← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 176 OF 313

Sashe 176

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

bata dai ce komai ba, yace "Ya su Ummi?" Tace "Suna lafiya lau" Yace "Ummi ta ban labari kun kulla kawance da Inna yanzu" Dariya Mayraah tayi, yace "To ki dai dinga bin a hankali kar ya kwabe maku" Murmushi kawai Mayraah tayi tana gyada masa kai, yace "Kin je weekend gida kuwa?" Tace "Na je" wayar kan desk dinsa ne ya fara ring, ya kalleta yace "MD na kirana, make sure kar ki tafi gida ki jirani i will drop you don nima zan je gidan" Tace "Toh" Mikewa yayi ita ma ta tashi suka fita office din tare, shi ya tafi last flour zuwa office din MD din, ita kuma ta sauka downstairs ta dau allurai a tray zuwa wani ward zata yi ma wata yarinya da aka yi admitting da safe, tana shiga ward din ta tarar Maman yarinyar na bata abincin da aka kawo masu na asibitin, sai da ta zauna ta jira ta gama bata abinci sannan ta mike ta fara hada alluran, bude kofar ward din aka yi Mayraah ta juya, sai kuma ta koma gefe tana kallonsu, MD din ne da Dr Khalil dake biye da shi a baya, Matar ta gaishesu MD din na kallonta yace "Hello Ma, is there any improvement?" Da turanci Matar tace har yanzu jikin yarinyar na zafi, sai zazzabin ya sauka sai ya sake dawowa, sannan yarinyar na zabura, MD ya kalli Mayraah dake tsaye gefe yace "Diagnostic procedure?" Haka kawai taji gabanta ya fadi ta dau file din yarinyar da ta shigo da shi ta fara budewa da sauri, lkci daya duk sai ta daburce, Dr Khalil ya amsa file din a hannunta yana dubawa ya sanar masa diagnosis din, Gyara tsayuwa yayi yace "Ita bazata iya dubawa ba sai kai" Dr Khalil yace "We have 19 more wards ahead Doctor" MD din yace "Therapeutic procedure?" Nan ma Dr khalil ya karanto masa within few seconds, MD din yace "Any medical History?" khalil ya sanar masa yana duban file din still, karasawa MD din yayi feeling the girls temperature ya duba ta da stethoscope din wuyansa, bayan few seconds ya kalli Mayraah a takaice yace "Give her the injections" Daukan alluran tayi ta nufi kusa da yarinyar zata yi mata amma sai abun yayi mata kamar bata taɓa yi ma kowa allura ba kamar ranan zata fara ga kuma kukan da yarinyar take ya gigitata, MD din ya kalli Dr Khalil a bit pissed off yace "Why is she so sluggish? Wannan ta san aikinta kuwa?" Dr Khalil zai amshi alluran ya dakatar da shi furiously yace "What for?" Mayraah ta masa wani kallon gefen ido bayan ta ɗan daure fuska, nan dai ta tsaida hankalinta waje daya tayi ma yarinyar alluran, ficewa yayi daga ward din Dr Khalil ya bi bayansa. Karfe biyar wata senior nurse ta sanar ma nurses dake reception da za su yi ma yan evening handing over cewar su jira akwai meeting, yan evening na zuwa to su yan morning za su shiga meeting din da director a meeting room dake cikin asibitin, the next day kuma kafin yan evening su tafi za su yi nasu meeting din. Mayraah ta fito daga wani ward Dr Khalil ya nufota yana kallonta yace "Kiyi tafiyarki gida kawai ba sai kin yi attending meeting din ba Ilham, beside he doesn't even have ur data for now sai na basa, after the meeting i will be coming back home too" Mayraah taji hankalinta ya kwanta don dama tun da Matron ta sanar masu da batun meeting ta rasa sukuni, ita in son samu ne ma bata son ko wani irin encounter ya hadata da wnn MD din har sanda zai koma, kawai taji kwata kwata bai mata ba she don't like him, he is rude and