Sashe 204
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Ina Mai farin cikin gabatar maku da garin Sabaya gangariya Mai dadin gaske Wanda zata cikomaku da da ramar ku jikin ku yayi gwanin sha'awa, ina uwar gida a Amarya zawarawa yanmata Kai jama'a wannan lafiyayyar sabayar ta maman Khadijah har maigidan ma da yaran gida duk zasu iya Shanta batada wata matsala dan neman Karin bayani zaku iya tuntubar mamann Khadijah Kai tsaye ta number waya ko WhatsApp* Mayraah na gama yin breakfast ta shiga yin wanka bandakin Ammi, Maheer kuma ya fita da tray din da suka yi breakfast din downstairs zuwa kitchen, ko da ta fito wanka ta tarar Ammi ta dauko mata kaya daga dakinta ta ajiye mata gefen gado, bayan ta shafa mai ta shirya ta fito parlor, har a sannan Badiyyah na parlon Ammi a kwance ita kadai, Mayraah na tafiya a hankali ta karasa kusa da ita ta durkusa tana kallonta tace "Ya jikin?" Kai kawai Badiyyah ta gyada mata, Mayraah tayi shiru tana kallonta hawaye na taruwa idonta, abubuwan da suka faru a baya ne da dalilin faruwansu kawai ke yawo mata a zuciya, da sauri ta goge idonta trying to shun away the thoughts off her mind, cikin sanyin murya tace "Kin yi breakfast ai ko?" Nan ma Badiyyah ta gyada mata kai tana kallonta, wani tausayinta Mayraah ta dinga ji har cikin ranta, she can't just imagine Badiyyah da ta sani ce wannan, a whole Badiyyah, Ammi ce ta shigo parlon, Mayraah ta juya tana kallonta, tana tsaye bakin kofar tace "Fito ki je wajen Abbanki Mimi, he is around" Mayraah ta mike tana goge wasu hawayen dake taruwa idonta ta nufi Ammi, a tare suka sauka downstairs, Mayraah na hada ido da Abba dake zaune kan kujera ya mike tsaye yana kallonta, sosai jikinta yayi sanyi ta sunkuyar da kanta and for the first time she felt guilty akan abinda ta aikata, for the first time ta ji bata kyauta abinda tayi ba, nan da nan hawaye ya cika idonta ta nufesa da sauri ta rungumesa sosai ta fashe da kuka tace "I am sorry Abba, don Allah kayi hakuri, i don't know what came over me, i was...." Kasa ci gaba tayi tana kuka sosai, Abba yayi patting din bayanta a hankali bai ce komai, tayi kukanta me isarta sannan ta durkusa nan gabansa cikin rawan murya tace "Don Allah ka yafe min Abba" Har a sannan ta kasa hada ido da shi, Abba ya zauna kan kujera a karo na farko yayi magana yace "It's okay Daughter.... I am glad you are back home hale and hearty, that was our prayer and hope, Alhamdulillah" Ganin yanda take kuka ya shafa kanta yace "Nace ya isa haka my dear" Ta gyada masa kai tana goge hawayen dake sauko mata, gefensa ya nuna mata ta dawo ta zauna ta daura kanta a jikinsa, sai a sannan ta lura da mutanen dake zaune parlon, Mama Ladi ce dake ta taɓe baki tana hararanta sai Hajiya Amina dake ta kallon Mayraah tana murmushi, matar looks so happy da dawowar Mayraah, Mayraah ta kalli Abba ya gyada mata kai yace "Go and greet her" Mikewa tayi ta ɗan kalli direction din dining da ta hango Usman a zaune shi ma yana kallonta, ta karasa har gaban Hajiya Amina ta durkusa gabanta ta gaisheta, Hajiya Amina ta dago ta sitting her down by her side ta jawota jikinta tana amsa gaisuwar ta da fara'a, Ammi dai na tsaye stairs taki karasowa cikin parlon all her attention na kan Mayraah, Mama Ladi da take ganin abinda ake bai shafeta ba ta mike tana kallon Ammi tace "Ke har yanzu fa shegiyar me aikinki bata kawo ma bakuwar nan abinci ba, ko kafura ce mai aikin da bata san ance baƙon ka annabinka ba" Ammi bata tanka Mama Ladi ba, don dauke kai ma tayi, Hajiya Amina na murmushi tana kallon Mama Ladi tace "Ayya Mama nace mun yi breakfast kafin mu fito" Mama Ladi tace "Aa ko farfesun ne bari inje in debo maki da burodi mu bamu gaji rowa ba a pamilyn mu" Daga haka ta wuce kitchen da sauri, Ammi ta juya ta wuce sama Abba ya bi ta da kallo, Mayraah na son tashi daga kusa da Hajiya Amina ta bi Ammi amma sai ta kasa, gaba daya she is not comfortable sitting down with her, mikewa Abba yayi ya wuce sama. Sai kusan karfe sha biyu Hajiya Amina da Abba suka bar gidan har sannan kuma Ammi bata sauko kasa ba, sai upstairs Hajiya Amina ta tafi tayi mata sallama a part dinta, Mama Ladi kuwa babu wanda zai ce ba wajenta Hajiya Amina ta zo ba don babu labarin karaye da bata ba Hajiya Amina ba, saboda ita ne ma har Hajiya Aminar ta iya kai wa karfe sha biyu a gidan, tunda ita kadai ce downstairs sai Usman dake aiki da laptop dinsa a dining area. Mayraah ta shiga dakin Ammi bayan tafiyar Hajiya Amina ganinta kwance har a sannan ta zauna gefenta tana kallonta