Sashe 54
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
+234 901 499 6620 [6/13, 7:29 PM] Khaleesat Haiydar💖: Bayan fitarsu Haseenah da yan uwanta Mayraah ta daga kai tana kallon Ammi cikin sanyin murya tace "Ammi ko in maki shayi?" Aunty Mariya tace "Eh kawo mata" Mikewa Mayraah tayi Ammi ta bi ta da kallo har ta fita daga parlon, Hajiya Safiyya na kallon Ammi tace "Kin dai ga Mayraah Alhamdulillah ta samu lafiya, don haka kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki ki cire komai a ranki don jininki ya samu ya dawo dai dai" Da damuwa Aunty Mariya tace "Ai shine, just forget everything that happened we should face reality, there is surely reason for everything a rayuwar nan" Aunty Mariya na kai wa nan ta mike ta shiga dakin Ammi ta dauko babban duvet zata kai dakin da aka sauke su Haseenah da wa enda suka kawota.... Mayraah na kitchen tana dafa ma Ammi shayi da yaji kayan kamshi ga madaran gwangwani da ta juye ciki yanda dai tasan Ammi ke son ayi mata, ita kadai Ammi ta fi son tayi mata irin shayin, Absentmindedly ta ke aikin da tunani iri iri a zuciyarta, zuwa yanzu kuma ji tayi zuciyarta ya kasa yarda wai ba su Ammi suka haifeta ba, she is now just finding it hard to believe, ta yaya ma za a ace ba Ammi ce ta haifeta ba bayan ita kanta ta san irin son da Ammi ke mata, or are they pranking her? Ji tayi an bude kofar kitchen din, ba tare da ta juya ba ta gane wanda ya shigo don haka yake bude kofa a ko ina, daga baya kuma taji kamshin turarensa, bayan some seconds ta dan juya ta gansa ya dau plate yana zuba abinci, ta kashe gas din sannan ta dau tea pot din ta fara tsiyaya shayin cikin cup, ganin zai fita daga kitchen din ta juya ta kallesa suka hada ido sai kuma ta sunkuyar da kai tace "Don Allah ina son inyi amfani da wayarka" Yace "Yana daki" Daga haka ya fita ya kulle kofar, Mayraah ta ɗan yi goge goge a kitchen din sannan ta wanke hannu ta dau shayin Ammi ta fita, zuwa yanzu babu kowa a gidan sai baƙin da suka zo daga nesa, duk aka bi ta da kallo har ta haura sama and that made her so uncomfortable, yanzu kallon ba er gidan ba ake mata kenan, tana shiga parlon Ammi ta durkusa gabanta ta ajiye mata shayin tana kallonta ta zauna gefenta, cikin sanyin murya Ammi tace "Nagode" Maheer ne ya shigo parlon, ya zauna kujera yana kallon frnd din Ammi ya gaisheta, ta amsa da fara'a tace "Ango ka sha kamshi" Ya ɗan yi murmushi ya kalli Ammi yace "Ammi ya jikin" Ta dau shayin da Mayraah ta ajiye mata tace "Alhamdulillah" Yace "Allah ya kara maki lafiya" Tace "Ameen" Yana kallon shayin gabanta yace "Wannan kamar shayin Mimi" Frnd din Ammi tayi dariya tace "Ai kam yanzun nan taje ta yo sa a kitchen, ni ma kamar ince a tsammin" Mayraah ta kalleta tana murmushin karfin hali tace "Akwai saura bari in debo maki" Hajiya Safiyya tace "Aa zan je da kaina in debo, ke da ba lafiya gareki sosai ba" Mayraah ta sunkuyar da kanta tana wasa da darduman da Ammi ke zaune, Maheer dai sai kallonta yake, bayan few seconds yace "Kin ci abincin Mimi?" Ta daga kai tace "Na ci" Yace "Okay ina jiranki dakin Usman" Yana fadin haka ya mike ta bi sa da kallo har ya fita. Haseenah dake zaune kan gado da kawarta Zaliha dake mata magana kasa kasa ta fusata cikin daga murya tace "To wai ke sai ma kin bata bakinki sai kace baki san ni ba Zaliha" Kanwar mamarta Hajiya Farida dake zaune kasa inda aka masu shimfida da sauran sisters dinta ga abinci iri iri da aka dire masu ta daga kai ta kalli Haseenah rai bace tace "Wai ke wace irin mahaukaciya ce mara kamun kai kina daga mana murya a gidan surkai? Sannan ba nace ki dau mayafin nan ki rufe jikinki ba tunda ba daina shigowa suka yi ba, wato sai kin gama gwada ma kowa ke fitsararriya ce ko?" Haseenah ta hade rai tace "Aa ni gaskiya Aunty zafi bazai hallaka ni ba a banza, ai ba nan ya kamata a zo a jirge ni ba kamar wata mara galihu" Aunty Mama ta kyabe baki tace "To nima dai shi na gani, na zata in kin gaida surkar taki da kakarsa gidanki kuma za mu kai ki, amma sai naga an kawo mu daki anyi shimfida an dire abinci ga mayunwata, a ina ma aka taɓa haka? Aa ni ban taɓa ganin haka ba tunda uwata ta haifeni, Aure duk ba wani armashi kamar auren dole, ni wllh sai nake ganin kamar ma ba wani sonta yaron yake ba ita ce kawai ke haukanta a kansa, atoh tunda gashi ya fi ba matsalar gidansu Muhimmanci a kanta" Aunty Farida dai ta tabe baki tace "Ba tace taji ta gani ba, mu kuma meye namu, kina jin