← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 278 OF 313

Sashe 278

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

take, amma haka wani lokacin classmate din nan tawa zata debo mana kayan abincin gidansu a boye ta kawo mana mu girka" Ceo tayi shiru staring at the big plasma in the parlor, sai kuma tayi murmushin takaici tace "The mistake we made ni da kanwata was that, bamu yi wayon ce ma Mom dinmu ta kai mu gun relatives dinta a South ba, nasan kilan su da baza su guje mu ba, bayan rasuwan Abbanmu da wata sha daya Mahaifiyar mu ma ta rasu, leaving us with nobody to look unto as family members or relatives, leaving us in this harsh world all alone, just i and my little sister" kuka take sosai tana kallon Abba dake kallonta da ma duk occupant din parlon, ita dai Mayraah na jikin Ammi ta rufe idanuwanta zuciyarta na bugawa, Ceo tayi kukanta me isarta, cike da karfin hali tace "Life took another horrible dimension for us, we have nobody to look unto, we were too young and naive, bamu da me ba mu abinci sai wannan classmate din tawa duk da iyayenta ba wai wasu masu kudi bane kawai rufin asiri gare su, gashi ko bin ta kanmu dangin Abbanmu basu yi ba duk da ganin mahaifiyarmu ta mutu, ga kudin hayanmu ya kare, amma mai gidan duba da halin da muke ciki na rashin gata da rashin iyaye sai ya maida mu wani gidan hayansa na masu karamin karfi wato daki daya, as i am talking to you now jikokinsa biyu na aiki hospital din, Dr Hamid here in Abuja, sai Dr Misbahu in my lagos branch, babu batun boko ko islamiyya a lokacin sai dai mu jira Classmate dita ta samo mana ɗan abinda za mu dafa daga gidansu kuma duk a boye take debo abincin ta kawo mana, kwatsam sai yayan babanta ya kai ta boarding da cousin sister dinta for her Ss school, wannan dalili yasa na fara jan kanwata zuwa kasuwa inyi dako don mu samu abinda za mu ci, da daddare mu dawo gida mu kwanta, dama tun bayan rasuwan Abbanmu muka bar zuwa islamiyya sai mom dinmu ta tafi da mu coci, to cocin ma tunda ta rasu muka daina zuwa don unguwan da mai gidan ya maida mu da nisa sosai daga cocin bamu da kudin motar zuwa, but i do read the bible together with my little sis sannan in koya mata karatun boko. Bayan wani lokaci sai wani mutumi a kasuwa ya bani aikin tsare masa babban shagonsa don kullum yana ganina cikin kasuwa da kanwata ina dako, duk ranan duniya yake sallamata bayan da na basa labarin bamu da iyaye, to da wnn kudin na hada na saka kanwata a makaranta mara tsada, ni kuma na ci gaba da zuwa kasuwa, a kwana a tashi har Aaria ta gama primary school, ita kuma classmate din nan tawa tayi candy ta dawo gida ta tafi tsohon gidanmu aka mata kwatancen inda muka koma, with her assistant na biya ma Aaria secondary school me kyau tana zuwa, ni kuma ta ban shawara tunda ina da kokari don kafin in zama drop out ni ke leading a ajinmu tace min in siya science textbooks na senior secondary school in dinga karatu kawai sanda za a fara registration na waec nima inyi registration in zana waec, hakan nayi amma fa sai da nayi shekara ina karatu a gida kafin in zana waec din wanda ita classmate din tawa ce ta biya min, Ita kuma ta samu admission a jami'a, duk kudin da nake samu a kasuwa tarawa kawai nake don ina son inyi sponsoring kanwata ko da ace ni ban samu wani karatu me zurfi ba ita ina son tayi karatu sosai don tana da kokari ita ma, tana gama junior secondary school nayi deciding ta tafi boarding school saboda yanda naga she is growing into a beautiful girl kuma maza sun fara bibiyanta at her very young age, beside Aaria is too naive sannan bata da wayo gata matsoraciya, she is just intelligent but not smart or brave, still a haka dai sai da wannan classmate din tawa ta tallafa mana don kudaden wajena basu isa na kai ta boarding din ba, bayan Aaria ta tafi boarding school iyayen classmate dita suka yi relocating back to kano, sunyi kokarin su nema mata transfer a University din da take amma bai yiwu ba, to hakan yasa sai dai ta je kano hutu, a sannan kuma bawan Allahn da nake jire ma shago ya koma Gombe da family dinsa, da ɗan kudin wajena nayi jari ina siyar da pure water a kasuwa ko gaya ma wannan classmate din tawa banyi ba don karatunta na bukatar nutsuwa sosai, she was studying medicine sai a jima bata fito daga cikin makaranta ba ma, duk don in dinga providing needs din kanwata dake boarding school nake sana'ar da nake" Shiru Ceo tayi tana murmushin takaici, duk occupant din parlon kallonta suke, i trust my little sis, a ɗan tarbiyyar da nayi mata tun bayan rasuwan iyayenmu nasan abinda zata aikata da wanda bazata aikata ba, ko a sanda nake jire shago a kasuwa da sun tashi boko kasuwa take zuwa ta sameni immediately kuma sai karfe shidda na yamma muke komawa gida tare, har dai ta tafi boarding school, bayan sun zana jarabawarsu na waec, ina kwance ni kuma bani da lafiya tun bayan da mota ta bugeni wajen siyar da pure water sai ban je na taho da ita ba tunda bata da kudin motar dawowa gashi waya bai yi yawa ba a sannan, ko yayi yawa ma we can't afford it, duk classmates dinta suka tafi gida sai ya kasance ba su da yawa da suka rage a makarantar don school was on vacation su kuma suna waec, ana haka sai wata classmate dinta taga ita ma zata tafi ta bar ta, hakan yasa ta samu Aaria tace Babanta zai zo daukanta su je sai a ajiyeta don su ma Adamawa za su, bayan an zo daukarta sai ta sanar ma Aaria ba babanta bane ɗan uwanta ne, a haka dai ya daukesu su biyu....."
Chapter 278 · 0% Book details