← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 188 OF 313

Sashe 188

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake.* Maheer ya wani hade rai ya daka mata tsawa yace "Baza ki bude baki kiyi magana ba kina bata ma mutane lokaci" Ta fashe da kuka a hankali tace "Wallahi Haseenah ce ta hada ni da shi ni ban san shi ba" Daga Ammi har Aunty Mariya basu san sanda suka juya da sauri suna kallon Badiyyah ba, Mama Ladi da ta gwalo ido tace "Wacece haka? Sunan fa matar Mashir naji ta kira ko dai kunnena ne jama'a? Sanisa dai da duka muka sani?" Cikin kuka Badiyyah tace "Wallahi ita ce ta hada mu, Malaminta ne shi yake mata aiki a Zaria" Salati Mama Ladi ta saki bayan ta ajiye maficin hannunta tana tafe hannu cikin kidimewa tace "Malaminta kuma?" Maheer kam kallon Badiyya kawai yake babu ko kiftawa kamar yanda Abba da Usman dake tsaye bakin kofa ma suke kallonta, Cikin rawan murya Badiyyah tace "Dama bayan an fasa auren Mayraah nace mata ina son Musharraf din ya dinga kulani, shine ta hadani da malamin wai ya iya aiki, shikenan mu ka fara waya da shi na fara tura masa dubu hamsin sai watarana yace in je Zaria zan amshi wasu turarruka da zan dinga amfani da shi, ni kuma sai nayi ma Hajja karya zan je Bichi sai na tafi Zaria wajensa" Tana kai wa nan ta kara rushewa da kuka, Mama Ladi dake ta zare ido tace "Sai aka yi yaya?" Cikin kuka sosai Badiyyah tace "Wallahi ni ban taɓa iskanci ba Haseenah ce ta hadamu da shi, kuma yace min shi ne ma yayi mata aiki har ta auri Ya Maheer, sannan ya bata asiri da ta kai dakin Ammi wai don Ammi taji ta tsani Mayraah, ita ma kuma ai tana zuwa wajensa a zaria sai da tayi aure ne ta daina zuwa wajen sa" Mikewa Mama Ladi tayi ta dafe gwiwa tana kallon Hajja da hawaye ke sauka ta gefen idonta tace "To Allah ya sa dai kunnuwanki basu samu matsala ba kina jin duk abinda marainiyar ki ke cewa, mu dai sai dai mu ce Allah ya isa lalata mana zuri'a da za ayi da shege, yau ga dai Badiyyah da cikin boka" Sai kuma ta fashe da matsanancin kuka ta rike kanta, Ammi ma kukan take sosai wani bakin ciki da takaici na taso mata a zuciya, ita dai Aunty Mariya shock ya sa ko motsi ta kasa yi a inda take zaune sai kallon Badiyyah take, shi kansa Abba kallon Badiyyah kawai yake ko kiftawa babu, can ya girgiza kai ya mike kawai ya fita daga parlon, Usman ya juya ya bi bayansa, Maheer ya kusa minti biyar tsaye parlon da tunani iri iri a ransa, can ya nufi kofa ya fita shi ma, Ammi ta mike ta bi bayansa da sauri har a sannan tana kukan takaici, tsayawa yayi har ta karaso inda yake cikin rawan murya tace "Yanzu Maheer ta yaya za ayi a cire cikin nan? Ya za mu yi yanzu ya fita Maheer?" Da mamaki Maheer ke kallonta yace "A cire fa kika ce Ammi?" Ta fashe da kuka tace "To me zance Maheer? da wani ido za mu kalli duniya? Wannan abun kunyar har ina Maheer? Badiyyah ta cuce mu, ta cuce mu wllh" Maheer ya girgiza kai yace "Ai in ma wani ya kawo shawaran a cire cikin ke me hanawa ne Ammi" Muryar Mama Ladi suka ji da karfi tana cewa "Ashe baki da kai Ammi? Ina maki kallon me ilimi ashe ba haka bane? Wani cikin za a cire? So kike Allah yayi fushi da kaf zuri'ar mu? Ga laifin zina sannan ga na zubar da ciki, to wallahi babu ruwana sai inyi ta kaina in fita daga zuri'ar nan in shiga duniya kamar yanda Mera tayi, babu zunubin shegiyar da zai shafeni ban ji ba ban gani ba, ai tunda taje ta yo cikin dole sai ta haifesa a ba Hajja ko kuma a baki ku yi raino don nasan Mariya bazata amsa ba, ni ma kuma ba ruwana wallahi, da ana canza ma tuwo suna wallahi a yau din nan da na canza pamily bakina alekum na koma wani pamilyn, yanzu zancen da nake maki wllh kunyan Mamuda nake ji tun dazu na kasa hada ido da shi" Ammi dai kuka take ta kasa cewa komai ta nemi dakali ta zauna, Maheer ya fita daga tsakar gidan kawai, a kofar gida ya tadda Abba tsaye alamar dai lamarin nan ya girgiza sa ba kadan ba, shi dai Usman na tsaye jikin gate din gidan har sannan bai ce komai ba, shi fa bai yi mamaki ba ko kadan yasan akwai ranan da za a zo wanna gaɓar in har Hajja ta ci gaba da biye Badiyyah to gashi nan kuwa an zo, Abba na kallon Maheer bayan ya fito yace "I won't decide for you Maheer, duk hukuncin da kaga ya kwanta maka a zuciya game da matarka zaka iya