← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 178 OF 313

Sashe 178

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*MUNA MARABA DA KU, MUNA GARIN SOKOTO MUNA AIKE KOWANI GARI KOWACCE QASA CIKIN AMINCI* Karasowa cikin parlon yayi yace "Ina wuni Ummi" Ummi tace "Lafiya lau, ko dai dama baka tafi ba?" Ya ɗan yi murmushi yace "Ban tafi ba kuma? Bayan har vid call mun yi 2 days back Ummi" Ummi tace "To na gan ka ne kamar an jefo ka ai" Sai a sannan ya ga Mayraah da kanta ke sunkuye kamar munafuka, lkci daya murmushin dake fuskarsa yayi fading, kallon Ummi yayi ya sake kallon Mayraah, kamar tasan kallon nata yake ta daga kai da sauri tace "Ina yini" Still looking at her yace "Lafiya lau" Ummi na kallonsa tace "Bakuwa ce" Yace "Oh ohk" Barin parlon yayi zuwa dakin sa, yana shiga ya ciro waya yayi dialing number Ahmad. Gaba daya Mayraah ta kasa cin abincin da ta debo a kitchen, duk ta rasa wani tunani zata yi, shi ma wannan mutumin gidansu ne nan kenan? She still vividly remember his face, Maida abincin gefe tayi ta jinginar da kanta da gado tsabar yanda ta zama confuse. Ana idar da isha mai aikin gidan ta zo tace mata Inna na kiran ta, ta mike ta saka hijab dinta ta fita, babu kowa parlor ta shiga dakin Inna da sallama murya can kasa, sosai gabanta ya fadi ganin Zainab, Dr Khalil da shi mutumin da ko sunansa bata sani ba su ma suna dakin inna, ta karasa ta zauna kasa tana kallon Inna tace "Inna ina yini?" Inna tace "Lafiya lau, naji shiru shiru baki shigo kin zubo min sabon ruwa a flask ba shine nace ko kema kin fara canza hali ne, ko kuma yan gidan sun fara canza maki ra'ayi" mikewa mutumin yayi ya fita daga dakin, Mayraah tayi murmushin karfin hali tana kallon Inna tace "Bari in kawo maki" Zainab dai sai danna wayarta take, Mayraah ta dau flask din ta fita daga dakin, Dr Khalil ya mike ya fita Zainab ta bi sa da kallon gefen ido. Mayraah na kitchen bayan ta kunna gas zata daura ruwan flask din aka bude kofa, ta juya da sauri ya shigo yana kallonta yace "U told me admission kika samu a Abuja? Aikin me kuma kike yi a asibiti yanzu?" Kallo daya tayi masa ta dauke kai ta ci gaba da abinda take tace "Admission din bai yiwu ba" yace "Why did u change ur name from the Mayraah u said at the hospital to Ilham?" Ta kallesa tace "Kaga kai ma ba dai dai ka fada sunan ba yanzu haka, so sbda irin wannan issues din yasa ake kirana Ilham most of the time" Yace "Really?" Tace "Yeah" Yace "Ohk, welcome to our home Ilham" yana fadin haka ya juya ya fita ta bi sa da kallo, wani boyayyen ajiyar zuciya ta sauke ta ci gaba da abinda take, ko da ta je kai ma Inna ruwan zafin ta tarar har Zainab da Dr Khalil sun tafi gida, ita ta ga kamar ma shakkar matar tasa yake wai ko magana bai mata ba saboda Zainab din na wajen, Inna na kallonta bayan ta ajiye flask din tace "Kin ga jikana Ahmad ya dawo daga kasar turawa ko, to shi ne babba a gidan kuma sa'annin juna ne da Halilu, shima kuma Halilun ɗan gida ne duk da ba jininmu bane shi amma ya zama ɗan gida, sai wannan mata da ta bari tayi kiba dazu da kika shigo tana zaune can tana latse latsan waya sunanta Zainab yanzu haka tana da yan biyu mata, saboda yabawa da kyawawan dabi'un Halilu, marigayi ubanta ya ba Halilun auren Zainab, kinsan ni na haifi uban nata, Allah dai ya ji kansa, Bayan Zainab sai yan biyu maza Hassan da Hussaini kullum sai su zagaya bayan windan nan su isheni da buga kwallo wai kar in huta, sai figgiyar yarinyar nan Fatima bata da aiki sai raye raye, duk Zuwaira ce ta haifesu, in ma kika ce ba ita ta haifi Halilu ba to ranta baci yake" Mayraah dai sai kirkiran murmushi take don ta kagu ta bar dakin, daga karshe ta samu ta sulale tace mata zata je tayi wanka. Musharraf na kwance dakinsa da safe Mami ta shigo, yayi mata kallo daya ya kauda kai, mancewa ma yayi bai kulle kofar ba bayan ya dawo masallaci, ta karaso cikin dakin ta zauna gefen gado tana kallonsa tace "Musharraf" Ya kalleta bai dai ce komai ba, ta kai hannu forehead dinsa tayi kasa da murya tace "Yanzu baza ka cire ma kanka damuwar nan ba Musharraf kayi facing reality" Ya ki kallonta balle yace komai, ta sauke ajiyar zuciya tace "Ta shi mu je kayi breakfast" Mikewa zaune yayi ya matsa daga kusa da ita yace "Mami duk ke kika ja wannan abun, u caused everything, da kin bari mun yi aure tun wancan lokacin she wouldn't have gone missing now, yanzu wa yasan halin da take ciki a inda take" Mami tace "Musharraf ita 'ya mace