Sashe 15
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washegari sai kusan karfe goma Mayraah tayi realizing basu yi waya da Dr Musharraf ba tun bayan da ya dawo da ita jiya, ta karasa wanke wanken da take yi a kitchen ta fito, Sabira ce kadai parlon tana goge goge, Mayraah ta wuce sama ta shiga dakin Maheer, tun karfe takwas ya fita aiki, yana fita kuma ta gyara masa dakin ta wanke bandaki, wayarta ta dauka ta zauna gefen gado tayi dialing number Dr Musharraf, har ya katse ba ayi responding ba, da har zata sake dialing kawai kuma ta fasa, ta daga kai jin an bude kofar dakin, Ammi ce ta shigo, Ammi ta karaso tana kallonta tace "Meye da dakin naki da kika yi hijira daga can yanzu?" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "Aa ba komai, kawai ina son Aunty Badiyya ta zama comfortable ne shi yasa" Ammi tace "To bana son haka, kuma kar in sake ganin haka, ki tattara yanzun nan ki koma dakin ki, kar ki sake cewa zaki kwana dakin Maheer saboda Badiyya na dakinki, as far as tana gidan nan to daki daya za ku zauna" a hankali Mayraah tace "Toh" Ammi tace "In ke tayi ma haka zaki ji dadi? Saboda ita ki ki zaman dakinki kamar ba er uwarki ba, naga dai ko cacan baki bai taɓa hada ku ba balle kice, to me ya janyo wannan abu haka? In kinyi hakuri duka duka ma kwana nawa ya rage maki a dakin Mayraah" Mayraah ta sunkuyar da kanta cikin sanyin murya tace "Kiyi hakuri Ammi" Ammi tace "Ki tashi ki koma dakin ki" Daga haka ta juya ta bar dakin, Mayraah ta bi ta da kallo. A hankali Mayraah ta bude kofar dakinta ta shiga ciki da sallama, Badiyya dake shiryawa bata ko amsa sallaman nata ba balle ta kalli inda take sai ma wani tsuke fuska da tayi, Mayraah ta karasa cikin dakin ta ajiye wayarta gefen gado sannan ta shiga bandaki rike da shower gel dinta da towel, Badiyya ta bi ta da kallon gefen ido har ta kulle kofar bandakin, Badiyya ta wani taɓe baki ta ci gaba da shafa cream dinta, ko minti biyar Mayraah bata yi a bandaki ba wayarta da ta ajiye gefen gado ya fara vibrate, Badiyya ta juya tana kallon wayar, da sauri ta dauka tana kallon number jikin screen din don da Emoji aka yi saving maimakon suna, wayarta ta jawo tayi snapping screen din sannan ta mayar da wayar inda yake ta ajiye da sauri, babu bata lokaci ta haddace number sa tayi snapping ta shiga True caller don ganin number waye, Musharraf Abdallah taga ya fito, wanda sai da gabanta ya fadi ganin sunansa kadai, a sanyaye ta ajiye wayarta ta karasa shafe shafenta ta mike ta dau kayanta ta saka ta koma gefen gado ta zauna, tayi nisa cikin tunanin da take bayan kusan minti ashirin taji fitowar Mayraah daga bandaki, mikewa Badiyya tayi ta figi wayarta ta fita daga dakin, Mayraah ta bi ta da ido, ganin bata kulle mata kofar ba ta karasa ta kulle kofarta. Musharraf ya shigo parlorn Maminsa ya zauna opposite dinta yana kallonta yace "Gani Mami" Mami tace "Why ain't u picking ur brother's call?" Yana karasa buttoning din t-shirt dinsa yace "Bana kusa da wayan" Mami tace "To ka kirasa za ku yi magana" Musharraf yace "Ohk" daga haka ya mike, Mami tace "Ina kuma za ka? koma ka zauna ka kirasa yanzu, don nasan ba kiransa zaka yi ba" Musharraf ya kalleta yace "Mami sauri fa nake, ba ni nace maki zan kirasa ba" Mami tace "Musharraf" Komawa yayi ya zauna ya jinginar da kansa da kujera, Mami tace "Kira sa yanzu" Musharraf ya hade rai yace "Mami shi fa gayen nan baya taɓa kiran mutum haka kawai, i know there is definitely something annoying that he wants to say to me" Mami tace "Why don't u respect the fact that he is ur elder brother Musharraf?" Musharraf bai ce mata komai ba ya dau wayarsa yayi dialing number brother din nasa wanda ko saving dinsa ma bai yi a wayarsa ba, yana fara ring ya sa handsfree, Mami dai sai kallonsa take, sai da ya kusa katsewa aka daga from the other side, Musharraf yace "Good morning" Yayan nasa yace "Baka ganin kirana ne?" Musharraf yace "Eh yanzu naga kiran" Daga daya bangaren brothern nasa da ake kira da Daddy yace "Akwai personal discussion da nake son mu yi akan auren nan da zaka yi" Musharraf ya ɗan yi jim, sai kuma yace "Ina ji" Daddy yace "Ok, amma da farko ina son sanin ko kana da issue da Farrah ne?" Musharraf yace "Wacece haka?" Ita dai Mami kallonsa kawai take, Daddy yace "Farrah ce baka sani ba?" Musharraf yace "Oh, me yasa ka min wannan tambayar?" Daddy yace "At the first place.... Why did u decide to date somewhere else ga er uwarka that has all qualities