Sashe 221
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ur evidence via 07087865788 Washegari karfe bakwai na safe Mayraah ta tashi ta sauka downstairs zuwa kitchen don girka masu Breakfast, babu abinda babu a kitchen din na foodstuff, bayan ta gama girkin ta kai dinning table ta jera kan table din, Ammi ce ta sauko downstairs Mayraah ta karasa ta gaisheta da ladabi, Ammi tace "How was ur night?" Tace "Alhamdulillah, Ammi ga breakfast na gama...." Ammi tayi murmushi tace "To sannu da aiki daughter, shiryawa za ki je kiyi yanzu ko? naga karfe takwas ya wuce kar ki makara" Mayraah ta gyada mata kai tace "Eh yanzu zan je in shirya" Ammi tace "To kiyi maza" Mayraah ta wuce sama don yin wanka, sai karfe tara ta sake saukowa downstairs sanye cikin black Abaya da handbag dinta sai envelope me dauke da credentials dinta, har ta mance rabon da ta sa Abaya sai Hijab, she look so cute and stunning kuma Abayan ya haska farin fatarta ta dawo kamar wata balarabiya duk da bata yi make up ba sai eye pencil da ta sa a ido, da lip gloss da ta goga a lips dinta, Ammi da Abba na dinning area ta samesu, Ammi na ganinta dama ta fara hada mata tea, Mayraah ta durkusa ta gaida Abba ya amsa da murmushi yace "Kin tashi lafiya?" Tace "Alhamdulillah" Yace "You look cute my dear" Mayraah tayi murmushi tace "Thank you Abba" Ammi ta nuna mata kujera tace "Zauna kiyi breakfast, u are already late" Mayraah ta mike ta zauna sannan ta dau shayin da Ammi ta hada mata, Ammi ta ajiye mata plate din irish a gabanta, tace "Amma after the interview za ki dawo ai, nasan ba yau za ki yi resuming aikin ba dai" Mayraah ta gyada mata kai, Ammi tace "Sai dai a samu food warmer ki dinga tafiya da abinci saboda lunch" Mayraah ta zaro ido ta turo baki tace "Food warmer kuma Ammi kamar er yarinya" Ammi tace "To da yunwa zaki je kina aikin, don nasan ba siyan abinci zaki dinga yi ba" Mayraah tace "To ai har na gama school bana zuwa da abinci fa" Abba dai yayi murmushi yace "In bazata dinga zuwa da shi ba sai drivern ya dinga kai mata abincin da rana kawai" Mayraah dai bata sake ce masu komai ba a ranta kuwa har ta gama deciding in dai drivern za a ce ya dinga kai mata abinci kawai ce masa zata yi yana fitowa ya cinye a hanya ya koma gida da warmer din don babu abinda zata yi da abinci a wajen aiki kamar wata baby, Tana gama breakfast din ta mike zata kai plate da cup din kitchen Ammi tace "Aa bar shi, lokaci ya wuce" Abba yace "Driver zai yi dropping dinki a asibitin, jiya a airport ai wayarki ya kira yaje ya dauko ku so i assume you have his number idan kin gama abinda kike yi sai ki kirasa yaje ya dauko ki, he is ur driver from henceforth" Mayraah tayi murmushi a hankali tace "Nagode Abba" Abba yace "You are welcome dear" Sallama tayi masu ta dau jakanta da Envelope, Ammi ta mike tace "Kiyi addu'a kafin ki fita" Mayraah ta gyada mata kai, har bakin kofar Ammi ta rakata tace "Allah ya bada sa'a daughter, stay safe pls" Mayraah ta ciro black glasses dinta ta saka tace "Ameen Ammi, in sha Allah" Murmushi Ammi tayi tace "Yau dai gayu kike ji daughter" Er dariya tayi ta fita compound din taga driver zaune yana jiran ta, ya sauko da sauri ya gaisheta da ladabi, maimakon ta amsa sai ta gaishesa ita ma sannan ta bude front seat ta shiga don bazata zama comfortable tana baya yana driving dinta ba, bayan sun bar gidan ganin ya kama hanya bai tambayeta inda zai kai ta ba sai kawai ta gaya masa, yayi kasa da kai yace "Ranki shi dade ai Alhaji ya sanar min tun a jiya, nasan asibitin ma, da yake na taɓa yin aikin Uber" Mayraah tace "Ohk" Agogon wrist dinta ta duba taga karfe tara da rabi, tafiyar minti talatin suka yi zuwa asibitin, Mayraah na fara hango babban building din hospital din ta ji gabanta ya fadi, yanzu zata je ta hadu da wancan jarababben mutumin ita wallahi ko irin farin cikin ta samu aiki a asibitin ma bata yi, she is not even excited don gaba daya ya sa taji bata son asibitin a ranta but bata son tayi shunning effort din Dr Khalil ga kuma Abbanta dake ta farin cikin ta samu aiki da ma brothers dinta, wnn ne kawai ya hanata cewa bata son aikin tun a kano, bayan drivern yayi parking ɗan gaba da gate din asibitin don kar yayi hindering masu shiga da mota, Mayraah ta bude motar ta sauka tace "Nagode, idan na gama zan kira ka" Yace "Toh Hajiya Allah ya bada sa'a" Tace "Ameen" Tana juyawa ta ga wani lafiyayyen mota ya taho zai shiga asibitin, tuni masu