← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 162 OF 313

Sashe 162

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wani kwaskwarima da za ayi masa" Mayraah tace "Toh ba damuwa, goben zan zo in sha Allah" yace "To Allah ya kai mu" Maheer na zaune parlon Ammi da ya siyo ma abinci bayan magrib yana jiran yaga ta fara ci, har da magunguna ya kawo mata don dazu da safe tace masa bata jin dadi, a maganin ya hado mata har da na cin abinci da kuma wanda zai sa ta dinga samun isasshen bacci don kana ganinta kasan bata bacci, ga wani rama da tayi tun ma tana gidan Hajja, ganin har an kira isha Ammi bata da alamar fara cin abincin gabanta yayi kasa da murya yace "Ammi ki ci ko kadan ne ki sha magani pls, nasan fa tun safe babu wani abu da kika ci" Ammi ta kallesa cikin sanyin murya tace "Amma Maheer ina kake tunanin Mayraah zata har kwana uku yau, ba fa wanda ta sani Maheer, ba kuma inda ta sani, ko dai gidan radio da social media za a bada cigiyarta?" Maheer ya sauke boyayyen ajiyar zuciya ya kwantar da murya yace "Duk inda ma take tana cikin koshin lafiya in sha Allah Ammi, kuma addu'a kawai za mu ci gaba da yi har Allah ya karkato da hankalinta ta dawo gida, babu abinda zai sameta da izinin Allah, Mayraah ba ɓata tayi ba balle mu yi cigiyarta she just decided to leave, yanzu ko anyi cigiyar ma kamar muna kara tona ma kan mu asiri ne, ya mace ce ita ana saka cigiyar kowa da perspective din da zai kalli abun, gwara kawai mu ci gaba da addu'a kawai Ammi" Ammi ta share hawayen da ya sakko idonta bata ce masa komai ba, bude kofar parlon aka yi Mama Ladi ta shigo da plate cike da taliya da cup din shayi a hannun ta, Maheer ya daga kai ya kalleta yana nuna mata nata abincin da ya siya mata yace "Baza ki ci wannan din ba Mama?" Mama Ladi tace "Inji wa?? Ai sai can cikin dare idan na farka in sha Allah, taliya ce leda daya na dafa don tun da na sauka wallahi ban samu na ci komai ba, sai wani gantalallen biredi da ruwan shayi da na samu a kitchen Usuman ya bari" Daga haka ta zauna ta fara cin taliyar, Maheer ya ji dadin dawowan Mama Ladi don gidan babu kowa sai Ammi sai Usman da yake kwana gidan shi ma saboda Ammin, amma da safe kuma yake fita aiki, har Maheer ya fara deciding kiran Mama Ladin sai ga ta kamar an jefota dazu da rana lokacin ya dawo duba Ammi.... Maheer yayi nisa tunanin da yake sai kawai ganin Mama Ladi yayi a gabansa tayi kasa da murya tace "Ka sameni a palo Mashir" Maheer ya bi ta da kallo sannan ya kalli Ammi da har sannan taki cin abincin gabanta, ya mike ya bi bayan Mama Ladi suka sauka downstairs, kujera Mama Ladi ta nuna masa tace "Zauna ina zuwa" Ya zauna ya ga ta nufi kitchen sai ga ta ta fito da abun kwasan shara ta ajiye masa tana kallonsa, da mamaki yace "Wannan fa?" Mama Ladi ta wani kyabe baki tana murmushi tace "To a karkashin gadon uwarka na gani an makala sa yana ta reto, kasan ina sauka dazu ko zaunawa ban yi ba na fara kwaleman dakin duk na kwalkwale ko ina, to dai ga tsiyar da na gani karkashin gadon Ammi tana ta rayuwa kai in gaya maka Mashir, ni dai da naga duk a birkice take damuwa ya mata yawa ko nuna mata abun ban yi ba ma har yanzu, kuma wallahi dama ance surkarta ta ajiye asiri a dakinta...." Maheer dake ta kallonta ya katseta yace "Wa yace haka?" Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Gun bawan Allahn da naje neman taimako mana, kai baka ga abubuwan dake ta faruwa babu kan gado ba, ai mutum bai ga ta zama ba Mashir, har auren nan da Ubanka yayi wallahi an gaya min...." Maheer ya girgiza kai yace "Wajen boka kenan kike zuwa" Mama Ladi ta zauna kan kujera a gigice tace "Auzubillahi, don Allah ka rufa min asiri kar ka sa ni a bakin duniya Mashir, wani irin boka kuma? Ashe haka kake ban sani ba?" Maheer yace "Yanzu ke har yanzu baki hakura da zuwa gun mutanen nan da ke cinye maki kudi suna maki karya ba Mama? babu fa wanda ya isa ya maka abu sai Allahn da ya halicceka, in mutum ya sa wannan a rai to babu ta yanda za ayi masa mugun abu, ke kawai baki da aiki sai zuwa gun makaryatan banza marasu tsoron Allah" Mama Ladi ta saki baki tana kallonsa, a fusace tace "Kar ka sake gaya min maganar banza Mashir, kai wawa ne baka san komai ba baka san me duniya ke ciki ba, kuma laifina ne don wannan zancen ma ba da kai ya kamata in yi ba don kai ba sa'ar magana ta bace, tsinanniyar matar nan taka dai ita ta saka wannan mugun abu a dakin Ammi, shi yasa duk abubuwa suka cakude