a daren nan za a gama komai ta dawo gida, ki kwantar da hankalinki don Allah" Hajja na kuka tace "Toh Allah ya sa Ammi, Allah ya dubi maraicin yarinyar" Abba na zaune parlonsa Maheer ya shigo ta dalilin kiransa da Abban yayi, ya zauna kan kujera Abba na kallonsa yace "Wayar wani babban mutum fa yarinyar nan taje ta dauka babu batun bail yanzu haka, anya kuwa yarinyar nan kanta daya bata da wani mental problem?" Maheer yayi shiru yana kallon Abba yana jinjina abinda Badiyyah tayi a ransa, Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Gaskiya an ɓata rayuwar yarinyar nan kawai, abun nata sai gaba yake, ya kai har da dauke dauke yanzu take, ko kwana goma ba ayi ba taje gidan matarka tayi mata sata wanda ya kai su ga fada har ta fasa mata kai, yanzu kuma wayar mutane taje ta dauko me tsada aka yi tracking, wannan wace irin rayuwa ce?" a ran Maheer tunani ya shiga yi don ma Abba bai san duk adadin gurmin da ta hada a yan watannin nan ba, iya wanda kawai ake gaya masa ya sani, wanda da zai san har da sa hannunta wajen barin Mayraah gida da ma fasa auren Mayraah da ko bin ta kan case din nan bazai yi ba, dama shi tun da yaji an zo an tafi da ita ko bin ta kan issue din bai yi ba don abinda ya damesa ma ya ishesa, duk inda ma za a kai ta a kaita for all he cares ba kuma abinda zai tofa a lamarin, Abba ya kara sauke ajiyar zuciya yace "Sai dai zuwa gobe da safe kuma mu ga abinda hali zai yi, amma wannan ba karamin case bane gaskiya, don sun ce sai me wayan ya zo yana Abuja, to wa yasan sanda zai zo" Maheer yace "Allah ya kyauta" Abba yace "Ameen" Wayarsa dake ring ya dauka ya ga Hajiya Amina ke kiransa, Maheer ya mike ya fita daga Parlon, this past days kawai karfin hali yake yi, rashin Mayraah ba karamin taɓa sa yake ba, it's weighing him down sosai ba kadan ba, dare daddaya ne baya mafarkinta idan ya kwanta, downstairs ya dawo ya zauna ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido missing his lil sis, he misses her so badly, ya fi minti sha biyar zaune parlon ya ji muryar Mama Ladi ya bude ido yana kallonta, Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Ya ake ciki, inji dai Mamuda bai samesu a wayar ba su yan sandan" Maheer ya gyara zama a hankali yace "Wayar wani babban mutum ta dauke, ba ma batun bail yanzu maganar da ake" Mama Ladi ta gwalo ido tace "Wayar babban mutum? Eh lallai Badiyyah ta shahara sauran kawai ta fara yawo da makamai, nan ko kakar tun dazu ta ishi kunnemu da kuka wai da kyar ba sharri aka laka ma Marainiyar ba ni ko a raina ina ta tunanin anya Hajja ba bakinsu daya da Badiyyah ba kuwa? Da kyar fa in ba ita take kai ma kayan satan ta ajiye mata ba, sannan don girman Allah kai dai ka ja bakinka kayi shiru kar ka wani ce ma kowa ance babu beli wllh hanamu bacci tsohuwar nan zata yi daren yau don gaskiya yanzu haka ma bacci nake ji kada a shiga hakkina akan abinda bai shafeni ba, yanzu haka ina komawa sama shimfida zan yi in kwanta ince mata Mamudan bai dawo daga caji opis din ba" Daga haka tayi wucewarta kitchen zata kai cup din shayi.... Still wajen karfe sha daya Maheer na parlor Ammi ta sauko downstairs zata shiga kitchen ta hado ma Abba shayi, Ammi na kallonsa a hankali tace "Ita waccen dake asibitin an sallameta ne da na ganka a nan" Maheer ya girgiza kai