← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 306 OF 313

Sashe 306

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

babu wanda zai canza mata ra'ayi" Abba yace "Better, Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi gare mu baki daya... Da can ba Musharraf din muka yarje mata ta aura ba banda ƙaddarar da ta gifta, so now also we should support her, yaron nan ba laifinsa bane, Ko ke a shekarun baya kin taɓa tunanin hada auren Mayraah da daya daga cikin yaranki?" Ammi ta ɗan yi murmushin karfin hali ta girgiza masa kai tace "Ban taɓa ba gaskiya, don a sannan they are all same a cikin zuciyata" Abba yace "Ohh yanzu they are not same kenan?" Ta fashe da kuka tana kallonsa tace "This i never bargained for, yanzu ba ni daya ke da Mayraah ba i have to accept that, an riga da an dasa min a rai cewar rikonta kawai nayi ban haifeta ba wanda a baya ban taɓa mata kallon warce nake riko ba, a yanzu ba tawa bace ita ni kadai, Gradually kuma zata koma gun righful owner dinta, ni da ita dama sai dai hange daga nesa" Abba yace "Ke kike ganin haka har ya tsaya maki a rai" Ammi bata sake ce masa komai ba ta mike tana goge idonta ta fita daga parlon Abba ya bi ta da kallo yana jin tausayinta har ransa... Aunty Mariya na zaune dakin Usman tana kallonsa tace "Don girman Allah ka ajiye wannan laptop din magana nake maka Barrister" Ya mayar da laptop din gefe yace "Aunty na fa ce maki let leave Mayraah, i don't want it to look like mu muka canza mata ra'ayi muka sa ta yin abinda bata yi niyya ba a ranta, let just pray this is just the best, Mayraah is not a kid, kuma da Ammi ta saka a rai cewar tana aure zata mata nisa dama ai shi aure babu inda baya kai mutum, ya kai mutum kasar waje ma balle just within Nigeria, i believe Mimi bazata mance halacci ba that is just it, at the end of the day ma ni sai nayi regretting me yasa nayi mata maganar da kika ce, even the Dr da na samesa da maganar maida ni clown yayi a compound" Aunty Mariya tace "Clown as in how?" Usman na kallonta yace "He isn't taking me or the issue serious, kamar it's funny to him wai taya don Mayraah tayi aure far away zata mance Ammi, daga karshe kuma yace min shi bai ma kawo wannan tunanin a rai ba, kinga ni da ke ne kawai muka kawo hakan a rai, shi yasa kawai naga mu bar ta with her choice, mun ma yi magana da Abba shi ma yace min haka...." Aunty Mariya tace "To ai shikenan, Allah ya sa hakan shine mafi Alkhairi gare mu baki daya" Yace "Ameen, ai Musharraf din na sonta har yanzu, ita ma haka, that is the most important of all" Jawo laptop dinsa yayi ya ci gaba da abinda yake, Aunty Mariya ta mike ta nufi kofa ta fita daga dakin ta kullo masa kofar. Washegari tun sassafe Aunty Mariya da Ammi da Bilkisu suka shiga kitchen domin fara girkin varieties na abincin da za su tari grandparent din Mayraah da shi, Mama Ladi na zaune kan kujeran dinning a bakin kofar kitchen din tace "Ai in kun kula tun jiya wasan er buya take da ni a gidan...." Aunty Mariya ta juya tana kallonta tace "Don girman Allah ki rufa mana asiri da wannan maganar da yaki ci yaki cinyewa tun jiya Mama Ladi, kuma ni wallahi tallahi nasan ba haka bane kece kilan dai kika juya lamarin a haka" Mama Ladi ta saki baki tana kallonta, can tace "Toh ki hutasshe da kanki ki ce min Ladi makaryaciya mana Mariya" Aunty Mariya dai ta ci gaba da abinda take, kilan in ba haka ta ma Mama Ladi ba wannan magana bazai taɓa mutuwa ba har Abba sai ta iya cewa zata gaya masa, don dai babu yanda za su yi da ita ne amma ita wallai bata so ma ace tana gidan Grandparent din Mayraah da iyayenta za su zo ba kar taje ta kunyata mutane kawai, Mama Ladi tace "Mutuniyar banza kawai da na haihu ai 'ya yana baza su zuba maki ido kina min wannan fitsara haka ba, ko da yake kema din dai gashi har yau shiru shekara sha uku da aure, haka nan lokacin bikin Mashir kika ce a koreni ga Ladin kauye ta zo biki...." Sai kuma ta fashe da kuka, Ammi ta kalli Bilkisu tace "Bilki kije in da wani abu zan kira ki" Bilkisu tace "To Hajiya" Daga haka ta fita daga kitchen din, Ammi ta kalli Mama Ladi cikin kwantar da murya tace "Don Allah kiyi hakuri ki rabu da Mariya Mama Ladi, baki ma tambayi wasu baƙin za mu yi ba yau muke ta girke girke" Mama Ladi tace "Yo shawara ku ke da ni da zan tambayi wasu baƙi za ayi ku gwaleni, kawai don ni Allah bai taɓa bani haihuwa ba sai in zama banza a gidan duniya...." Ammi na ɗan murmushi tace "Haba Mama Ladi, ai ke uwar mu ce halaq malaq, To iyayen Mayraah ne za su zo yau, dama so nayi ki ga hakan a ba zata shi sa nake ta boye maki" Mama Ladi ta saki baki tace "Iyayen Mera kuma? Su waye iyayen Mera da na sani banda ku?" A hankali Ammi tace "Iyayenta na asali da suka haifeta, dalilin tafiyar mu kaduna kenan satin da ya wuce, dama cewa nayi kawai sai dai mu yi ma Mama Ladi ba zata" Mama Ladi tace "Ni ai kin rikita ni, iyayenta da suka ya da ita cikin kwata a kwali ko kuma wasu iyayen kike nufi?" