Sashe 186
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
kawo" MD yace "Till then" Khalil yace "Don Allah kafin su Madam su shigo kasar nan ka bata aikin nan, kasan in suna nan it will be hard wllh" MD yace "Ka ma maida ni ban san abinda nake ba Khalil, ta yaya zan bada aiki babu CV?" Khalil yace "Ko Hafsat ba sai daga baya aka kawo ba, kuma me wuyar dama mutum yayi graduating ko" MD yace "Don Allah lokacin kwanciya na yayi, in dai yarinyar nan ne bazan bata aiki babu takardu ba, apart of takardu sai nayi interviewing dinta, kuma idan naga she is not fit for the job Billah sai dai kayi hakuri bazan bata ba kaji har na rantse, even after the interview idan tayi passing kenan she will be starting as an Enrolled nurse" Khalil yayi shiru yana kallonsa, can a hankali yace "Enrolled nurse kuma MD" MD ya fara tarkata textbooks dinsa da nufin barin parlon, Khalil ya sauke ajiyar zuciya yace "Toh shikenan ba matsala, amma a fara interview din tukunna pls" MD yace "Then she should come together with an apology letter in 2 days time, gobe bani da lokacinta haka ma jibi, sai ta bari on Sunday kenan idan Allah ya sa na shiga Asibitin" Yana gama fadin haka yace "I will be going to Bed Khalil" Khalil ya ɗan yi murmushi ya mike yace "To shikenan, thank you sir, Allah ya tashe mu lafiya" Daga haka ya bar parlon. Maheer dake zaune dakin Usman sai kallonsa yake har ya rufe hand luggage dinsa, can Maheer yace "When did u see the debit alert?" Ba tare da Usman ya kallesa ba yace "Not long ago" Maheer yace "To yanzu ina za ka?" Usman yace "I contacted my account officer ya sanar min a Abuja ta cire kudin" Da mugun mamaki Maheer yace "Abuja?" Usman dai bai ce masa komai ba, Maheer yace "Yanzu Abujan zaka tafi da daddaren nan?" Usman yace "Yeah" Maheer yace "But... Ta yaya za ka fara tracing nata a garin Abuja that is wide??" Usman yace "Watch and see, i have been waiting for this day dama" Maheer ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, tun da Usman ya kirasa ya sanar masa Mayraah ta cire kudi a account dinsa yaji wani kwanciyar hankali ya zo masa don the silence is too much, shirun ne yasa duk hankalinsa ya tashi, but tunda har ta cire kudi ya nuna she is fine and doing well kilan kudin account dinta ya kare kenan, Maheer yace "But ya kamata ka fara zuwa gidan Hajja ka dubata har yanzu she is not saying anything, she is really shock" Usman ya kallesa yace "Wani abu ya faru ne da zan je dubata?" Buda baki Maheer yayi yana kallonsa don sarai yasan abinda ke faruwa duk commotion din nan da aka yi throughout yau yana sane amma yaki tofa nasa, Maheer ya mike ya dafa shoulder dinsa yace "Saboda Ammi zaka yi Usman, ni ma ba don Ammi ba i won't involve my self in this, yanzu haka can zan tafi, kayi hakuri mu je tare" Usman bai ce masa komai ba suka fita gidan a tare. Maheer ne ya fara shiga parlon Hajja da sallama Usman na biye da shi a baya, Hajja na kwance an sa mata drip sai bin kowa take da ido tana numfashi sama sama, Mama Ladi na gefenta sai fifita take mata ta tsuke baki, Ammi da idanuwanta yayi jajir ita ma tana zaune kasa har a sannan bata daina kukan da take ba, Aunty Mariya dai tayi tagumi, Abba ma na zaune parlon don ko minti biyar bai yi da shigowa ba su Maheer suka zo, Maheer ya karasa kusa da Hajja yana dubata, Mama Ladi ta fashe da kuka tace "Mashir ni dai da kawai a tafi asibiti a duba min er uwa da kyau, naga kamar karkacewa bakin nata yake kokarin yi, ita kenan gareni a rayuwar nan fa ka rufa min asiri mu tafi asibiti" Maheer yace "Ko mun je asibitin abin nan da nake shi za a mata, in sha Allah zata samu sauki" Shi dai Usman na tsaye bakin kofa, Abba ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Ammi for the first time yace "Ina Badiyyar?" Mama Ladi tace "Er iskar na daki in gaya maka Mamuda, wa ma zai bi ta kanta muna kokarin ceton ran er uwata wallahi ko sanin halin da take ciki bamu yi ba yanzu haka, kawai yanzu tunda zaratan mazan nan sun shigo kamata yayi su risketa a dakin da duka ta fadi uban da yayi mata ciki duk mu ji, tun dazu nake ce ma Ammi da Mariya su shiga su tambayeta cikin waye sun ki hankalinsu na kan lafiyar uwarsu" Abba ya sunkuyar da kai yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Sai ga hawaye na sauka idon Hajja, Mama Ladi ta fashe da kuka tana goge mata hawayen da dankwali tace "Tun dazu a haka take, sai dai kawai mu ga hawaye na bin gefen idonta ni dai na shiga uku na lalace Badiyyah ta cucemu" Abba na kallon Maheer yace "Kira min ita" Maheer bai so wannan aiken na Abba ba, don shi kansa tun dazu bai sa Badiyyah a ido ba bai kuma tambayi isilinta ba ya ma zata ta gudu ta bar gidan, amma bai ma Abba musu ba ya mike ya tafi zuwa dakinta, bude kofar yayi ya shiga ya ganta kwance kasa kamar warce ta yi wata uku tana jinya da alama har yanzu ko ruwa bata samu ta kai baki ba, tana ganinsa ta rushe da kuka ta mike zaune da kyar tace "Yaya don girman Allah ka rufa min asiri ka bani magani in cire cikin nan" bata rufe baki ba ya sauke mata lafiyayyen mari yayi ball da ita yace "Ni kike ce ma in baki magani ki cire ciki?" Bude kofar yayi fuskarsa a murtuke yana nuna mata waje yace "Fita ki je ki gaya masu who is responsible kar in kakkarya ki" Jikinta na rawa ta fara rarrafe zuwa bakin kofar don ko tashi bazata iya ba, rakubewa tayi jikin pillar dake corridor din tana kallon mutanen parlon hawaye na sauka idonta, Abba da Mama Ladi sai Usman kawai ke kallonta, don Ammi kauda kai tayi haka ma Aunty Mariya da zuciyarta ke tafarfasa, Mama Ladi na nunata da yatsa tayi mitsi mitsi da ido tace "Allah ya isa tsakaninmu da ke Badiyyah, kaf zuri'a ba a taɓa dauko mana abun kunya ba sai a kanki, Allah ya isa bamu yafe ba, yanzu da wani ido za mu kalli yan ubanmu?" Sai kuma ta rushe da matsanancin kuka tace "Ba don mun zama daya da Mamudan ba shi kansa da wani ido za mu kallesa wannan abun kunya haka a pamily dinmu" Abba na kallon Badiyyah calmly yace "Who is responsible?" Ta kara makalewa jikin pillar tana zazzare ido kamar me nazarin abinda zata ce, Abba ya sake jefo mata tambayar still looking at her, ta daga kai a hankali ta kalli Maheer.