yace "Sai gobe za a sallameta yan uwanta na asibitin, amma Ammi na so kawai taje gidansu daga asibitin don ina bukatar space, but Abba ya hana hakan ni kuma gaskiya i can't stand the sight of her a yanzu" Ammi dai tayi shiru bata ce komai ba, can ta wuce kitchen kawai. Kamar kullum yau ma karfe bakwai na safe Mayraah ta fito daga daki bayan tayi shirin tafiya aiki, kitchen ta tafi ta dafo ma inna ruwan zafi don for 5 days now ita ke kai mata ruwan zafi da breakfast kafin ta fita aiki, Mayraah na shiga dakin ta ajiye mata ta gaisheta, Inna da bakinta ya bude ras tace "Lafiya lau, kin ga yau fes na tashi bana jin ciwo a ko ina alamar guban ya sakeni" Mayraah tayi murmushi tace "Haka ake so dama inna Allah ya kara maki lafiya" Inna tace "Ameen, ai da so suka yi ace na mutu su hade har gadona, ni da nasan komai" Mayraah dai murmushi kawai take tana hada mata shayin, Inna tace "Allah maki albarka ke dai, naji wai aiki kema kike a asibitin su Halilu ko?" Mayraah tace "Eh" Inna tace "Toh Allah ya baki sa'a, kuma Kinga yaran gidan nan ki bar sake masu fuska kar su raina ki yanda suka raina ni basu da mutunci kwata kwata ya yan jaraba ne ga uwar bata kwabarsu" Mayraah dai sai murmushi take tace "Bari inje kar inyi latti Inna" Inna tace "Toh maza ki tafi Allah ya tsare" Mikewa tayi ta fita, bata tsaya tayi wani breakfast din kirki ba don ka'idar asibitin karfe takwas ne, sallama tayi ma Ummi ta fita gidan, kwana biyar yau basu hadu da Dr Khalil ba sun je wani workshop Lagos, Ta fito daga wani ward downstairs wajen karfe sha daya Dr Balogun ya shigo Reception, tare da shi aka tafi workshop din, nurses dake reception suka hau gaishesa suna masa sannu da zuwa yace "The MD is around, so u have to compose ur selves...." Daga haka ya wuce sama, Smartly dressed in black suit with white shirt ya shigo Reception din hannunsa rike da laptop dinsa, Mayraah ta bi sa da ido, gaba daya nurses din suka dinga gaishesa da ladabi kamar sun ga wani prominent person, yayi wucewarsa sama bayan ya amsa a takaice without looking at any of them, Dr Khalil dai na biye da shi a baya holding on to his laptop too ya daga ma nurses din hannu, Hafsat ta kalli Mayraah dake kokarin ajiye file din hannunta ta dawo ta zauna tayi kasa da murya tace "Wai shi ne me asibitin?" Hafsat ta buda ido sosai tace "He is the managing director" Mayraah bata sake cewa komai ba, bayan few seconds ta sake kallon Hafsat tace "But he is a foreigner?" Hafsat tace "Wallahi ban dai sani ba, amma ya cika jaraba mutumin, and he is a no nonsense, kowa shakkarsa yake" Da sauri Mayraah ta mike bayan ta tuna akwai wata patient da Dr Hamid yayi assigning dinta ta sa ma ido, ward din ta nufa to check on the patient, bayan azahar Mayraah ta tafi office din Dr Khalil zata kai masa wani file, gaishesa tayi ya amsa yace "Ya kwana biyu, ya aiki?" Tace "Alhamdulillah, how was the trip?" Yace "So stressful, nan da wata daya za mu koma in sha Allah" Mayraah tace "To Allah ya kai mu" Yace "Ameen, just that you have to be very careful cause or Director will be around har zuwa next workshop kafin ya koma, don haka ki zama diligence kan aikinki kar ki bari encounter mara dadi ya hada ku it wont be funny, though bana wani jin ki tunda har Balogun yayi commending dinki" Mayraah ta zauna