tace "Ammi ko dai baki da lafiya ne?" Ammi ta sakar mata murmushi tace "Aa kawai hutawa nake Daughter" Mayraah tace "Toh ba abinda za a kawo maki?" Ammi tace "Aa... i am okay" Shiru Mayraah tayi, tun dazu take zaune dakin da Badiyyah take kwance bayan Ammi tace ma Badiyyar ta koma can za a gyara mata part dinta, ita dai ta rasa wani irin tausayin Badiyyah take har cikin ranta, sai Mama Ladi ce ta zo ta kirata taje suyi sallama da Hajiya Amina tana mata mitar meye hadinta da Badiyyar zata ne ta makale mata kowa na baya baya da ita salon ta shafa mata wani cutar, ita dai Mayraah bata ce mata komai ba, bayan tafiyar Hajiya Amina ne ta hauro sama ta shigo part din Ammi, mikewa Mayraah tayi after some minutes, Ammi na kallonta a hankali tace "Anjima idan na tashi ki zo in gyara maki gashin ki" Mayraah tace "Toh Ammi" Fita tayi daga dakin ta koma dakin da Badiyyah take, Badiyyah na kallonta da kyar tace "Baƙin sun tafi? Ina son in je parlor na gaji da nan din" Mayraah tace "Eh sun tafi" Ita kanta Badiyyah yau ta ɗan samu sukuni tunda ba ayi neglecting dinta as always ba, yau gashi har ruwan wanka sai da Mayraah ta tara mata ta samu tayi wanka, hatta Ammi bata bi ta kanta a gidan iyaka ta ajiye mata abinci in ta ga dama ta ci, wanka ma idan ta ga dama taje ta tara ruwa tayi, sai kuma Maheer da ta saka yake bata medication shi ma yana ajiye mata magani yake fita, Mama Ladi kuwa sai dai bata kyallara ido ta ganta ba, munanan kalamu sai wanda ta manta ne bata sakar mata, hakan kuma ke sa Badiyyar kuka sosai taji kamar ta mutu ta huta kawai, yau kuwa tun da Mayraah ta dawo take by her side even if she is not saying anything to her, Mayraah tace "Sun tafi, za ki iya saukowa, ba kowa a parlon" Da kyar ta lallaba suka koma downstairs ta kwanta nan tsakar carpet, sabuwar mai aikin gidan ce ta kira Mayraah da ladabi tace "Hajiya ta hanata saukowa ta kwanta nan saboda baƙi masu shigowa fa" a hankali Mayraah tace "Ba jimawa zata yi a nan ba" Suna cikin magana Haseenah ta leko Parlon don tabbatar da Mama Ladi bata ciki kafin ta shigo, tana ganin bata parlon ta shigo zata kitchen ta debi abincin rana, dama yanzu ko gas bata kunnawa sai an girka a nan ta faki idon mama Ladi ta shigo ta diba tunda ba wai kanta ya gama healing bane ita ma har yanzu jinya take, tana kyallara ido taga Badiyyah ta fara wakar habaici tana taunar cingam wai wata tayi cikin shege don ta ci ragon suna.... Can kuma ta hango Mayraah wani matsiyacin kallo ta mata ta shige kitchen bata fasa wakar da take ma Badiyyah ba, Mayraah dai ta bi ta da kallo, ita dai Badiyyah dama ko kallon direction dinta bata yi ba don duk haduwar da za su yi da Haseenah a gidan wakar da take mata kenan, to tana fama da kanta ina taga ta kulata. Washegari wajen karfe goma na safe Mayraah ta tashi daga baccin da take, har ta mance rabon da tayi bacci peacefully kuma me tsayi haka, wanka tayi ta shirya sannan ta gyara ma Ammi dakinta ta fito parlor, Maheer ta gani zaune parlon shi kadai, ta karasa kusa da shi ta zauna kasa tace "Yaya ina kwana?" Yana kallonta yace "How was ur night?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Kan ya daina ciwo?" Ta ɗan buda ido sannan ta cire dankwalin kanta don gashinta suka zubo kasa tace "Ya daina" Tun jiya da Ammi tayi mata kitson kalaba take complain din ciwon kai don ta dade bata yi kitso ba, hakan ma yasa ta kwanta da wuri jiya da daddare, yanzu kuma da ta tashi taji babu ciwon, yana kallon kitson nata yace "Yayi kyau" Murmushi tayi tace "Thank you, yaya result dinmu fa?" Sai bayan da tayi tambayar gabanta ya fadi sosai she can't imagine her spilling, ya ɗan yi shiru yana kallonta, nan da nan hawaye ya cika idonta, yanzu gaba daya hawaye baya mata wahala nan da nan take hawaye, cikin rawan murya tace "I had issues ko?" Yace "Nasan tsohon saurayinki ya gaya maki ai" Har sannan gabanta na faduwa tace "Wallahi yaya A'a, babu ta inda zai yi accessing dina ya gaya min" Yace "Ai na zata kin ga result din naki tuntuni" Ta girgiza masa kai tayi narai narai da ido, yace "To bari in nuna maki, but...." Hankali tashe tace "But what yaya??" Yace "Promise me u will be calm ko me zaki gani, kuma ki gode Allah" Wasu hawayen ne suka taru idonta, yace "Toh shikenan" Da sauri ta goge idonta tace "I will be calm plss" Yace "Good, dawo nan" Mikewa tayi ta koma gefensa da ya nuna mata ta zauna sai tsuru tsuru take da ido, ya shiga WhatsApp dinsa ya nemo chat dinsa da Hamidah da ta turo masa result din, Mayraah da duk jikinta ke bari don bata san me zata