yankewa but... Ka tabbatar baza kayi hakan ba sai kana da kwakkwaran hujjoji da zaka gabatar ma danginta don Badiyyah ba abun yarda bace, a yau na gama sarewa da lamarinta sannan na zame hannu a duk wani abu da ya shafe ta babu ruwana, sannan zan gaya ma mahaifiyarku daga yau bana son Badiyyah ta sake takowa cikin gidana" Abba na kai wa nan ya shiga motarsa ya wuce. Mayraah na zaune kan darduma bayan ta idar da sallan asuba tana azkar dinta idonta a lumshe ta jingina da bango, wayarta ne ya fara ring ta bude ido tana kallon wayar cike da mamakin wanda ke kiranta by this time, Dr Khalil ta gani jikin screen din, ta sake duba agogo taga karfe shidda, picking call din tayi ta kai kunne hade da sallama, ya amsa yace "Good morning, how was ur night?" Tace "Alhamdulillah, ina kwana" yace "Lafiya lau, i just want to let u know ba sai kin shigo hospital yau ba MD na da meeting, but just make sure karfe tara na yi ki tafi gidan Ummi mu hadu a can" Mayraah ta ɗan yi shiru, yace "Are u there?" A hankali tace "Eh ina ji" Yace "Good! Zan kira in ji ko kin tafi anjima nima sai rana zan shiga asibitin" Tace "Toh" Katse wayar yayi ya juya yaga Zainab tsaye kansa tana masa wani kallo, bai ma san ta fito parlorn ba, a fusace tace "To kar ta kuskura ta sake kai kafarta gidan mahaifiyata don wallahi zan mata rashin mutuncin da bazata taba mancewa a rayuwarta ba, ka nemi wani wajen da zaka kai ta amma in har tayi mistake din zuwa gidanmu yau din nan to zata ga ikon Allah, halan ita arniya ce da bata da iyaye har zata shigo garin Abuja namiji ya dinga accommodating dinta, kuma ko bata da iyaye ai bazata rasa yan uwa ba ko yawon bariki ta shigo yi a Abujan ne dama" Dr Khalil dai kallonta kawai yake ya ma rasa me zai ce mata, tace "Naga rainin hankalin ya kai rainin hankali yanzu, wato har kiranta kake da asuba ka gaya mata kar ta ma je asibiti saboda baza ka je ba, duk kwanan nan dama ina ta lura da take taken ka, ga wani gidan Ummi da ka tsiri zuwa kullum tunda ka kai ta can, an mayar da ni wata shashasha to my patient is finished, kuma ka sani babu yarda tsakanina da kai yanzu" Ya mike tsaye yace "Listen Zainab...." Ko sauraronsa bata tsaya tayi ba ta wuce daki kamar zata tashi sama, ya sauke ajiyar zuciya bai ma san yanda zai mata bayani ta fahimci babu komai tsakaninsa da Mayraah ba sae Kasancewarta er uwar sa musulma da baxai so ganin ta fada halaka ba, gani yayi ta fito daga daki da akwati kamar dama ta hada akwatin ta ajiye gefe abinda take jira kenan, da mamaki yace "Ina zaki Zainab?" Ko tsayawa bata yi ba ta bude kofa ta fice daga parlon, ya kalli dakin da twins dinsu ke ciki suna bacci, komawa yayi ya zauna don yasan ko ya bi ta tunda har taki tsayawa a nan ta sauraresa to a wajen ma bazata sauraresa ba sai ma dai kawai su tona ma kansu asiri, he definitely knows ba gidan Ummi zata ba gidan Aunty Rabi'ah zata dama ita ke zugata always. Tara da yan mintuna Mayraah ta fito daga gida bayan Dr Khalil ya sake kiranta yace kawai ta taho asibiti ba sai taje gidan Ummi ba kuma, wajen karfe sha daya ta shigo asibitin ta gaisa da nurses din da ta gani reception ta tafi sama zuwa office dinsa, hijab ne jikinta bata saka uniform ba, zaune ta samesa office din da twins dinsa sun cika sa da surutu shi kuma yana ta aikin gabansa, tun da ta hadu da su a supermarket ranan bata sake ganinsu ba sai yau don bata taɓa ganinsu gidan Ummi ba, ko kilan an kai su bata nan bata sani ba, ta karasa tana murmushi tana kallon kyawawan yaran tace "Su ma sun zo aiki yau ne Dr?" Shi dai kawai yayi murmushi yana ci gaba da abinda yake yace "Ya hanya?" Tace "Alhamdulillah" tace "Ya sunansu?" Yace "Fatima and Khadija, ana kiransu Ashnaah and Ashfah" Tace "They are so cute" yace "Dama zan fita, ke nake jira so u can stay with them here" Mayraah tace "Ohk, Maminsu fa?" Yace "Bata jin dadi ne" Mayraah tace "Toh Allah ya sauwake" Yace "Ameen" Yana kallon girls din yace "Za ku zauna tare da Aunty zan je in dawo yanzu kun ji? Ga cartoon zan kunna maku sai ku yi kallo, do not disturb Aunty" Ashnaah da Ashfah suka kalli Mayraah a tare, dukawa tayi tana masu murmushi ta kamo hannunsu tace "Hello cuties, yanzu Daddy zai dawo, i will keep u company" Dr Khalil ya dau
Chapter 188 · 0% Book details