← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 225 OF 313

Sashe 225

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ma'am, babu ticket for that same flight... Sai dai wani jirgin, wannan da muka yi booking jirgin ya cika, sai ma da muka yi contacting dinsu suka soke wasu ticket din aka samar mana 10 din da muke bukata...." Dr Khalil ya saki baki yana kallon MD don ko booking ticket din basu kai ga yi ba tukunna, Ceo tace "Ohk, that's fine" Daga haka ta juya ta fita daga office din, Dr Khalil na girgiza kai yace "Ka ji tsoron Allah Dr Aliyu, what's there idan anje workshop din da ita, ai ire irensu ma ya kamata...." Dakatar da shi MD yayi yace "Baza ta je ba, yaushe ma aka bata cikakken aiki a nan din da zata je workshop din manyan likitoci a Lagos, wa enda suka yi shekara da shekaru a nan ma basu je ba sai ita mara kunya da ko fara aikin bata yi ba" Dr Khalil yace "Toh dai Ceo da kanta ai tace aje da ita kuma ta san sabuwa ce" MD yace "To ni kuma as the MD of this hospital nace banda ita, baxata je ba, kuma abinda baka sani ba ni ba full employment na bata a asibitin nan ba, she will just work as an Intern in here, not a staff, beside ko service fa bata yi ba daga amsan statement of result kawai sai aiki?" Dr Khalil yace "Thank God dai ba government hospital bane nan din balle kace, kuma wannan kamar bakin ciki kake mata...." MD yace "Shi din ne ma" Juyawa Dr Khalil yayi zai fita, MD yace "Book the flight immediately pls... 10 seats" Dr Khalil yace "Ohk" Daga haka ya fita ya kulle masa kofa. Yana komawa office dinsa yace "Mayraah if it's okay anjima idan na amso su daga gida Ummi ko da daddare ne sai in kai maki gida, cause kamar babu scrubs din available yanzu" Mayraah ta mike tace "Ohk nagode" Yace "You are welcome, ki gaida su Ammi" Tace "Za su ji" Daga haka ta fita daga office din don tun dazu Drivernta ke waje. Wajen karfe biyu Mayraah ta isa gida, tana bude kofar parlon ta ga Usman a zaune shi kadai, sau biyu yana daga kai yana kallonta wanting to be sure ita din ce, ta karaso parlon ta ɗan yi murmushi tace "Yaya yaushe ka zo?" Ya hade rai yace "Yaushe kika fara wannan dressing din in zaki fita?" Tayi kasake tana kallonsa, can ta zagaya inda yake zaune, ya dinga kallonta daga sama har kasa, tace "Yaya me ya faru da dressing din?" Yace "Tambayata kike? Ok barin hijabs din naki kika yi a kano kenan?" Ta ɗan turo baki tace "Yaya Abaya ce fa ba wani abu ba, beside....." Calmly yayi shutting dinta yace "Keep quiet" Ammi ce ta fito daga kitchen ta tsaya tana kallonsu, A nutse yace "Kar ki sake wannan dressing din a gidan nan, were you trying to get someone impressed a hospital din?" Ammi tace "Ban gane kar ta sake wannan dressing din ba, meye da shigar tata da bazata sake ba?" Ya ɗan daga kai ya kalli Ammi don bai ma san ta fito daga kitchen din ba, Mayraah dai sai turo baki take, can dai yace "To gidan biki za ta Ammi, haka ake zuwa interview dama?" Ammi tace "Aa ba ruwanka, let her dress the way she wants as far as ba wando ta saka ta fita ba, meye laifin Abaya?" Mikewa yayi ya bar parlon ya shige daki, Mayraah ta bi sa da kallo, Ammi tace "Rabu da shi ki tafi kije ki yi wanka ki sauko ga abinci na gama" Mayraah ta gaisheta a hankali sannan ta wuce sama, wajen karfe uku ta sake saukowa downstairs bayan tayi wanka tayi sallah sannan ta canza kayanta, dinning area ta tafi ta debi abincin da Ammi ta ajiye a nan, spoon daya ta ci, sai kuma kawai ta mike ta nufi dakin da taga Usman ya shiga dazu, a hankali tayi knocking kofar dakin, tana ta tsaye taji ya bude