← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 313

Sashe 150

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake.* Karfe biyu da rabi Mayraah ta sauka daga mota rike da karamin jakarta tana bin park din da kallo, kowa hada hadar gabansa yake cikin hanzari don hadari ne sosai a garin, muryar dreba da taji yana tambayar ko bata da kaya ne a booth din mota ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi a inda take tsaye, ta girgiza masa kai ta nufi hanyar da ta lura nan ake bi a fita daga cikin tashar, tsaye tayi bakin titi tana makale da jakarta a dai dai sanda aka fara iska sosai ta dinga bin duk motocin da ke wucewa da kallo, yan adaidaita sahu sai tambayarta inda za ta suke, kan kace me aka fara yayyafi, ta fara dube duben inda zata raɓa kar ruwan ya jikata, wani shagon point of Sale da kuma accessories din waya ta nufa da sauri ta tsaya a ɗan rumfan shagon nan aka fara ruwa kamar da bakin kwarya, saboda karfin ruwan sai ya kasance da ma rumfan da take karkashi gwara babu, don ruwan har ya fara jikata, me shagon na ganin haka yace "Ki shigo ciki Hajiya, ai wannan jikewa zaki a wajen" Mayraah ta juya da sauri ta shiga shagon tace "Nagode" Kan plastic chair ya nuna mata ta zauna, ruwa aka yi sosai don sai kusan hudu da rabi ruwan ya ɗan tsagaita, me shagon har bacci yayi ya tashi, ita dai Mayraah na takure kan kujeran don wani sanyi take ji sosai ga gajiya da jiri da take ji, gaba daya tayi weak wanda ko ba a fada mata ba tasan symptoms din low bp ne, Mai shagon yace "Hajiya ko dai a tare maki Napep tunda ruwan ya ɗan tsagaita ki tafi gida, naga kamar sanyi kike ji, kuma babu alamar daukewar ruwan nan yanzu" Mayraah ta juya ta kallesa kamar baza ta ce komai ba, sai kuma a hankali tace "Ni daliba ce yau na fara zuwa garin ban san ko ina ba, ban san kowa ba, ina son zan kama gida irin na dalibai ne, to ban san ta yaya zan fara ba" Mutumin yace "Jami'ar nan da take gwagwalada?" Mayraah ta gyada kai da sauri, mutumin na gyada kai yace "Chabb ae ko gida wahala yake a garin nan sai shegen tsada, dama dai Suleja kika ce to can ma ni nake, business dina ne kawai ke fitowa da ni cikin gari, ni nasan yanda za a samu gida me kyau a suleja, sai dai kuma Sulejan yayi maki nisa zuwa gwagwalada gaskiya, ga tsadan kudin mota" Da sauri Mayraah tace "Aa in dai za a samu bai yi min nisa ba" Mutumin yace "Atoh in zaki iya shikenan, ina daga nan zan sa a bincika min gida a can, ai garinmu ne Suleja iyayena da matana duk suna can" A hankali Mayraah tace "Toh Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi, ka bincika min sai in bada kudin a kama min" Yace "In sha Allahu zan bincika a yau kuwa, amma dai yanzu makarantar zaki tafi? Kin dai ga garin kara lullubewa yake" Mayraah ta kalli sama da ya kara lullubewa tace "Eh tare min adaidaitan" Mikewa yayi ya fita cikin yayyafin ya samu adaidaita sahu sannan ya dawo yace "Ga can wani na tare maki har na maki ciniki da shi kudin kawai za ki basa" Ta mike tace "To nagode sosai" Yace "Yanzu lambar wayarki zaki bada a kira ki in an samu gidan ko ya za ayi?" Tace "Ai wayata ta mutu, goben dai zan zo in sha Allahu sai in ji ko an samu" Yace "To ba laifi, Allah ya kiyaye" Fita tayi daga shagon tana jin sanyi sosai ta tafi ta shiga adaidaita sahun da ya tare mata, bayan sun ɗan yi nisa Mayraah na kallon mai adaidaita sahun a hankali tace "Bawan Allah akwai hotel don Allah a unguwan da za mu je yanzu?" Yace "Kwarai kuwa, iri iri ma kuwa" Tace "Toh kai ni daya don Allah" Yace "Toh ba damuwa" Yana isa wani hotel yayi parking yace "Kinga ga wani nan, me kyau ne wannan naga yan mata na zuwa sosai" Mayraah na kallon hotel din tace "Toh Nagode" Ta sauka a daidaita sahun zuwa yanzu ruwan ya sake dawowa da karfi, tana kallonsa tace "Nawa ne kudinka" Ya fada mata ta ciro a handbag dinta ta basa sannan ta shiga cikin hotel din da sauri ruwa na jikata, a reception ta zauna bayan sun yi confirming payment dinta suka bata makullin dakinta ta wuce dakin, tana shiga ta kashe Ac din dakin ta kwanta ta rufa da bargo saboda sanyin da take ji sosai, har kusan magrib tana nan a haka gashi bata yi sallah ba, gashi tana jin kamar alamar cramps wanda hakan yayi mugun daga mata hankali, to yanzu ya zata yi ita kam, ta yunkura ta tashi ta shiga bandaki ta dauro alwala ta fito ta fara Sallah. Tun bayan da Abba ya gama karanta takardan da Hajiya Amina ta mika