Sashe 245
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ur evidence via 07087865788 Mayraah na biye da Maheer dake dauke da akwatin ta suka shiga main building din gidan, ya kunna wutan parlon cause everywhere was dark, ya juya yana kallonta yace "Nasan dai kinyi bacci a jirgi" Tana cire jacket din jikinta tace "Eh nayi bacci amma ai ba da yawa ba, though i am not sleepy now" Ya kalli agogo dake nuna karfe uku da kusan rabi yace "Yunwa fa?" Ta wara ido tace "First class fa muka shiga yayana, kasan me da me na ci?" Da mamaki yace "First class? Ke da wa? Hospital din ne ya biya maku first class?" Tayi murmushi ta zauna tace "Wa enda muka je conference din mana, tare muka dawo da su ai" Ya zauna yana facing dinta yace "So how was the conference like?" Ta langwabar da kai tace "Duk fa ban je ba Yaya" Yace "Baki je conference din ba?" Ta gyada masa kai tace "Kawai a gidanta na tsaya duk 2 days din nan" Shiru Maheer yayi bai ce komai ba amma deep down him yana mamakin amfanin zuwa da ita kasar da aka yi, can yace "Ku nawa ku ka je?" Tace "I think 4, yaya Abba yana nan?" Maheer ya girgiza kai yace "Yana kano" tace "Ohk.... yaya har bana son in tuna cold din kasar" Yayi murmushi yana kallonta, Hira ta dinga yi masa a parlon yana biye ta duk da baccin da yake ji don dama wajen karfe biyu ya kwanta, ya fara bacci ba dadewa ta kirasa, har kusan lokacin da za a tada sallan asuba suna zaune parlon, suka ji ana saukowa downstairs, Maheer ya kalli agogo yaga nan da minti goma za a tada sallah a masallaci, tuni Mayraah taji kamshin turarensa ta gane shi ne, yana saukowa parlor tun da ta kallesa sau daya ta dauke kai tana ci gaba da yi ma Maheer maganar da take masa, kallo daya shi ma ya mata ya nufi kofa ta bi sa da kallon gefen ido har taga ya bude kofa, tayi kasa da murya tana kallon Maheer tace "Yaya yaushe ya dawo?" Maheer yace "Jiya da rana" Ganin ya ja kofar parlon bayan ya fita ta wani taɓe baki tace "Yaya kasan abinda yayi min ne a UK?" Maheer yace "Me ya ma ki?" Tace "Ai babu ruwana da shi daga yanxu, kawai fa daga...." Mikewa tayi da sauri ganin Usman ya dawo Parlon ashe yana jikin kofar bai tafi ba, tana ganin ya nufota ta ruga sama da gudu tayi bangaren Ammi, ya juya ya fice daga parlon, Maheer dai ya bi sa da kallo, Mayraah na shiga parlon Ammi ta kulle kofar tana turo baki, Ammi da ta fito daga bandaki ta taho parlon jin alamar an shigo, buda baki tayi tana kallonta tace "Mayraah" Dariya Mayraah tayi ta tafi da sauri ta rungumeta tace "Ammi na dawo" Ammi tace "Ikon Allah, yaushe kika dawo?" Mayraah tace "Dazun nan wajen karfe uku" Da mamaki Ammi tace "To wa ya dawo dake gida?" Mayraah tace "MD din mu" Ammi tace "Maa sha Allah, welcome daughter" Mayraab bata yarda ta bar bangaren Ammi ba don tsoron tafiya dakinta take ta hadu da Usman, wajen karfe shidda Ammi ta sauka downstairs don hado mata shayi ta kawo mata da bread, Ammi na ajiye shayin ta tadda ta ta jinginar da kanta da kujera ta fara bacci, Ammi ta dafata tace "Tashi ki sha shayin sai kiyi wanka ki kwanta" Mayraah ta buda ido a hankali tace "Ammi akwatina na downstairs" Ammi tace "Aa babu akwati downstairs, ko Maheer din ya kai maki daki" Mayraah tace "Zanyi brush in fara wanka kafin in sha shayin" Ammi tace "To je kiyi, in kin gama sai ki hado wani shayin bari in sha wannan" Mikewa Mayraah tayi ta fita daga bangaren Ammi da sauri ta tafi dakinta, tana shiga ta kulle da makulli. Wajen karfe takwas tana parlon Ammi ta gama breakfast kenan Usman ya shigo parlon, tun da ta kallesa sau daya taki dago kai Ammi ta amsa gaisuwar da yake mata, yace "Zan je kaduna Ammi" Ammi tace "Kayi breakfast din?" Yace "Nayi" tace "Toh Allah ya tsare hanya, Allah ya kiyaye, yau din zaka dawo?" Yace "Aa sai Monday in sha Allah" tace "Toh Allah ya kai mu lafiya, ya tsare hanya, drive safely pls" Yace "In sha Allah" Daga haka ya mike ya nufi kofa, Ammi ta kalli Mayraah tace "Kun gaisa ne da shi?" Mayraah ta gyada kai tace "Tun daxu da na dawo" Mikewa tayi ta dau wasu chocolates da turare daya ta fita daga parlon, dakinsa ta nufa gabanta na faduwa, ta ɗan yi knocking kofar a hankali sannan ta bude, yana rufe karamin box dinsa, taki bari su hada ido ta kulle kofar, a hankali tace "Yaya don Allah kayi hakuri, i am so sorry about what happened" Jin yayi shiru ta daga kai ta kallesa, calmly yace "Wani abu ya faru ne?" Ta ɗan yi murmushi tace "Bayan nasan fushi kake da ni har yanzu, ni