← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 161 OF 313

Sashe 161

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake. Da sauri Mayraah ta dauke kanta kafin ya kalli direction din da take tsaye ta bar wajen ta koma wani section din mall din gabanta na faduwa tana zare ido, wani lecturer dinta ne Dr Nasir which is a very good frnd of Musharraf don su biyu kadai ne young Dr's din department din nasu as at then, farko da Musharraf ya fara sonta yayi discussing hakan da Dr Nasir din ne, yawanci sai Dr Nasir ya kira ta office din sa as if zai yi mata tambaya ko kuma ya ce zai tura mata Pdf na handout in kuma taje office din tare zata gansa da Musharraf da baya ce mata komai a lokacin, nan kuma shi yake sa Dr Nasir din ya kirata office din kawai don ya ganta, that was 2 years back don tuni Dr Nasir ya bar department din nasu yana Uni Abuja yanzu, Mayraah duk ta rikice ta fara tunanin yanda zata bi ta maida kayan da ta zuba a karamin shopping cart dake hannunta don tana tsoron kar ace taje wajen biya su hadu da shi a can, da ta sani da ta fito da nose mask, cikin dubara ta ɗan sake leka section din da Dr Nasir din yake taga yana tahowa, da mugun sauri ta juya zata bar wajen ta ci karo da wata mata rungume da babynta, zaro ido Mayraah tayi tana kallonta ganin alamar bahaushiya ce matar tace "Don Allah kiyi hakuri...." Matar tayi mata murmushi tace "Ba komai" Ko rufe baki matar bata gama yi ba Mayraah taga Dr Khalil bayan matar rike da wata babyn mai kama da warce matar ta rike alamar dai yan biyu ne, Dr Khalil ya ɗan buda ido alamar yana son tuna sunanta yace "How are you" Matar ta juya ta kallesa, ita dai Mayraah duk a rikice take kar Dr Nasir ya zagayo ya ganta, kamar mara gaskiya tace "Ina yini" Dr Khalil yace "Lafiya lau ya jikin, hope kin ji sauki gaba daya yanzu?" Mayraah tayi saurin gyada masa kai, Dr Khalil ya kalli matarsa yace "Patient dita ce, dazu muka sallameta a asibiti" Matar na kallon Mayraah tace "Allah sarki, Allah ya kara lafiya" Mayraah na murmushin karfin hali tace "Ameen Nagode" Dr Khalil ya lura da how tensed Mayraah is don ta kasa tsaye waje daya kamar mara gaskiya, matarsa na kallon Mayraah tace "To sai anjima" Mayraah ta gyada mata kai da sauri ta bar wajen, Dr Khalil suka wuce tare da matar sa, wani ajiyar zuciya Mayraah ta sauke batan ta hango Dr Nasir can bakin entrance din mall din zai fita da sauri yana waya kuma babu komai hannunsa alamar kilan ya fasa siyayyan, har dai taga fitar sa, gaba daya sai ta dawo uncomfortable a mall din don gani take kamar zata sake haduwa da wani wanda ta sani, da kamar ta fasa siyayyan kawai ta koma hotel dinta sai kuma ta tuna ba fa ta da mai da zata shafa gobe, kuma har pad tana son siya with few junk food don ba ko da yaushe take jin cin abinci ba, kamar mara gaskiya haka ta dinga shopping din nata being very cautious, duk inda kuma taga alamar za su hadu da Dr khalil da matarsa sai tayi maza ta canza route dinta har dai ta gama picking few things da take bukata sannan ta nufi counter inda zata biya, tana hango Dr Khalil da wife dinsa tsaye wajen su ma sun gama siyayya sai taki biyan kudin kayan nata a nan, ta koma next counter din, Dr Khalil na gama biyan kudin abubuwan da suka siya, dai dai sanda aka zo kan Mayraah dake daya side din, tana kokarin bude handbag dinta ta ciro Atm card dinta ya mika ma mutumin Atm card dinsa da turanci ya ce masa ya cire kudin, Mayraah ta daga kai ta kallesa da sauri tace "Aa Dr kar ka damu, i will pay" Dr Khalil yace "Ai na riga ma basa card din...." Mayraah ta kalli matarsa dake kallonta, hakan yasa matar ta sakar mata murmushin karfin hali, Mayraah ta mayar mata da murmushin tace "To Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi" Tuni aka yi ma Mayraah packaging few abubuwan da ta siya ta amshi ledan, matar kadai tayi ma sallama ta fita daga mall din don su kayansu da yawa ba a gama masu packaging ba, Zainab ta kalli mijin nata tace "Kai kowa dai patient dinka ne Dr" Yayi murmushi yace "Amma kamar patient yan matan sun fi tsaya maki ko...." Tace "Not at all nasan halin ka ai, and i trust u" Yace "Double that trust girlfriend" Tayi murmushi tana kara rungume daughter dinta dake bacci. Washegari karfe goma saura Mayraah ta fito daga hotel