Sashe 100
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
lalata zai yi ba meye zai wani dinga bibiyarta bayan an fasa aure, to ni dai ba ruwana" Ammi dake ta kallonsu, cikin sanyin murya tace "Mama Ladi amma da an bar ta, a hankali zata rabu da shi ba farat daya ba, mutumin kirki ne wallahi ba ruwansa...." Maheer ya dinga ma Ammi kallon mamaki, Mama Ladi tace "Kaji wata magana kuma ko? Wato muna nan muna babatu ashe ke kika daure mata kugun ta ci gaba da kula katon, kanin ubanta ne shi da bazata iya rabuwa da shi farat daya ba??" Ammi ta kalli Maheer tace "Plss take it easy on her, ka daina firgita min yarinya, ka taɓa ganin inda aka rabu farat daya? Allow her breathe plss" Tana fadin haka ta mike ta shiga dakin, Mama Ladi ta bi ta da kallo baki bude, Maheer dai na tsaye ya kasa cewa komai, can ya juya ya fita daga parlon. Karfe goma saura Usman ya shigo parlon Ammi Maheer na biye da shi, tun da Mayraah ta hada ido da su sau daya ta sunkuyar da kanta ta ci gaba da danna wayarta, Maheer dai na tsaye bakin kofar, Usman ya zauna yana kallon Ammi, calmly yace "But Ammi, kamar bai kamata kiyi supporting din...." Ammi ta dakatar da shi tace "Plss bana son wannan maganar, kowa yayi abinda zai fishshesa, bana son a sake tada min zancen nan" Mama Ladi ta matsar da farfesun gabanta kamar zata yi kuka tace "Yau naga jaraba ni Ladiyo, meyasa kike haka ne Ammi, mata kiyi ta goyon bayan karya kamar uwarki Hajja, wannan wani irin dabi'a ce ku ka gada wajenta, yanzu so kike a zuba ma yarinyar ido ta lalace ta zama er banza, Abu ya taru ya mata yawa ga rashin sanin asali gashi ta lalace? Ina ruwanta da shi wancan katon da ya fasa aurenta in dai za ayi maganar gaskiya jama'a, ai tunda har babu maganar aure tsakaninsu to kilan da wata manufa yake bibiyarta, amma saboda sonta ya rufe maki ido kin kasa fahimta, to ni dae wllh ba ruwana" Ammi dai ta hade rai taki cewa komai tana kallon TV, Mama Ladi ta kalli Usman da Maheer tace "Kyau ace daya daga cikin ku ya aure er banza in ga ta tsiya" Daga Maheer har Usman sai da suka yi still a inda suke cause they never saw that coming from Mama Ladi, Mayraah ma taji komai ya tsaya mata jin abinda Mama Ladi tace, ita kanta Ammi felt somehow da furucin Mama Ladi, Tuni Mama Ladi ta maida kanta kan kwanon farfesunta kamar ba ita ta fada ba, mikewa Usman yayi ya nufi kofa ya fita daga parlon, Mayraah ta ɗan daga kai suka hada ido da Maheer dake kallonta, da sauri ta kauda kanta, Mama Ladi dai sai cin farfesunta take, Bayan few seconds Maheer ya sake kallon Mayraah, a hankali yace "Dauko Hijab dinki mu tafi" a takaice Ammi tace "Sai da yamma" sosai Mayraah taji wani relieve, Maheer ya juya ya fita daga parlon ya kulle masu kofa.... Bayan la'asar Mayraah na kwance dakin Ammi suna waya da Dr Musharraf, duk yawanci hirar tasu akan fast approaching exams dinta ne, yana bata tips on how to prepare for the final exams, a hankali tace "But sir unlike before, yanzu i am finding it difficult to apprehend idan ina karatu, sae in dade a handout daya ban gane ba" Dr Musharraf ya kwantar da murya yace "That's because kin sa damuwa a zuciyarki Mayraah, pls ki cire komai a ranki and read like there is no tomorrow, this is ur future, it will be sad ace kin samu issue, you need not to worry about ur project for now i will handle that, kawai kiyi concentrating a karatunki, in sha Allah zan baki AOC a courses dina biyu, and i will try and get from other lecturers too if that will be possible, i will write it down idan mun hadu school gobe sai kiyi sharing with ur cousin Badiyyah" Shiru Mayraah tayi jin abinda yace, Dr Musharraf yace "A gida daya ku ke da ita?" Girgiza masa kai tayi kamar yana ganinta, yace "Hello" A takaice tace "Aa" Yace "Ohk, but ta bangaren Abba ku ka yi relating ko bangaren Ammi?" Mayraah tace "We will talk later, ana kirana" yace "Alright dear, take care, zan kira ki Anjima" Katse wayar tayi without saying anything to him, ta sauka daga kan gado ta fita daga dakin. Bayan magrib Mayraah na zaune parlon Ammi dake mata combing dogon gashinta don dama Ammi ce ke mata always, Mama Ladi kuma ta shiga makota tun da yamma har sannan bata dawo ba, Maheer ya shigo parlon da sallama, zaunawa yayi ya gaida Ammi, Ammi ta amsa without looking at him, Mayraah tace "Ina wuni" Yana kallonta yace "Lafiya lau" Bayan few seconds ya kalli Ammi yace "Tare mu ke da Haseenah za ku gaisa Ammi" Ammi tace "To ka shigo da ita nan mana" Mikewa yayi ya fita daga parlon, ba a dau lokaci ba sai gashi ya dawo tare da Haseenah dake sanye da dogon Hijab, Haseenah ta zauna kan carpet ta sunkuyar da kai tana murmushi, Ammi tace "Aa tashi ki hau kujera mana Haseenah" Haseenah ta girgiza kai tace "Aa nan yayi Ammi, ina wuni" Ammi tace "Lafiya lau Haseenah, ya gidan?" Haseenah tace "Alhmdlh Ammi" Haseenah ta kalli Mayraah tana murmushi tace "Gyaran gashi ake Mayraah" Mayraah ta ɗan kalleta tace "Ina wuni" Haseenah tace "Lafiya lau, ya gida" Ammi ta dau hulan Mayraah ta sa mata tace "Tafi ki kawo mata ruwa Mimi" Mikewa Mayraah tayi ta nufi kofa, Maheer ya bi ta da kallon gefen ido, can ya mike shi ma ya fita daga parlon, Ammi na kallon Haseenah tace "Fatan dai babu matsala Haseenah" Haseenah ta girgiza kai tace "Lafiya lau Ammi, ba komai" Ammi tace "To maa sha Allah, haka ake so" Haseenah ta kara jingina jikin kujera tana ɗan laluban kasan kujeran ta cikin hijab dinta taji ko ina is sealed, kallon agogo tayi sai kuma tace "Zan yi sallah Ammi" Ammi tace "Toh shiga daki Haseenah" Haseenah ta mike jakarta na makale cikin Hijab dinta, don dama Hijab din ba me hannu ta saka ba ta wuce dakin Ammi, Tana shiga dakin Maheer ya shigo parlon tare da Mama Ladi da tayi kasa da murya tana masa magana.....