dai plss i am sorry yaya, ga tsaraba nan nayi maka" Bata jira cewarsa ba ta tafi ta bude jakar da ya ke rufewa ta zuba masa chocolate din a ciki ta kulle, sannan ta karasa inda turarrukansa suke a dakin ta ajiye turaren hannunta, sauke idonsa yayi daga kallonta, ta karaso kusa da shi tace "Pls ka hakura yaya?" Yace "I will think about it" Murmushi tayi tana kallonsa. Da yamma Maheer na zaune parlon Ammi, Mayraah ma na parlon, Ammi ta girgiza kai not convinced with what Maheer is telling her tace "Ni manufar tafiya da ita nake son sani tun da ba a bar ta taje conference din a kasar ba, why will they insist on going with her? This doesn't sound right Maheer, wallahi ni fa hankalina yaki kwanciya da aikin nan har yanzu" Maheer ya kalli Mayraah dake kallon Ammi, Ammi ta girgiza kai tace "Ni bazan boye maku ba kawai naji ban ma yarda da ceo din ba, ta yaya daga fara aikin yarinya ko wata biyu ba ayi ba ta dage sai anje wata kasar da ita bayan ga tsofaffin ma'aikata a asibitin, kuma tun da Usman ya dawo yace min gidanta ta sauke ta na kasa nutsuwa, a ina aka taɓa yin haka?" A hankali Mayraah tace "But Ammi she is so kind...." Ammi ta mike tace "Ban yarda da kindness din nan nata a kan ki ba, ai ba ke kadai bace worker a asibitin, why is she just being kind to you?" Daga haka ta yi wucewarta daki Mayraah ta bi ta da kallo, can ta daga kai ta kalli Maheer dake kallonta a hankali tace "Ammi zata ce kar in kara aikin ko?" Maheer ya kwantar da murya yace "Bazata ce ba, do not worry i will talk to her" Mikewa Mayraah tayi ta nufi kofa ta fita daga parlon ta koma dakinta. Da yammacin Washegari da ya kasance Saturday Mayraah ta gama jera kayanta da aka goge mata a press ta fito daga dakin zata sauka downstairs ta hango Maheer zaune Parlon shi kadai yana danna wayarsa, makalewa jikin karfen stairs din tayi tana kallonsa kamar ta samu TV, ta fi minti shidda tsaye a gurin kawai taga ya dago kai, da sauri ta manne da bango yanda bazai ganta ba tana zaro ido, amma tuni ya ganta, mikewa yayi ya nufo stairs din, tana ganin haka ta juya da gudu ta wuce bangaren Ammi, ganin wajen wayam ba kowa kawai ya sauka downstairs ya ci gaba da zaman sa. Da daddare Mayraah ta fito parlon Ammi zata tafi dakinta ta kwanta don har ta fara bacci ta hadu da Maheer a hanya zai je gun Ammi, yana kallonta ganin taki kallonsa zata wuce bayan ta gaishesa yace "Mayraah" Juyowa tayi tana murza idonta a hankali tace "Yaya bacci nake ji" Ya kama hannunta yace "I know... is there anything u are wanting to say?" Bata yarda ta kallesa ba still tace "Something? Like what?" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa taga kallonta yake, ta ɗan yi murmushi murya can kasa tace "Not at all yaya, dazu kawai naga kana ta gyangyadi shine nake kallon ka fa" Ya wara ido kafin yace komai ta marairaice tace "Zan fara baccin fa a tsaye a nan Yaya" A hankali yace "To fara" Jingina tayi da bango ta lumshe ido slowly, kallonta kawai yake babu ko kiftawa, bayan few seconds ita ma ta bude ido tana kallonsa, bude kofa da taji anyi ya sa ta kifta ido da sauri ta janye hannunta daga nasa, juyawa yayi ya nufi downstairs ta bi sa da kallo har ya sauka, Ammi ta karaso tana kallonta da mamaki tace "Me kike a nan? Baki tafi kin kwantan bane?" Kame kame ta fara yi sai kuma ta wuce dakinta da sauri, Ammi ta bi ta da kallo har ta shiga dakin ta kulle. Mayraah na isa daki kwanciya tayi ta lumshe ido, gaba daya ta nemi baccin ta rasa, tayi ta juye juye har daga karshe baccin ya dauketa wajen karfe sha daya da rabi. Da safe tana kitchen tana dafa ma Ammi shayi Maheer ya shigo kitchen din, tana gane shi ne taki dago kanta tana ci gaba da abinda take, Calmly yace "Good morning Mimi" Still not looking at him tace "Good morning yaya" Ya ajiye cup din hannunsa ya juya ya fita, sai a sannan ta bi sa da kallo sannan ta ci gaba da abinda take. Tana daki wajen karfe sha daya wayarta ya fara vibrate ta jawo ganin Dr Khalil ne tayi picking don tun da ta dawo sau daya ya kirata ya mata sannu da zuwa, bayan sun gaisa yace "Hope kin huta enough?" Tana murmushi tace "Sure" Yace "MD yace a gaya maki ki kawo account details dinki today, za kuma ki amshi ID card...." Mayraah tace "But i wrote down my account details the other day, ID card kuma ai gobe monday ba sai in amsa ba goben" Dr Khalil ya ɗan yi murmushi yace "To dai hakuri za kiyi ki zo tunda yace ki zo yau din, shi ma kin ga baya shigowa sundays