kofar ta daga kai tana kallonsa, sai kuma ta bi ta gefensa ta shiga cikin dakin ta juya tana kallonsa ta marairaice tace "Yaya did i dress indecent?" Kulle kofar yayi ya koma ya zauna, ta bi bayansa tana kallonsa, yace "Amminki ta ce ba indecent bane... She gat your back" Murmushi tayi ta durkusa gabansa tace "Toh kayi hakuri yaya bazan sake ba, kuma ma ai uniform zan dinga sa wa ba kayan gida ba daga yau" shi dai kallonta kawai yake, ta mike tace "Have you eaten?" yace "Yeah" Tace "Toh zan je in ci abinci" Daga haka ta juya zata fita yace "Mayraah" Juyawa tayi ta kallesa, ba haka nan duk brothers dinta ke kiran sunanta kai tsaye ba, yace "In kin gama abinda kike yi da daddare ki shigo za mu yi magana" Da mamaki take kallonsa wondering maganar me za su yi, sai kawai tace "Toh in sha Allah" Daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita. Bayan magrib Mayraah na zaune kan darduma wayarta ya fara vibrate ta dauko a zaton ta Maheer ne don tayi masa kira har biyu bai yi responding ba, Dr Khalil ne ke kiranta, ta daga kiran bayan sun gaisa yace "Na dauko maki Scrubs din a gidan Ummi, can i come over yanzu in kawo maki, kin san za mu je lagos gobe da safe and probably monday za mu dawo" Mayraah tace "Ohk to Nagode" Yace "Address din fa?" Tace "Bari in tura maka" Katse wayar tayi ta tura masa address din, bayan minti sha biyar ya sake kiranta yace gashi a kofar gida, mikewa tayi sai da ta fara zuwa ta gaya ma Ammi sannan ta fito daga gidan sanye da hijab dinta har kasa, tana ta kallon motar wondering ko ya canza mota ne, ta dai karasa ya sauke glass din yana kallonta da murmushi yace "Good evening" MD ta gani zaune front seat ya wani hakikance, Dr Khalil ya sauko daga motar ya zagayo back seat ya dauko mata uniform din ya mika mata yace "Sai fa da yan sanda suka tsayar da mu kafin mu shigo nan, wai wajen wa za mu" Mayraah tayi murmushi tace "Sai kace masu wajena mana" Dariya yayi yace "Eh lallai kam wajenki" can yayi kasa da murya yace "Baki gaida boss dinki ba Hajiya" Mayraah ta sake kallon MD da yayi kasa da kai yana kallonta ta Mirror, don unguwan haske tarrr kamar da rana ko ina fitilu ne, yana ganin ta juyo ya dauke kai yana danna waya with a serious face, a takaice tace "Ina yini" jin bai amsa ba Khalil ya karasa har kusa da door din motar yayi knocking yace "Ana gaisuwa Oga" MD yace "Dalla ka zo mu tafi kana bata min lokaci kasan ana jirana" Mayraah na kallon Dr Khalil tace "Nagode Dr sai da safe" Ya mata murmushi yace "Ki gaida su Ammi" Tace "In sha Allah" Daga haka ta shige cikin gida, Dr Khalil ya zagaya ya shiga driver seat, MD ya kallesa yace "Burin ka kawai ka dinga ja mana raini wajen yarinyar nan, yanzu sai ta ga kamar biyoka nayi fa in her stupid mentality, ji wani iyayi da take, to meye da Unguwan nan?" Dr Khalil yace "Aa bawan Allah, sai da nace in ajiye ka eatry ka jirani in zo in kawo mata sakon kafin in koma in daukeka muje inda za mu kace no way sai ka biyo ni" MD yace "To ni ɗan iska ne zan yarda ka ajiyeni eatry ba abinci nake ci a eatry ba?" Dariya Dr Khalil yayi yace "To nan dai ne gidansu incase....." MD ya kallesa yace "Incase what?" Dr Khalil na murmushi yace "Incase Watarana mana" Mayraah na komawa dakinta ta dau wayarta taga miss calls din Maheer, murmushi tayi har zata kirasa sai kuma ta tuna za su yi magana da Ya Usman kamar yanda yace mata dazu, ta ajiye wayar with the intention of calling him back idan ta dawo, sannan ta sauka downstairs ko hijab dinta bata cire ba ta nufi dakin da ta gansa ciki daxu.
Chapter 225 · 0% Book details