arrogant sannan ta ga alamar ya iya disgi, Ta langwabar da kai tana kallon Dr Khalil tace "Toh shikenan, sai ka dawo" Yace "Hope kina da cash dai?" Tace "Ehh ina da, thank you" Ko minti goma bata kara a asibitin ba ta dau jakarta ta tafi bayan taje tayi ma Nurse Hafsat sallama a injection room, tana fita nurses din reception suka fara kus kus a tsakaninsu ganin ta tafi bayan ance akwai all staff meeting, dama tun da aka lura da yanda wasu daga likitocin asibitin ke yaba mata shkkn aka fara mata hassada kiri kiri don wasu ko magana basa mata a asibitin ita kuwa ko sanin suna yi ma bata yi ba tunda ba wani surutu take ba ko hira, tsakaninta da su gaisuwa shi ma wasun su sai suyi kamar basu ji ba, asibitin da ko kwana goma bata yi cikakke da fara zuwa ba, hatta yanda Dr Khalil ke kiranta office da kuma yanda Dr Balogun ke interacting da ita ya tsaya ma da yawansu a wuya, wata nurse fa'iza tana kallon colleague dinta murya can kasa tace "Wato ita shafaffiya da mai bazata tsaya meeting din ba kin ga ta dau jakarta ta tafi, tabdi bata san MD bane, ta zata irinsu Dr Khalil da Dr Balogun ne ko Dr Hamid dake shining mata hakora, muna nan dake wallahi sai MD ya gane bata shiga meeting din ba, sai in dai basu hadu a asibitin ba wannan mayen, zan ga ko shi ma kwarkwasan zata dinga masa yanda take ma sauran likitocin, Allah Ubangiji ya sa ya disgata gaban kowa da kowa mu ga iskanci, ko su Dr Khalil din da Dr Balogun babu abinda za su iya yi in ba haka ba ya hada da su" Nurse Victoria tace "The thing tire me my sister, ke daga zuwanki sai wani feeling kanki kike kin zo kin samu mutane a waje ki dinga wani ciccin magani kina daga masu kai wai ke me kokari, who does that?" Nurse Bola dake jin su tace "Fatana kawai yana ganinta after all the meetings ya gane bata shiga ba, a nan zata ga ikon Allah" Suna hango Nurse Hafsat duk suka yi shiru. Mayraah na isa gida ta tadda Ummi zaune parlor tare da Zainab matar Khalil da kanwar Ummi warce ake ce ma Aunty Rabi'ah, tun zuwan ta gidan sai ranan taga Zainab ta zo, ta karaso ta zauna ta gaida Ummi da Aunty Rabi'ah sannan ta gaida Zainab din ma, kallo daya Zainab tayi mata ta kauda kai ta amsa, Mayraah ta mike ta shiga dakin da take, Sai da Ummi ta ji ta kulle kofa sannan ta kalli Zainab tace "Wannan wani irin amsawar walakanci ne Zainab?" Zainab tace "Walakanci kuma Ummi, ta gaisheni kuma ai na amsa" Aunty Rabi'ah tace "Wai Ummi har yanzu bata samu gidan bane, last week da na zo ce min kika yi gida take nema fa, wannan ko sabon gidan da aka gama ginawa take so ya ci ace ta samu yanzu dai" Ummi tace "Bata samu ba, kuma baza a samun ba ma" Aunty Rabi'ah ta kyabe baki tace "To Allah ya kyauta" Har bayan magrib Mayraah bata fito daga daki ba, cause impression din Zainab duk sai yayi weaken dinta gaba daya, Mimi ce ta shigo dakin tana kallon Mayraah tace "Aunty Ummi tace in kira ki" Mayraah tace "Toh" Mikewa tayi daga kan darduma ta fita zuwa parlor, Ummi kadai ce zaune parlon, Mayraah tace "Ga ni Ummi" Ummi tace "Naga baki debi abinci ba" Mayraah tace "Ina jiran ayi isha ne" Ummi tace "To ai lokacin ma ya gabato, Inna na tambayarki nace kin dawo kina hutawa ne a daki" Mayraah tayi murmushi dai dai nan aka yi sallama kofar parlon, Ummi ta daga kai tana kallonsa da mamaki tace "Aa... kai kuma daga ina haka? 5 weeks din kenan?" Juyawa Mayraah tayi gabanta ya fadi lokaci daya ta dauke kanta da sauri.
Chapter 176 · 0% Book details