haka" Maheer ya kai hannu zai dau layan ta janye parkern da sauri tace "Rufa mana asiri, ni nasan inda zan kai sa, ni kaina bazan bari hannuna ya taɓa ba" Can dai yace "To meye manufar layan da aka sa kasan gadon kenan?" Mama Ladi tayi kasa da murya tace "A rabata da Mera ta tsaneta taji bata sonta kwata kwata, sannan kuma a tarwatsa mata gidanta ta dawo bora, kaga kuma yanzu tsakani da Allah wanne ne bai faru ba? Rabata da Meran ko tarwatsa gidan? Wai ma ina Mamuda don na tambayi Ammin tace min bata sani ba dazu" Maheer ya sauke ajiyar zuciya yace "Ya koma can wani gidan da ya gina da matar" Mama Ladi ta gwalo ido ta daura hannu a ka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wani gidan da ya gina? Amma ga dukkan alama matar ma matsiyaciya ce shaidaniya, zuwa kawai tayi ta mallakesa ta rabasa da Ammin, kai shegu dai sun yi yawa wallahi a duniya, yanzu ka gaya ma Ammin suna wani gida da katuwar matar?" a hankali yace "Ban gaya mata ba" a hankali Mama Ladi tace "To ka ja bakinka kayi shiru kar hankalinta ya sake tashi don naga ɓatan Mera ya gigitata gaskiya, kar ka kuskura ka gaya mata" Wayarta ta kunce a ɗan kyalle da ta cusa cikin hulan kanta ta mika masa tace "Kira min Mamudan" Maheer ya dinga kallonta, a fusace tace "Kira min shi mana" Amsan wayar yayi, yayi mata dialing number Abba sannan ya mika mata, ta amsa ta kai kunne, yana fara ring Abba ya daga, da karfi tace "Mama Ladi ce Mamuda..." Gaisheta Abba yayi, tace "Don Allah ina son ganinka yau na shigo garin" Yace "Toh sannu da zuwa Mama, zuwa gobe kenan idan Allah ya kai mu" Mama Ladi ta girgiza kai da sauri tace "Wani gobe? A yau nake son ganin ka Mamuda" Yace "Toh zan sa Maheer ya kawo ki inda nake" Mama Ladi tace "O'o ba ruwana gaskiya kawai ka shigo mota ka taho ina nan gidanka yanzu haka gani ni kadai zaune a parlor ba kowa" Abba ya dan yi shiru, sai kuma yace "To gani nan zuwa" tace "Yauwa ina jiranka" Daga haka ta katse wayar tana kallon Maheer tace "Ai kaga ni ba er banza bace da zan je in samesa a wani sabon gida bayan yayi watsin ruwan tsarki da 'ya ta" Shi dai Maheer bai ce komai ba. Maheer na barin gidan da minti arba'in Abba ya shigo wajen karfe tara da rabi kenan, Har sannan Mama Ladi na zaune parlon tana jiransa bayan ta gama cin abincin da Maheer ya kawo mata daxu, Abba na shigowa ya gaisheta da ladabi sannan ya zauna kan kujera yace "Ya hanya Mama?" A hankali Mama Ladi tace "Kai yanzu Mamuda so kake ranan gobe kiyama ka tashi da shanyayyen ɓarin jiki? So kake duk mu tafi aljanna kai kana wuta? Auren da har yanzu bamu gama na'am da shi ba a zuciyarmu shine har ka fara rashin adalci a cikinsa Mamuda? Ita Ammin ka gama cin moriyarta ta zama bola kenan yanzu kake nufi?" Sai kuma ta fashe da kuka tace "Ko me Ammi zata maka a duniya bata cancanci walakanci daga gareka ba Mamuda, balle baiwar Allahn bata taɓa maka komai ba sai biyayya da girmamaka tun kana talakan ka, sai yanzu don kaga ka rasa yanda zaka yi da kudi sai ka canza hali ka kasa hakuri da ɗan kuskuren da ta maka? Ko ka mance ɗan adam ajizi ne? Ammi ta taɓa maka wani gagarumin laifi duk zaman ku tare tsakaninka da Allah?" Abba yace "Yanzu tace maki na mata wani abu ne Mama?" A fusace Mama Ladi tace "Kayi mata mana, sai ta fada sannan za a san ka mata? don me za ka dau bazawarar da ka aura sama ta ka, ka kai ta sabon gida ku tare a can Ita kuma ku bar ta a nan?" Abba yace "Ai ni ban san tana gidan nan ba ma" Mama Ladi tace "Kai dai kaji tsoron Allah kaji tsoron kamun Allah Mamuda, wallahi kaji tsoron Allah ina gaya maka" Abba yace "Yanzu tun da nasan tana gidan duk ranan kwananta zan shigo gidan in kwana a bangarena" Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Haba Mamuda, don Allah kayi hakuri.... wallahi ni kaina nasan Ammi tayi kuskure nasan bata kyauta ba amma duk sharrin shaidan ne, kai shaida ne mutuniyar kirki ce Ammi, babu sa wa babu hanawa, kar ka yi mata mummunan hukunci saboda wnn ɗan kadɗarar ya fada mata, wallahi kaddararta ce wannan, amma kai kanka kasan duk bamu fi ta son Mera ba, kayi hakuri ka dubi halin da take ciki ka ja ta jiki ka maida komai ba komai ba har Allah ya dawo mana da gantalalliyar yarinyar nan da ta tafi inda bamu sani ba dama kuma ta saba shiga duniya da er matsala ta faru, Wallahi Ammi na cikin mawuyancin hali yanzu a kan batar yarinyar nan, da wanne kake so ta ji, ga kishiya ka dankara mata Mamuda?" Abba dai
Chapter 162 · 0% Book details