gadi suka bude gate din suka ɗaga karfen gaban gate din inda motar zata wuce, bata ga wanda ke cikin motar ba don tinted glass ne, bayan motar ya shiga ta bi ta inda ake bi a shiga cikin asibitin da kafa, tana tafiya a hankali, Tana shiga reception din ta gaida nurse din dake wajen sannan ta tafi sama not minding yanda aka bi ta da kallo, ko basu ganeta bane oho, office din Dr Khalil ta nufa duk da bata ga motarsa ba a parking space, knocking tayi to be sure if he is around ya mata izinin shigowa ta bude kofar, yana ganinta ya mike tsaye cause da farko bai gane ta ba yace "Mayraah...." Ta ɗan yi murmushi ta karasa tace "Ina kwana" Yana gyada kai yace "Lafiya lau, ashe haka kika iya gayu, ai ni ban gane ki ba wallahi" Murmushi kawai tayi ta zauna, yace "Maa sha Allah, you look cute, jiyan ku ka shigo kenan?" Mayraah ta gyada masa kai, yace "That's good, Jiya Ceo ma ta shigo kasar, i think she will be around today kinsan gobe za mu je workshop din lagos" Mayraah tace "Oh ok, ya twins?" Yace "They are fine Alhamdulillah, are you together with the credentials?" Ta gyada masa kai yace "Ohk let me have a look first" Mika masa Envelope din tayi, ya amsa yana ciro takardun ciki yace "MD din ma yana nan ai, tare muka shigo dazu, sai da naje na daukosa a motar sa, shi yasa ban ma zo da tawa motar ba...." Statement of result dinta ya fara dubawa, ya dinga kallon result din babu ko kiftawa, can ya nemi kujera ya zauna ya kalleta ya buda ido sosai da mamaki yace "Really?" Ita dai Mayraah tayi shiru bata ce komai ba, buda baki yayi yace "First class?" Still ta ki ce masa komai, Yace "Ikon Allah.. this rare, are you this intelligent Mayraah? I am really surprise wallahi" Mayraah ta ɗan masa murmushi kawai, ya gyada kai yace "Maa sha Allah, i am really impressed, ai duk nan ina ga banda MD we don't have any staff with first class na degree..." Sai kuma ya fara dariya kamar wanda ya tuna abu, Mayraah dai taki ce masa komai har da ɗan daure fuska, Dr Khalil ya duba other credential din nata sannan ya maida su cikin Envelope yana murmushi yace "Za mu shiga theatre nan da minti talatin, bari in samesa if u can go for the interview now, don banda shi za mu shiga theatre din" Mayraah ta gyada masa kai tace "Ohk" Ajiye envelope din yayi ya fita office din zuwa office din MD, a long pavement din saman ya samesa ya fito daga office din CEO walking towards his office, Dr Khalil ya jirasa har ya iso MD yace "3 nurses, 5 Dr's for tomorrow's workshop, zaka yi booking flight din yau, 10 ticket in all" Dr Khalil dai na biye da shi har suka shiga office dinsa, MD ya zauna letting out a sigh yace "Yanzu zaka ga ta sake biyo ni nan" Dr Khalil yayi dariya yace "Amma ana gama workshop din zata koma ne?" MD bai ce masa komai ba ya mike ya dau tea cup dinsa ya tafi ya wanke ya dawo ya zauna yace "Nan da sati biyu ne Conference din da tace a England ai, or is it even US, na dai manta" Har ya bude flask din sai kuma ya sake kallon cup din ya mike ya tafi ya kara wankewa ya dawo, Dr Khalil yace "Ohk ku biyu za ku yi attending Conference din kenan?" MD yace "No pls... Dr Balogun should go" Dr Khalil yace "Kai ma kasan she can't do without u in anything ai" MD ya kalli wayarsa dake ring ya dauka yayi picking call din ya kai kunne, cikin minti biyu ya gama wayar ya ajiye, ya kalli Dr Khalil yace "What were u saying?" Dr Khalil ya kalli agogon office din saboda theatre da za su shiga he is cautious of time, MD ya sake tashi ya tafi ya wanke tea cup din hannunsa ya dawo, kiran Ceo ne ya shigo wayarsa ya zauna ya daga yana sauraronta, sai kuma yace "Ohk ma, i will bring them in 30 mins time" Bayan ya katse wayar ya tashi ya sake wanko cup din ya dawo, Dr Khalil ya taɓe baki ya mike yace "Are you ready? Za ta shigo interview din yanzu, cause she is around" MD ya daga kai ya kallesa, sai kuma ya hade rai yace "Waye haka?" Dr Khalil yace "You insisted she should come for the interview last week, so she is around today" MD yace "Ohh shine yasa CEO ke tambayana ita da naje office dinta yanzu kenan, ashe ta ganta ne, ita dai ta dage lallai sai tayi aiki a asibitin nan, ko dai mayya ce yarinyar nan?" Dr Khalil yace "Ga dai ta nan with her credentials kamar yanda ka bukata, so i will send her right away, don ni zan shiga theatre" Ko tankasa MD bai yi ba ya sake tafiya ya dauraye cup da zai sha coffee, kafin ya dawo har Dr Khalil ya fita daga office din, yana