komin rintsi ban ga dalilin da zata bar gidansu ba ko ince gidan da ta taso, bata da wani hujjan da zata ce ta bar gida, ni fa tunda yarinyar nan ta iya tsallaka kafa tayi tafiyarta har aka zo ana zargin ka akayi arresting dinka naji ta fita a raina bazan boye maka ba, who knows the life she's living now tunda ta gwammaci ta shiga duniya tayi rayuwarta..." Musharraf da yaji haushin furucin Mami har ransa yace "Mami kika san wani pressure yasa ta tafi? She is so young for all this that is happening to her, she can't think straight, so ake yarinyar ta kamu da depression, she is just 22 fa Mami" Mami tace "Ni dai in za ma ka cire ta a rai ka ci gaba da harkokin gaban ka is better u do so, don babu aure tsakanin ka da wannan yarinyar just put that in mind, in kuma har ka mance abinda guardian dinta suka mana a police station sai in ji, it's simple idan har zaman kasar ma baka so to ka tafi Canada ka samu Daddy...." Musharraf ya katse ta yace "Waye Daddy? Mami pls ki daina hadani da gayen nan, i have no business with him" Mami tace "Shi ɗan uwan naka zan daina hadaka da?" Musharraf ya sauka daga kan gadon yace "Ɗan uwana that is happy with what i am going through, he is happy with my downfall, ko sau daya bai taɓa kirana duk wannan abubuwan dake faruwa ba" Mami tace "To saboda me zai kiraka, kai kiransa kake Musharraf?" Bai sake sauraronta ba ya fice daga dakin. Maheer na zaune parlon Ammi yayi kasa da murya yace "Ammi yau za a sallami Haseenah daga asibiti, so Abba insisted in kawota gidan nan har ta karasa samun sauki" Hajja da ke zaune parlon hannunta rike da carbi ta dago da sauri tana kallonsa jin abinda yace, Aunty Mariya ma da ta zo jiya da mai gidanta da ya zo yi ma Hajja jaje ta kalli Maheer da mamaki, Hajja tace "Wani gidan? Wai ci gaba da zama da matsiyaciyar nan zaka yi kake nufi Maheer? Ko dai baka da kai ne? Ita Hasinar kake mararin dawowa da ita har zaka kawota gidan nan?" Ammi dai bata ce komai ba, Hajja ta kalleta ta hade rai tace "Ya kika yi shiru Ammi? Kema kin goyi bayan ta dawo ya zauna da er matsiyatan kenan tunda har kika yi shiru" Ammi ta kalli Hajja ta sauke ajiyar zuciya tace "Hajja ba daga ni bane, nima na so nuna ma Alhajin hakan amma yace lallai Maheer bazai rabu da ita ba saboda ɗan matsalar nan da aka samu, shi yasa kawai na hakura na ja bakina nayi shiru" Hajja na gyada kai tace "Eh lallai, dole kice ɗan matsala tunda ba ke aka kai Caji opis ba aka ci ma mutunci aka walakanta ba ko shi Mamudan, ae ni aka taɓa dama ba ku ba, karshen biyayyar da kike ma Mamuda naga sakayya ya maki da kishiya ai, ke uwar yan bin miji, wato baza ki iya nuna masa ke baki yarda ba an ci mutuncin uwarki shine kika yi shiru kika kyale hukuncin da ya yanke, to ba komai ai rayuwa ce" ita dai Ammi kanta na kasa, mikewa Hajja tayi tana kallon Aunty Mariya tace "Ni ai sai in bar gidan, dama banda lalura da damuwar da yayi min yawa ban san halin da yarinyar mutane ke ciki ba ga dangin ubanta sai zarya suke mana me zai zaunar da ni a gidan surki har zuwa yau, ai an san ba halina bane wannan, ki tashi mu je Mariya dama zuwanki kawai nake jira kuma jiyan baku iso da wuri ba" a hankali Ammi tace "Aa kiyi hakuri Hajja yanxu haka fa Alhajin suna hanya da Badiyyar mun yi waya da shi yace an gama komai in Allah ya yarda yau zata dawo gida an rufe case din" Ko rufe baki Ammi bata yi ba Badiyyah ta shigo parlon, Hajja ta saki salati ta fashe da kuka ta tafi da gudu ta rungumeta tana kiran sunanta, Ammi dai sai kallon Badiyyah take ganin yanda ta rame tayi bakikirin kamar ba ita ba, ita kanta Aunty Mariya sake baki tayi tana kallon Badiyyah, Hajja na kallonta daga sama har kasa cikin kuka tace "Sannu Badiyyah, sannu, Allah Ubangiji ya saka maki wannan abu da aka maki, Allah ya saka maki" Aunty Mariya tace "Allah ya saka mata fa kika ce Hajja? Yarinyar da ta dauke wayar mutane me tsada ne zaki dinga yi ma wannan addu'ar? Maganar da sai da na kai zuciyata nesa na iya sanar ma mai gidana saboda kunya, kuma ke nan har kullatata kika yi ban zo ba, sata fa Hajja? Gaskiya wannan ba karamin abun kunya Badiyyah ta ja mana ba ta ja ma kanta, me ta rasa da zata jefa kanta cikin wannan mummunan hali na satan kayan mutane?" A mugun fusace Hajja ta juyo zata yi magana sai ga Abba ya shigo da sallama, Hajja ta koma ta zauna tayi kasa da kai don dama da hijab dinta a jiki, Abba ya zauna ya gaida Hajja, Hajja ta amsa tana masa sannu
Chapter 178 · 0% Book details