abinda tsamurarriyar tsohuwar can ta gama fada a kunnenmu ai, me yafi wannan walakancin? Ga Salmanu bawan Allah da ya nace mata kememe yarinyar nan taki wai bai yi boko ba sannan ba shi da kyau da qualities din da take so, to wa ke ta wani kyan banza yanzu in dai mutum na da nera meye kuma wani kyau, duk shekara fa Salmanu sai ya je hajji har ma ya biya ma wasu, gashi ba wai zata zauna da kishiyar bane tunda har ya nuna mata ginin da yake mata zai ajiyeta ita kadai, kuma gidajensa sun fi biyar a garin kano, ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba yafi wannan da ta makalema arziki, shi wannan ina ga ubansa ne kaɗai ke da arzikin ma, duka duka nawa ne albashin likita" Bude kofar dakin aka yi duk suka yi shiru, Mama Ladi ta shigo tana rafka uban sallama, Haseenah ta fara kiciniyar yafa gyalenta ta rufe fuska da sauri, Mama Ladi na washe hakora ta dafe gwiwa tace "Sassannunku da hutawa fahh, in ji dai bakwa bukatan komai ko? Abincin ma idan bai isheku ba sai a kwaso maku sauran dama don ku aka girka, Ko katifa za a karo maku ku baje nan kasa?" Haseenah sai hararanta take ta cikin mayafi don har taji tayi mugun tsanarta, Aunty Mama na kirkiran murmushi tace "Aa hakan ma ya isa Babaa, mun gode sosai wllh" Mama Ladi tace "To bari a buda maku tagogi yanda iska zai shigo maku a wadace ba algus" Tana fadin haka ta tafi ta fara bude windows din har da net din jiki duk ta wangale sai ga su tsirara suna hango waje, duk suka dinga bin ta da kallo har ta gama ta fice daga dakin, Aunty Fauziyya ta rike haɓa tace "Anya tsohuwar nan na da lafiya ma kuwa, wannan ai sai sauro ya kashe mu kafin gari ya waye, ji wani shegen buda window fa da tayi kamar an sa ta, ga Ac a kunne meye na bude mana window" Aunty Mama ta ja tsaki ta mike ta tafi ta kullo windows din tana cewa "Wallahi in dai naga babu alamar kai ta gidanta gobe da safe to tafiyata zanyi ba da ni za a zauna gida nan har yamma ba kamar wata mara abun yi..." A hankali Mama Ladi ta bude kofar dakin da Hajja ke ciki tana lekawa don tun dazu da suka yi baram baram ta fita bata sake komawa dakin ba sai yanzu, ganin yanda Hajja tayi tagumi ya sa ta karasa ciki da sauri tace "Lafiya yaya da wannan uban tagumin? Naga jikin Ammin ai da sauki daga can ma nake yanzu haka har muka ɗan yi hira da ita, dake Meran na jikinta in gaya maki kamar ba ita bace ke kwance tun safe rai a hannun Allah, anya akwai shegen da zai iya raba Ammi da Meran nan kuwa naga wani azababben soyayya take mata, ba don ba don yarinya bace Meran ai da sai ince asiri ta ma Ammin" Hajja ta sauke ajiyar zuciya tace "Ladi ba nace maki haka kawai su Nura baza su ki zuwa daurin auren Mahir ba??" Mama Ladi tace "Wanene kuma Nura?" Hajja tace "Kanin mahaifin Badiyya mana wanda take wajensa a Bichi" Ladi tace "Aiho wnn guntun me hanci wargajeje dai da na sani?" Hajja tace "Ashe wai Badiyya zuwa tayi ta ce ma dangin mahaifin nata wai an daga bikin gaba daya sai zuwa bayan karamar sallah" Mama Ladi ta saki salati tana tafe hannu tace "Amma yarinyar nan anyi tantiriyar er iska" Hajja tace "Haba Ladi ki daina zaginta don Allah, shiriya za mu yi ta nema mata kawai, to na kasa hakuri yanzu na sa aka kira min lambarsa inji dalilin rashin zuwansa daurin aure sai yake sanar min gashi gashi abinda Badiyya tace masu ai, nayi salati hankalina ya tashi ainun, ban boye masa ba nan na labarta masa duk abinda ke faruwa da abinda ake zargin yarinyar nan taje ta aikata mana, yanzu gobe yace min da safe zai dauko Badiyyar su zo nan har da Garba yayansa" Mama Ladi ta saki baki da karfi tace "Wani zargi?? abinda kowa ya tabbata ya kuma shaida ita ce ta aikata wannan abu zaki ce zargi, wllh ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba Badiyya ce ta aikata wannan zunubin, kuma gwara su taso keyarta ayi ta ta kare" a fusace Hajja tace "Gaskiya Ladi idan baza ki dinga yayyafa ma lamari ruwan sanyi ba to ki dinga jan bakinki kiyi shiru, ke duk wani fitina kin san yanda zaki tada shi a rayuwar nan?" Mama Ladi ta kyabe baki ta nemi waje ta zauna, Hajja tace "Sannan ni tsakani da Allah fargaban zuwansu da ita nake, kowa dai yasan yanda Usman da Maheer suka kullaceta abun ba kyau, kuma kinsan Usman dama tun asali ya tsaneta kada a zo da ita ya illata er mutane mu shiga uku...." Mama Ladi ta mike tsaye da sauri tace "Kin gan ki ko? To me kike nufi a takaice? A kyaleta a zuba mata ido kada a hukuntata kenan ta ci bulus?" Hajja