masa yake zaune parlor ya kasa cewa komai, ya furta Innalillahi wa inna ilaihi raji'un ya fi a kirga a zuciyarsa, ita dai Hajiya Amina na inda take a tsaye ita ma ta kasa cewa komai, daga karshe kawai ta juya ta bar parlon, kiran Maheer ne ya sake shigowa wayar Abba for the third time, Dagawa Abba yayi, calmly yace "Kana ina yanzu?" Maheer yace "Ni ina asibitin har yanzu, Ammin ma taki saurarata ta bar asibitin yanzu haka, ta ma ki jiran in tafi da ita a mota" Abba yace "Bayan kai babu kowa a asibitin?" Maheer yace "Eh yanzu wasu cousins dinta suka iso..." Abba yace "To ka taho gida yanzun nan" Daga haka ya katse wayar, Maheer didn't get dalilin da zai sa Abba yace ya taho gida yanzu bayan ga abinda ke faruwa, kawai dai ya tafi parking space din asibitin ya kama hanyar hoping all is well, Duk da rashin nutsuwan dake tare da Abba haka nan ya kira abokinsa wanda shi ma babban ɗan sanda ne, in brief ya sanar masa abinda ke faruwa, abokin nasa yace "Wani Division ne ranka shi dade?" Abba that was just confused don kusan Absentmindedly yayi masa bayanin yayi wani sigh yace "I don't really know" police officer din yace "To a wani anguwa abun ya faru, sai in kira division din anguwan with immediate effect" Abba ya fada masa anguwan da gidan Maheer yake, Officer din yace "Ohk, give me a minute" Daga haka ya katse wayar, Abba ya ciro handkerchief ya share zufar goshinsa ya mike ya fara safa da marwa a parlon yana sake nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a zuciyarsa, sake duba takardan yayi for the countless time, kawai ya koma kujera ya zauna ya rike kansa yana kiran Allah a zuciyarsa, duk wannan abubuwan dake faruwa Abba bai taɓa jin haushin Ammi yanda yake jin haushinta yanzu a zuciyarsa ba, Bayan some minutes wayar Abba ya fara ring, ya duba ganin officer din ne ya daga, Officer din yace "Yauwa after making series of calls an samo division din yanzu, in sha Allah za a saketa sannan ayi sulhu a gida tunda Allah ya takaita ita warce aka ji ma raunin is responding to treatment, wannan family issue ne kawai dama a gida ya kamata a sasanta, Allah kuma ya kiyaye gaba" a hankali Abba yace "To nagode kwarai da gaske officer" Sallama suka yi Abba ya katse wayar ya sake mikewa yana zaga parlon, dai dai nan aka bude kofar parlon Mama Ladi ta shigo duk ta hada zufa, Abba dai kallonta kawai yake har ta Karaso cikin parlon tace "Mamuda yan sanda fa sun yi ramm da Hajja" Sai kuma ta fashe da kuka tace "Wayyo Allahna, wayyo Allah, Allah sarki yayata, wallahi da dai ni suka tafi da suka bar ta amma suka ki sauraron haka, da kafa na taho gidan nan Mamuda tsabar gigicewa ga yunwa ko gidan ban rufo mata ba, unguwan nan ya cika babu matsaka tsinke in gaya maka, sai ga Hajja a motan yan sanda, tunda uwata ta haifeni ban taɓa ganin irin wannan tashin hankali da bala'i ba sai yau, wai ace surkan jikanta suka dauko mata yan sanda kusan goma" Abba ya katseta don surutunta kara masa ciwon kan da yake ji yake, a takaice Abba yace "Nayi waya an saketa" Mama Ladi ta fashe da sabon kuka tace "Allah Ubangiji yayi maka albarka, in ba kai din ba wallahi sai dai ta kwana cikin barayi a self, tana kuka fa basu ji tausayin tsufarta ba suka dinga figarta har kofar gida, kuma ba kowa ya ja mata ba Badiyyah" Maheer ya shigo parlon da sallama, ya nufi Abba yana kallonsa ganin yanayinsa amma ya kasa cewa komai, Abba ya mika masa takardan hannunsa yana kallonsa ya girgiza kai sounding so pained yace "Ur mother failed me" Daga haka ya wuce sama, ita dai Mama Ladi sai zare ido take tana bin takardan hannun Maheer da ido, Sai da kan Maheer ya sara yana fara karanta first 3 lines din takardan kuma yaga writing din Mayraah, ya ji kafafuwansa sun kasa daukansa ya zauna kan kujera zuciyarsa na bugawa yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Mama Ladi ta zaro ido a tsorace tace "Lafiya, takardar mecece Mashir?" Kasa bata amsa yayi ya rike kansa. Hajiya Fauziyya da mukarrabanta dake cikin mota za su koma asibitin da aka kwantar da Haseenah bayan ta tabbatar mai gidanta ya bada order din kada a bada belin Hajja sai an kama Badiyyah tukun wayarta ya fara ring, dauka tayi ganin mai gidan nata ne ta daga tace "Abban Ikram muna hanyar asibitin yanzu haka, don Allah ka kara jaddada masu kada a bada belin matar nan sai an kamo matsiyaciyar yarinyar" Mai gidan nata yace "Ai ina jin
Chapter 150 · 0% Book details