Sashe 260
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
sannan Musharraf ya juya ya kallesa, Mami na kallon MD tace "I heard she was poisoned?" Gyada kai kawai MD yayi bai iya yace komai ba, Mami tace "Allah sarki, yarinyar nan na ganin jarabawa iri iri" Sai kuma da mamaki Mami tace "Wait... Amma ai da kai aka kai kudin auren nata Daddy ko ka manta ne? Ai zaka gane yayyinta maza da ma Abban nata...." Girgiza kai kawai MD that was speechless and confuse yayi yana kallon Mami amma ya ma kasa magana, Mami bata sake ce masa komai ba cause she can see he is tired don taga hakan a idonsa, bayan few seconds ya lumshe ido kansa na jingine da kujera zuciyarsa na ci gaba da bugawa, Musharraf ya dau can drink din gabansa ya bude ya fara sha, Mami kuma ta dau bottle water ta bude, Lkci daya MD ya bude ido bayan kusan minti biyu jin wayarsa na vibrate, yana dubawa ya ga Ceo ce ke kiransa, gaba daya yaji kamar an zare masa laka ne a jikinsa, Musharraf ya mike bayan ya kusa shanye drink din Mami na kallonsa tace "Zaka koma ward din ne?" Yace "I want to get something for her outside first" Mami tace "Ohk, amma kasan Flight dina na komawa Kano bayan magrib ne zaka yi using motar Daddy kayi dropping dina airport nan da minti talatin" Musharraf yace "Toh" Kallon MD da ke ta kallon kiran ceo yayi, gaba daya he is absentminded don hankalinsa ma baya kan kiran kawai kallon screen din yake babu ko kiftawa tunaninsa na wani wajen daban, Musharraf ya karasa kusa da shi yace "Zan yi amfani da motar ka" Sae a nan MD ya dawo duniyar tunanin da ya tafi ya daga kai da sauri ya kallesa, sai kuma ya daga kiran Ceo kafin ya katse, sanar masa tayi ta shigo asibitin tana office he should meet her, bayan sun gama magana MD ya katse wayar ya dauko makullin motarsa ya mika ma Musharraf ba tare da ya kallesa ba, Musharraf ya amsa ya nufi kofa, Mami dake ta kallon MD tace "Daddy are you sure you're okay?" Ya mike da sauri yana feigning smile yace "Mami na gaji ne fa, bari in je our Ceo is around ita ta kirani yanzu" Mami tace "Ohk" Yana tafiya a hankali ya fita daga office din. Har ya isa Office din Ceo hankalinsa baya jikinsa, ya sameta tana waya, ya sunkuyar da kai ya jira har ta gama, sannan yayi mata sannu da zuwa da ladabi, ta ajiye wayar hannunta tana kallonsa daga sama har kasa tace "Are you okay?" Ya gyada kai yana kirkiran murmushi yace "Sure Ma'am" Takarda ta dauka kan table dinta tayi rubuce rubuce sannan ta mika amsa tace "Magunguna da alluran da za a canza ma Mary Ann kenan, it should start from tomorrow morning pls" Ya amsa yace "Ok Ma'am" Tana kallonsa, bayan few seconds tace "You said the result will be ready today Aliyu" Yace "Sure Ma'am it's out, yana office dina ma..." Shiru tayi tana kallonsa, shi dai yana tsaye yana jiran next instruction da zata bada, Ajiye pen din hannunta tayi a hankali tace "Bring it to me" Yace "Alright Ma" Daga haka ya juya ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita. MD na komawa office dinsa ya zauna with confusion yana kallon Mami, calmly yace "But Mami ita wannan ai da iyayenta fa, har ma da yayyinta maza, warcen kuma ba cewa aka yi bata da iyaye bata da asali ba? Sannan ita wannan a nan Abuja suke zama...." Mami da ta ma rasa abinda zata ce masa tayi shiru tana kallonsa as if wanting to figure out something, ya girgiza kai yace "Gaskiya ina jin ko kamanni ne, ko kuma, kawai dai ba yarinyar bace....." He just realized he sounds stupid and he is not making any sense, ya kara girgiza kai ya mike ya dau envelope din result din genetic testing din da Ceo ta bada ayi, kofa ya nufa Mami ta bi sa da kallon mamaki har ya fita, yana komawa office din Ceo ya ajiye mata envelope din saman table yace "Here is it Ma'am" Kallon envelope din kawai Ceo take, yace "Is there anything again Ma'am?" A hankali tace "Just wait" Yace "Ohk Ma" Gefe ya koma ya tsaya, ta dau envelope din tayi unsealing dinsa gently ta ciro result din ciki, Shi dai MD kallonta kawai yake, Glasses dinta ta dauka ta saka sannan ta warware takardun tana dubawa, MD wondered why she was this nervous checking the result, ko da yake tace family issue ne, mikewa yaga tayi da sauri ta dafe table dinta, MD ya karaso da sauri kusa da table din yace "Is everything okay Ma'am?" Sai kuma yaga hawaye na sauka idonta ta cire glasses din idonta da sauri tace "I need privacy pls Aliyu" Yana kallonta yace "Alright Ma, take care pls" Daga haka ya nufi kofa yana waigota ya ga ta nufi dakin dake office din, shi dai ya fita ya kulle kofar, jingina yayi da bango ya lumshe ido zuciyarsa na wani irin bugawa, da kyar ya iya jan kafa ya bar wajen ya koma office dinsa, yana shiga office din Mami ta mike tace "Kar nayi missing Flight dina Daddy" a hankali yace "Okay Mami, Musharraf din ya dawo ne" Tace "Eh yana waje, mu je in fara masu sallama tukunna" Bai iya yace mata komai ba, suka koma ward din da Mayraah take, Mami ta karasa kusa da gadon Mayraah tace "Allah ya sauke Mayraah" Mayraah dai ta sunkuyar da kanta, kallonta MD yake babu ko kiftawa, Mami ta ciro 50k a jakarta ta ajiye gefen Mayraah tace "A siya maki fruits" Ammi tace "Har da dawainiya Hajiya, zuwan kadai ma ai ya wadatar wallahi" Mama Ladi ta kalli Ammi da sauri tace "Kul, ba a maida hannun kyauta baya, godiya kawai za kiyi mata kice Allah ya kara arziki haka ake yi" Murmushi kawai Mami ke yi tace "Lallai kam Mama gwara dai da kika gaya mata" Cikin sanyin murya Ammi tace "To Allah ya saka da alkhairi Hajiya, mun gode kwarai da gaske, Allah ya bar zumunci" Mami tace "Ameen ya Allah, ita kuma Allah ya bata lafiya ya tsare gaba" Ammi tace "Ameen" Mayraah ta ɗan daga kai ta kalli MD da bai fasa kallonta ba suka hada ido, kauda kanta tayi da sauri, Ammi da Mama Ladi suka fita raka Mami, Usman dai sai kallon MD dake kallon Mayraah yake.