← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 303 OF 313

Sashe 303

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

yi maza taje ta kirata a dakinta, Abba dai tun zuwanta sau biyu tayi waya da shi, Maheer bai kirata ba ita ma bata kirasa ba. Ranan laraba da yamma misalin karfe biyar Mayraah na hada kayanta a akwatinta da ta dawo da shi dakin uwarta gaba daya, duk jikinta a sanyaye ta ke hada kayan har ta gama ta kulle box din, Aaria dai na zaune gefen gado tana ta kallonta bata ko kiftawan kirki, bayan wani ɗan lokaci Mayraah ta daga kai tana kallonta, mikewa tayi tana tafiya a hankali ta isa kusa da ita ta zauna gefenta tayi mata side hug ta jinginar da kanta jikin shoulder dinta cikin sanyin murya tace "Momy kiyi hakuri, ai zan dawo in sha Allah, i will be back soon" Aaria da hawaye ya cika idonta ta sauke kai bata ce komai ba, Mayraah duk jikinta yayi sanyi bata san sanda ta rungumeta ba a hankali ita ma hawaye cike idonta, muryarta na rawa tace "I promise you i will be back soon, i have cook all ur favorite na sa maki a freezer, microwaving dinsa kawai Aunty Farida zata dinga maki kinji?" Aaria ta gyada mata kai kawai hawaye na zuba idonta bata iya ta ce komai ba, a haka Ceo ta shigo dakin ta samesu don Driver na jiran Mayraah tun dazu, juyawa tayi ta fita daga dakin kawai ita ma duk jikinta yayi sanyi, Mayraah tayi pecking din mom dinta a goshi ta kara rungumeta tightly tace "Sai na dawo in sha Allah" Daga haka ta mike tana goge idonta ta tafi ta dau akwatin ta, ta juya tana murmushin karfin hali tace "Momy baza ki rakani bakin mota ba?" Girgiza mata kai kawai Aaria tayi, Mayraah ta ja box din ta nufi kofa, bata yarda ta juyo ba saboda hawayen dake sauka idonta har ta fita daga dakin ta jawo kofar a hankali, a parlor ta tadda Ceo a zaune, Ceo na kallonta a hankali tace "Kin ce mata zaki dawo?" Mayraah ta gyada mata kai, Ceo tace "Zan kira ki da layinta sai ki dinga kiranta frequently kin ji?" Cikin sanyin murya Mayraah tace "Toh...." Mai aikin Ceo ta kai uban shopping din da Ceo ta sa aka yi ma Mayraah da akwatinta har bakin tsadadden motar da zai yi dropping dinta a gida, Ceo na rike da hannun Mayraah suka fita har zuwa parking space din, har cikin ranta take jin kewar mahaifiyarta tun bata bar gidan ba, yanzu shikenan ita kadai zata yi ta zama a daki don da alama ko zaman parlor bata so, Mayraah ce ke jan ta su fito parlor, Ceo tayi pecking hannunta tace "Take care of ur self daughter" Mayraah ta gyada mata kai tana murmushin karfin hali, Ceo tace "Ki gaida min parent din ki da brothers din ki" Mayraah tace "Toh za su ji" Har Mayraah zata shiga mota sai kuma ta tsaya tana kallonta cikin sanyin murya tace "Ma'am ai za ki zo gobe, pls ki zo tare da ita" Ceo ta ɗan yi murmushi tace "Ohk i will my dear" Daga haka Mayraah ta shiga bayan motar ta ɗan ji ta samu relieve don gobe alhamis Ceo zata zo gidan nasu saboda Uncles din su Musharraf that will be around, Ceo ta kulle motar tana daga mata hannu har suka bar babban compound din. Mayraah na isa dai dai gate din gida taga Usman tsaye bakin gate din shi da Security alamar magana yake masa amma tun da yaga motar ya maida attention dinsa kan motar waiting to see who is inside, Tuni Drivern motar ya sauka ya bude mata motar kafin ta ankare, ta ɗan buda ido cause bata yi expecting haka ba, can dai ta sauko daga cikin motar, er dariya Usman yayi bayan ya ganta, ita kam murmushi kawai tayi ta nufesa tana tafiya a hankali, yace "Ni ai na zata er wani governor ce ta shigo estate din namu za ayi dropping dinta gidan kawarta or so, ashe dai Mimin mu ce" Mayraah bata san sanda tayi dariya ba tace "Kai yaya" Yace "Irin wannan mota haka Mimi" Ta marairaice tace "Yaya Allah bana so" Yana murmushi yace "Tohm an daina, welcome back home" Ta sauke idonta a hankali tace "Thank you, good evening" Usman yace "How are you?" Tace "Alhamdulillah" Security din gidan ne ya amshi kayanta gun driver din da ya kawo ta, Usman na kallonta yace "Ko dai sai an bude maki gate din gidan ne?" Bai jira me zata ce ba ya bude mata gate yanda drivernta ya bude mata mota, Dariya tayi tace "Don Allah yaya ka bari pls" Yace "Shiga dai an bude maki naga kamar haka kike jira" Shiga gidan tayi tana murmushi tace "Thank you" Yace "Ya kika baro yan can gidan?" Tace "Suna gaisheku" Yace "Muna amsawa" Tafiya ta fara yi zuwa main entrance din gidan ta bar masu kayan nata gaba daya, tana isa kofar shiga Parlon ta bude a hankali sannan ta shiga da sallama, Maheer ne kwance 3 seater a parlon yana kallon kwallo, yana jin sallamarta ya kulle ido as if yana bacci, ta gefen ido take kallonsa da ta shigo parlon can ta dauke idonta har ta fara tafi hanyar staircase sai kuma ta juya ta kallesa sake rufe idonsa yayi ruff kamar me bacci, juyawa tayi bayan komai yayi escaping mind dinta, lkci daya ta koma cikin parlon ta zagaya ta inda kansa yake ta sakalo kanta tana kallonsa a hankali tace "Stop pretending Yaya" Still dai bai bude ido ba, dukawa tayi ta kai fuskarta dai dai nasa har yana jiyo saukan numfashinta tace "Allah nasan ba bacci kake ba da yamman nan" A hankali ya bude ido suka yi ido hudu da shi, a gigice suka ji muryar Mama Ladi da ta fito daga kitchen da kwanonta cike da shinkafa da miya tace "Auzubillahi ni Ladi, sumbatar sa kike Mera?" Mayraah ta dago kanta da sauri ta tashi tsaye, shi kuma ya mike zaune, Mama Ladi dai ta saki baki tana kallonsu da idanuwanta kamar za su fito alamar ta gigice, Can tace "Usuman wallahi tallahi abinda na gani kenan, kai in na masu sharri kar Allah ya bani cin gobe da na jibi, ashe kai ma dai kana tsaye jikin kofa kana kallon ikon Allah, ace gubar lafiya Mera ta ci?? Sumbatarsa fa take, Aa ba ruwana wallahi" Mayraah ta juya da sauri ta kalli bakin kofa taga Usman dake dariya har ya juya ya fita daga parlon ya bar mata kayanta a bakin kofar, Mayraah ta maida dubanta kan Mama Ladi da sauri ta marairaice tace "Sumbata kuma Mama? Wallahi kawai...." Mama Ladi taki tsayawa balle ta saurareta irin taga abinda ya fi karfinta din nan tayi hanyar stairs kawai da sauri, Mayraah ta kalli Maheer hankali a tashe kamar zata yi kuka tace "Yaya shine zaka yi shiru?" Ya gyara zama yace "Nima ba farkawa nayi naga kamar kina hakan ba"
Chapter 303 · 0% Book details