room dinta bayan sun gaisa da ma'aikatan wajen ta fita ta tari adaidaita sahu tace masa tasha zai kai ta, ya tambayeta wani tashar, nan ta hau kalle kalle don bata san ma sunan tashar da aka sauketa shekaranjiya ba, can dai ta shiga tana kallonsa tace "Kai ni ko wanne" a traffic ta siya nose mask ta saka don bata son taking risk yau, luckily kuwa mai adaidaitan ya kai ta tashar da aka sauketa Shekaranjiya, ta sauka ta basa kudinsa sannan ta karasa shagon mai pos din ranan, yana ganinta ya gane ta, bayan sun gaisa yace "Har ina tunanin kilan kin samu gidan ne da na ji ki shiru" Mayraah ta ɗan yi murmushi ta zauna kan kujera tace "Aa ban samu ba, jiya ban ji dadi bane shi yasa baka gan ni ba" Yace "Allah sarki, Allah ya sauwake" Tace "Ameen, ka duba min gidan kuwa don Allah?" Yace "Kwarai kuwa an bincika har an samu biyu, duk wanda yayi maki a ciki shi za ki zaba" Tace "To ba damuwa, kuma nawa ne sai in tura kudin?" Yace "Toh Hajiya yanzu dai kowa yasan yanda duniya ya dawo babu gaskiya, daga haduwa da ni ba haka nan zaki yarda dani har ki bani dukiyarki ba duk da dai kowa yasan nan ne wajen neman abinci na, amma abinda ya kamata yanzu kawai zuwa can sulejan za mu yi tare da ke, bayan kin duba gidan kin ga wanda yayi maki sai ki bada kudin a baki makullin gidan" Mayraah tace "Aa ni kam ba sai naje ba, kar ka damu kawai a zabar min duk wanda aka ga yafi, but pls ya kasance da ruwa kuma da wuta a anguwan" Yace "Ai kar ki ji komai Hajiya ni ma bazan kai ki anguwan da zaki jigata ba don naga baki yi kalar wahala ba, wuta har sai kin gaji da shi, sannan babu matsalar ruwa gida me borehole aka duba maki" Mayraah tace "Toh nawa kudin hayan?" Yace "Toh amma ke irin gida me part part na haya kike so, ko kuma karamin self contain wanda ke kadai zaki zauna ciki?" Mayraah tace "Eh ni kadai nake so, bana son me mutane" Mutumin yace "Toh me daki daya suna bada shi akan naira dubu dari biyu da hamsin har agreement, in kuma daki biyu kike so har dari uku da hamsin ana bayar wa, dari hudu dai a takaice in da agreement, tsakar gidan ma zaki gansa ba lefi mota daya zata shiga ta zauna lafiya lau" a hankali Mayraah tace "To duk wanda dai aka samu ba damuwa" Yace "Amma fa gaskiya me daki biyun nan deal ne Hajiya, in dai da kudin kawai ki rufe ido ki amshe sa don anguwa ce me kyau akwai kuma jama'a kintsatsu ba laifi" Mayraah tace "To shikenan, a ina za a tura kudin" Yace "Ki saka a account dina don cash zan kai masu kar a zo ana dogon zance" Mika masa Atm card dinta tayi, don kudin ciki zai kusa 1.3 tunda babu abinda take da kudi ko Abba ya tura mata sai dai yayi ta zama a account din tunda su Maheer duk wani abun bukatarta su suke siyo mata, ya amshi Atm card din hannunta ta gaya masa pin tana kallonsa tace "Ka cire dubu dari hudu da talatin, sai ka rike dubu talatin din Nagode sosai" Godiya sosai mutumin yayi mata yace "Don dai kin ki ne Hajiya da akan idonki za ayi komai na gidan, har kudin in basu a gabanki" Tayi murmushi tace "Kar ka damu, don Allah ina zan samu sim card in siya?" Yace "Ai ina siyarwa" Ta ɗan yi shiru don tasan su suke ma layin register da kansu, can dai tace "Toh bani daya" bayan ya cire kudin ya mayar mata da Atm card dinga sannan ya dauko sabon layi ya mika mata ta amsa tace "Nawa ne?" Yace "Aa ki bar sa, ai ba tsada" tace "Toh nagode, sannan don Allah a can garin ana samun gado ko da ba babba ba?" Yace "Gado? Ko dai katifa irin ta yan makaranta?" Ta gyada kai tace "Shi" yace "Gaskiya can zai yi tsada, kyau a siya daga nan a kai can din kawai" Mayraah tace "Toh, zan tafi yanzu, ka bani numberka anjima idan na saka layin zan kira ka inji yanda ake ciki" Yace "Toh Hajiya" Ya rubuta mata number ta amsa sannan tayi masa sallama ta bar shagon, sai da ta fara biyawa wani karamin eatry ta siya snack sannan ta koma hotel din da take. Mayraah na gama cin meatpie din ta dau magungunanta ta tasha sannan ta kwanta tayi bacci. Bata tashi ba sai can kusan yamma, dauko wayarta tayi ta saka sabon sim card din taga layin ya hau, sai dab da magrib ta kira me pos din, bayan sun gaisa yace mata an biya kudin gidan, tace "To shikenan nagode" Yace "Ko gobe kika ce zaki tare in dai da abubuwan da zaki zuba a gidan ba matsala don sabon waje ne ba
Chapter 161 · 0% Book details