also" Musharraf bai san sanda ya mike tsaye ba yace "Is that so? Since ni ban yi ba ai kai zaka iya yi a madadina it's still not too late, look yaya ni dama nasan there is nothing good da zaka kirani ka gaya min, and sorry to say bana son kowa ya kara sa bakinsa a lamarin aurena, not even you! Hatta su Aunty Halima babu ruwansu da matar da zan aura, i am not a kid da za ayi min zabin matar aure... Kai idan ka tashi auren sai ka auri Farrah ai ka ma fi ni saninta" Yana gama fadin haka ya katse wayar, Mami kam buda baki tayi tana kallonsa da mugun mamaki, ya juya ya fice daga parlon, Dama ita she is not in support of cewar sai ya auri cousin dinsa kamar yanda dangin ubansa suka dage, beside she is not even interested da wannan hadin da suke ta dagewa a kai, Allah kadai yasan me suka kira Daddyn suka tsara masa shine ya kirata da batun ita kuma tace ba ruwanta ya kira ɗan uwan nasa sun fi kusa, to dai ga yanda kiran ya karke a gabanta, Wayarta ne ya fara ring ta dauka ganin Daddy ke kiranta ta daga ta kai kunne, Daddy yace "Mami daga wannan moment din na cire baki a kan duk wani issue da yayi concerning Musharraf, he can go an do whatever he wish, sannan wllh bazan zo daurin auren ba ma, kudi da na kai masa gidansu yarinyar ma nayi da na sani, kawai na bata lokaci na shigo kano akan yaron da ya bi ya raina kowa...." Mami tace "Wani magana kenan kake yi Daddy, kana da kamarsa a duniya ne? Ni fa ban ga lafinsa ba, he is not a kid da za ace lallai lallai sai an zabar masa warce zai aura, kuma ai gaskiya ya fada kawai choice of words dinsa ne are wrong, a gabana ya kiraka ai, meye za su dage sai ya auri Farrah?" Daddy yace "of course nasan zaki yi supporting dinsa ne ai Mami, to sai yaje ya auri yarinyar da zai aura, amma ni kam bazan zo daurin aurensa ba tunda har ni yayi ma rashin kunya a waya" Mami ta tabe baki tace "Yana da wani ɗan uwan da ya wuceka ne da zaka ce baza ka zo daurin aurensa ba? Ni don Allah sai anjima kar ku ɓata min rai kai da shi" Daga haka ta katse wayar ta mike ta tafi wajen Musharraf, yana kokarin fitowa daga dakinsa tace "Ina za ka?" Ya ɗan kalleta yace "Zan fita ne" Mami tace "Musharraf shi yayan naka ka gaggaya ma magana babu kunya a gabana?" Musharraf yace "Mami ke baki ji maganan da yake min bane, he just love controlling me alhalin naji kunce da shekara biyu kawai ya girmeni, nasan ai bashi da girlfriend to don me bazai yi dating farrah ba su yi aure" Mami ta kamo hannunsa tace "I know they are wrong but ba haka ya kamata kayi approaching maganar da yayi maka ba, yayi deserving some respect from u, for peace kawai kamata yayi kace masa u are not interested shikenan" Musharraf yace "Mami ni fa as far as u are not against my marriage to babu wanda ya isa ya hanani abinda nake so, tun daga kan Daddy har su kawu da su Aunty Halima, nobody" Mami ta sauke ajiyar zuciya tace "Yanzu ya batun lefen jiya baka ce min komai ba" Yace "I decided to give her the money su siya kayan" Mami tace "Nawa ka bata?" Yace "7M" Mami tace "Why not make it 10m?" Yace "Zan kara mata" Mami tace "To ka dai ce mata banda Abaya da akwati ko?" Yace "Yeah" Badiyya na zaune dakin Haseenah tana goge hawayen da yaki tsaya mata cikin rawan murya tace "Haka kawai kun sa in koma gidan ni ban ga amfanin komawata ba yau kwana biyu kenan, tun da naje dama ta tattara ta koma dakin Maheer, ba wani information da nake samu banda numbersa da nayi snapping dazu da ya kirata tana bandaki, kuma kinga ai tun dazu muke kira baya shiga saboda settings dinsa da ya saka idan baya da numberka bazaka samesa" Haseenah tace "Kilan Private line dinsa ne, amma babu ta yanda likita zai sa wayarsa a wannan setting din, definitely yana da wani layin da kowa ke samunsa" Badiyya ta jinginar da kanta jikin gado tana shessheka tace "Wllh na gaji Haseenah, wasa wasa fa yau saura wata daya bikin" Haseenah ta sauke ajiyar zuciya tace "Ni zaki gaya ma sauran kwana nawa bayan rana daya ne da nawa da Maheer, ai ko nima an cuceni wannan damuwar da aka sa ki, banda haka da yanzu ai har dake zamu yi ta shirye shiryen bikina, amma ace ana ta abu ba ke" Badiyya dai bata ce komai ba sai hawaye take, Haseenah tayi kasa da murya tace "Toh kece da gaddamar tsiya, Nan nan Zaliha ta kawo mana shawara shekaranjiya kince ba haka ba, wannan kadai ne fa option dinmu yanzu Badiyya" Badiyya tace "Ke ni fa bazan dau kudina in kai ma wani kato wai Malami ba, wa enda na kai a baya wani result din na gani? Duk karyace