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Bari in maki bayani yanda za ki fahimta Mama" Nan Ammi ta fara dauko ma Mama Ladi bayani tiryan tiryan sai dai yawanci duk kwaskwarima tayi ma labarin don bata gaya mata Ceo ba musulma bace, sannan bata gaya mata Ceo bace ta yada Mayraah ta dai ce wata makiyiyarsu ce a gidan tayi hakan saboda tana jin haushin Aaria, sannan still ta boye yanda Abdallah ya auri Aaria cikin sirri don iyayensa where against the marriage, bata kuma gaya mata dangantakar Mayraah da Musharraf ba don kar ma labarin yayi tsayi, haka dai tayi fabricating labarin yanda Mama Ladi bazata samu abun fade ba na har abada, Mama Ladi da ta mike tsaye ta dinga salati tana tsine ma matar da ta yasar da Mayraah, Aunty Mariya dai aikinta kawai take ta yi, Ammi tace "Kakanta sananne ne a kasar nan ma" Mama Ladi ta zaro ido tace "Waye shi?" Nan Ammi ta gaya mata sunansa, Mama Ladi ta saki sabon salati tace "Yo ai na sha zuwa kofar gidansa a Adamawa in amso abincin sadaka in kai gida wajen Hajja, don wallahi wani lokacin sai naje na bi layin karban sadaka muke samun abincin da za mu ci ku duk baku wani girma ba, kinsan babanku sai yayi tafiyarsa ya kwashe wata da watanni bamu gansa ba, haka za muyi ta wahala, sannan shi kakan nata wajen ubansa ya gaji uban dukiyar nan tasa har yayi Gwamna a Adamawa, Innalillahi wa inna ilaihi raji'una yanzu daga wannan tsatsson Mayraah ta fito?? Mahaukacin kudi fa gare kakanta ban dai san uban nata ba, matar kakar tana nan ana ce mata Hajiya Ramatu mata me kirki da faram faram da jama'a, duk sai ta tabbatar mun samu abincin sadaka a wancan lokacin in mun bi layi, kuma ai ɗanta daya tak a duniya bata sake haihuwa ba bayan shi, to ban dai san ko Alhaji Saminun ya kara wani auren ba ko uba Meran ɗan kishiyarta ne" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Wannan ɗan nasa guda dai shi ne mahaifin Mayraah" Mama Ladi ta koma ta zauna tana gwale ido tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ita Meran? Yau mun shiga uku mun lalace Allah ya so bamu taɓa cutarta ba" Ammi bata sake ce mata komai ba ta ci gaba da aikinta ta bar ta tana ta salallami. Karfe goma Mayraah ta fito daga dakinta, tun da gari ya waye bayan ta gaida su Ammi ta koma daki bata sake fitowa ba, Breakfast ma Bilkisu ce ta kai mata, downstairs ta sauko tana tafiya a hankali, tana hango Mama Ladi zaune bakin kofar shiga kitchen duk ta cika muryarta a parlorn, ta juya da sauri tun kan ta ganta ta koma sama tana zaro ido, sai kuma ta nufi bangaren Ammi, ta bude kofar gently tana leka cikin Parlon, Maheer ne zaune da pepper soup a gabansa da bai fara ci ba, suna hada ido ta juya ta bar wajen ta koma jikin bango ta tsaya, shi dai ya ci gaba da danna wayarsa, har ta fara tafiya sai kuma ta tsaya, ta juyo a hankali ta koma bakin kofar parlon tana makale jikin kofa without looking at him tace "Yaya ina kwana" Shi ma bai kalleta ba yace "Lafiya lau, sai yanzu kika tashi kenan" Sunkuyar da kanta tayi ta karasa ta zauna kasan carpet ɗan nesa da shi tace "Aa" Bai sake cewa komai ba, ita ma tayi shiru, bayan wani lokaci tace "Baka je aiki ba?" Yace "Sai da yamma" Tace "Ohk" Mikewa tayi tana tafiya a hankali ta nufi kofa ta fita sannan ta kullo kofar. Karfe sha daya da rabi su Alhaji Saminu suka iso gidan Abba, kuma kusan tare ma suka iso gidan da Ceo da Aaria, Mayraah dai na kwance dakinta bata ma san duk sun iso ba, gaba daya ta rasa me ke mata dadi ga shi sai faduwa gabanta ke yi wanda ta kasa gane dalilin hakan, Bude kofar dakinta aka yi ta mike zaune da sauri tana kallon kofar, Usman ne ya shigo dakin ta dinga kallonsa har ya karaso yana kallonta yace "Me yasa kika makale a daki tun safe, ko saboda Mama Ladi?" Tayi murmushin karfin hali ta sunkuyar da kanta tace "Aa, bacci nayi na tashi" Yace "Hope you've taken ur bath?" Ta gyada masa kai yace "Our visitors are around" Sosai gabanta yayi mugun faduwa ta daga kai da sauri tana kallonsa....
Chapter 306 · 0% Book details