← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 263 OF 313

Sashe 263

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

da night shift ya gaida Abba da ladabi, Bayan Abba ya amsa yace "Pls Dr kayi min magana da MD wai yana nemana" Dr Khalil yace "Ohk to bari in duba ko yana office" Fita Dr Khalil yayi ya tafi office din MD, zaune ya gansa a kan office chair dinsa da cup din coffee a gabansa ya jinginar da kansa da kujeran idonsa a lumshe, yana jin an bude kofa ya bude ido a hankali, Dr Khalil ya karasa yace "Wai lafiyarka kuwa duk na ganka wani iri, in dai Mayraah ce naga fa har magana ta fara bawan Allah" MD yace "Ban gane ba" Dr Khalil yayi wani dariya yace "Dama ina ta son sai ta samu sauki in maka tambayoyin nan dake cunkushe a raina sun hanani sukuni....." MD yace "Tambayar me?" Dr Khalil na murmushi yace "Ko da yake da sauran time, ba yanzu ya kamata in maka tambayar ba" Ko kallonsa MD bai sake yi ba, ya matsar da coffee din gabansa, Dr Khalil yace "Dad dinta ne ya zo office dina wai kace kana nemansa" MD yace "Yea, bari in fara ma Ceo magana, ita ce ke nemansa" Daga haka ya mike yana tafiya a hankali Dr Khalil dai ya bi sa da kallo. Abba na zaune office din Dr Khalil MD ya shigo bayan ya gaishesa yace "Tana office dinta zaka sameta a can Sir" Abba ya mike yace "Ohk then" MD yayi leading dinsa har zuwa office din Ceo, bayan yayi knocking ya bude masa kofa, Abba ya shiga MD ya kullo kofar sannan ya bar wajen, Zaunawa Abba yayi saman kujera yana gaisheta, a hankali ta amsa, Abba yace "Ya kokari kuma? Dazu da safe nake Allah Allah in tambayi Bill dinmu sai kuma wani uzurin ya taso min naje kano, dawowata kenan aka sanar kina nemana" Ceo ta gyada kai, bata bari sun hada ido da shi ba duk da dai glass na idonta speaking calmly tace "Pls birth certificate din daughter din ka nake tambaya da garin da aka haifeta...." Abba yayi shiru yana kallonta ita dai bata bari ta hada ido da shi ba, ta dinga kauda takardun kan table dinta, Abba yace "Ai ranki shi dade wannan sai dai in tambayi me dakina, don na mance ko an mata ko ba ayi ba gaskiya...." Ceo tace "To ko zaka tambayeta sai ka dawo yanzu ina jiran ka" Abba yace "Sure, right away" Mikewa yayi ya nufi kofa ta bi sa da kallo kafin ya fita a hankali tace "Ko da ba a mata Birth certificate ba ina bukatar garin da aka haifeta, da ranan da aka haifeta, da kuma lokaci" Abba ya juya ya kalleta, shiru yayi na ɗan dakikai, sai kuma da sauri yace "Toh zan tambaye ta" Daga haka ya fita ya kulle mata kofa, mamaki ne ya cika Abba, don ya kai second talatin a tsaye bayan ya fito daga office dinta, to me kuma zata yi da birth certificate din Mayraah, ai it's something that is not necessary shi dai a tunaninsa, to ko saboda a saka a file dinta ne take tambaya, amma gaskiya shi kam bai taɓa jin asibiti sun bukaci birth certificate ba in ba dai kilan shi ne bai sani ba, a haka dai har ya isa dakin da su Mayraah suke.... Zaunawa yayi yana kallon Ammi dake lallaba Mayraah ta ci abincin da Aunty Mariya ta girka mata, yace "She is asking for her birth certificate" Ammi ta juya ta kallesa tace "Birth certificate kuma? What for?" Abba yace "Ni ma dai shine na kasa ganewa, dama idan an kwantar da mutum a asibiti ana tambayar Birth certificate dinsa ne? Ina ce iya shekarunsa ake tambaya" Mayraah dai kallonsu kawai take, Ammi ta ajiye plate din abincin hannunta bata sake cewa komai ba, Abba dake kallonta yace "Ya naga mood dinki ya canza, lafiya kuwa? is there anything wrong?" A hankali Ammi tace "To ai ban taba jin haka bane, why is she asking for her birth certificate, ita dai ba iyaka ta fadi bill dinsu mu biya su kudinsu su sallamemu mu wuce gida ba, ai jikin nata ya ma yi sauki tun da yamma kawai a sallamemu gaskiya..." Abba zai yi magana Usman ya shigo da sallama, Ammi na kallonsa da sauri tace "Usman ka taɓa jin inda aka tambayi patient birth certificate a asibiti? ba iyaka shekarunsa ake tambaya ba ko date of birth dinsa? Then why the certificate gaba daya?" Usman yace "Birth certificate kuma? Me za ayi da shi" Abba yace "To haka dai tace, har cewa tayi in ma babu birth certificate din to tana bukatar garin da aka haifeta, ranan da aka haifeta da kuma lokaci, amma bari dai Maheer ya shigo sai mu tambaye sa ko haka ake yi" Ammi tace "Aa kawai kace mata ba a taɓa mata certificate din haihuwa ba, kuma a kano aka haifeta a gida ba a asibiti ba...." Abba dai bai sake cewa komai ba. Ana kiran isha shi da Usman suka tafi masallaci, Ammi dake ta zaune ta kasa motsawa daga inda take tun maganar da Abba ya kawo mata ta juya a hankali ta kalli Mayraah, cikin sanyin murya tace "Ina ke maki ciwo yanzu kuma Mimi?" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "Yanzu dai babu ko ina Ammi, kawai dai jikina ba kwari ne har yanzu" Ammi tace "Kin gaji da zaman asibiti ko?" A hankali Mayraah ta gyada mata kai tace "Na gaji Ammi" Ammi ta bude handbag dinta ta ciro dubu biyar sannan ta mayar da jakar ta ajiye ta mike tsaye tace "Mu tafi gida kawai nasan baza su yarda su sallamemu ba sai suce sai nan da wasu kwanaki..." Daga haka ta kama hannun Mayraah ta sauko da ita daga kan gadon dama an riga an cire mata drip tun dazu da ya kare kuma ba a sake saka mata wani ba, Ammi ta dauko mata takalmanta ta ajiye mata, Tana rike da ita ta saka takalmin, sai da Mayraah ta ga wani jiri bayan ta tsaya, Ammi bata damu da hakan ba tana rike da hannunta suka nufi kofa suka fita daga ward din, suna shigowa reception ta ki kallon ko wace nurse ta nufi kofar fita, daya daga nurses din ta mike tace "Ma'am... Za ku ina?" Sai a sannan Ammi ta kalleta da sauri ta kirkiro murmushi tace "Aa za mu ɗan zaga premises din asibitin ne tayi exercise ko zata ji kwarin jikinta" Nurse din ta koma ta zauna tace "Ohk Ma" Daga haka Ammi ta fita rike da Mayraah, direct gate suka nufa Ammi na waige waige har suka fita daga asibitin gaba daya, da kyar Mayraah ke tafiya don har strength dinta ya kare, Ammi dai na rungume da ita a jikinta har suka iso bakin titi ta tsayar masu da adaidaita sahu suka shiga ta gaya masa inda zai kai su.
Chapter 263 · 0% Book details