← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 313

Sashe 59

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Ka bar er mutane fa a gida Maheer..." Yace "Ai kawayenta suna nan, kuma sai naje ma zan maida su various houses dinsu" Ammi ta kalli Mayraah tace "To sai kun dawo Mimi" yana gaba ta bi bayansa suka fita daga parlon, mamaki bai cika Maheer ba sai da yaga all through the ride ko tari bata yi ba, Mayraah da har sai ya gaji da labarinta idan suna mota tare, sosai ya ji abun ya damesa yanzu, yayi parking dai dai wani eatry yana kallonta a hankali yace "Shawarma da me zan siya maki?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Anything" Bayan few seconds ya bude motar ya sauka ta bi sa da ido, yana dawowa motar ya ajiye mata abinda ya siyo mata sannan suka bar wajen, duk da hanyar da ta ga ya nufa da ita bata ce komai ba, bayan tafiyar kusan minti ashirin yayi parking dai dai gate din gidansa, wayarsa ya dauka yayi dialing number Haseenah tana dagawa yace "Tell ur frnds ina jiransu zan ajiye su gida yanzu" Da mamaki Haseenah tace "Ban gane ba, ina abokan naka? Kana nufin yanzun ma baza a siyi baki ba da sauransu?" Maheer yayi shiru kafin yace "Bakin wa za a siya?" A fusace Haseenah tace "Ni wallahi na gaji da walakancin da kake min Maheer dama ba sona kake ba ka aureni?" Tana kai wa nan ta fashe da kuka, yace "No.... it's not like that Haseenah, kinga frnds dina yawanci a Abuja suke so duk sun koma saboda aiki, kiyi hakuri kawayen naki su fito in maida su gida, sannan su fadi nawa za a basu sai su turo account number" Cike da shagwaba Haseenah tace "Za ku yi magana da Zaliha idan sun fito" Yace "Alright" Daga haka ya katse wayar, juyawa yayi ya kalli Mayraah, if it was before yanda tayi shiru haka da ya ja hancinta amma yanzu kam bai yi hakan ba, yayi kasa da murya yace "Tunanin me kike?" A hankali tace "Bacci nake ji" Yace "Ohk, yanzu zan maida ki gida ki kwanta, hope kina shan magungunan da na siyo maki tunda baki son alluran?" Ta gyada kai tace "Ina sha" Yace "Ohk" kawayen Haseenah hudu suka fito daga gidan har da Badiyyah, Maheer ya hade rai ganinta, Zaliha ta bude front seat tana washe baki tace "Ango ka sha kamshi" Gaba dayansu suka yi turus ganin Mayraah gaban motar, barin Badiyyah da ta bude baki da mugun mamaki, Maheer yace "Ku shiga in ajiye ku gida, it's getting late" Zaliha ta kirkiri murmushi ta koma back seat tare da sauran frnds din nasu, Badiyyah ta zaro ido tace "Aneesah na baki wayata kuwa?" Aneesah tace "Aa" Da sauri ta juya ta nufi cikin gidan tana cewa "Lahhh ban ciro sa a caji ba kenan" Badiyya na tuntube ta koma dakin Haseenah, tsaye ta ganta gaban madubi tana gwada kayan baccin da zata sa tana murmushi, Badiyyah tace "Ke kinsan da wa Maheer yake a cikin mota kuwa?" Haseenah ta juya da sauri tace "Aa" Badiyyah tace "Wllh er tsintuwar nan muka gani zaune gaban motarsa, wato duk maganganun da muka maki kan cewar ki ja masa aji yau akan abubuwan da ya dinga maki a biki har kin watsar kin wani kwaso kayan bacci kin zube kina zaba ko? To ai shikenan" Sosai gaban Haseenah ya fadi jin warce Badiyya tace mata sun gani a motar Maheer, ta dinga kallon Badiyyah ko kiftawa babu, tuni Badiyyah ta juya ta fice daga dakin ta koma compound tana ma mai gadi sallama sannan ta fita kofar gida, still tayi bakin gate ganin babu motar Maheer alamar ya tafi ya bar ta. Wajen karfe tara da rabi Mayraah na tsaye a kitchen kusa da gas tana dafa ma Ammi shayin da ta saba yi mata, dafa shayin take amma gaba daya hankalinta baya jikinta, rashin samun wayar Musharraf ya dameta sosai don har wani zazzabi take ji yanzu, to ko dai he doesn't need her anymore because of who she is, tunanin hakan yasa taji hawaye ya kawo idonta, sai yanzu ta sake tabbatar da son da take ma Musharraf na gaske ne, tana kokarin zuba shayin a cup bayan ta gama taji an bude kofar kitchen din ta juya, sosai gabanta ya fadi ganin Badiyya ce ta shigo, Mayraah tayi saurin dauke kanta ta ci gaba da abinda take tana goge idonta zuciyarta na bugawa, dawowar Badiyya kenan gidan tun bayan da Maheer ya tafi ya bar ta, Badiyyah tayi wani dariya tana kallonta tana tafe hannu, can ta rike haɓa tace "Ohh wai Shege ya fi ɗan masu gida, to in ji dai yanzu kin gane cewar matsayina da naki ba daya bane a family dinmu, don ke ba kowa bace facce tsintattciya walakantacciya warce karuwar uwarta ta wuragar da ita a gefen masallaci! Banda ma rashin sanin wacece ke ai da baza ki fara soyayya da Musharraf ba don yafi karfinki nesa ba kusa ba, shima kuma ko a mafarki bazai so ya kula irin ki ba mara asali, dama ance rashin sani yafi dare duhu, ai irin su Dr Musharraf sai mu masu asali gaba da baya yan dangi yan gata ba wa enda aka jefar tun suna tsummam haihuwa ba...." Mayraah kasa juyowa tayi sai hawaye kamar an bude famfo, ihun da taji Badiyya ta kwala ne yasa ta juyawa da sauri, da kafa ya sa ya kwasheta sai ga ta rigijib a kasa sannan ya kulle kofar kitchen din, Mayraah ta tsorata sosai ga koma gefe tana kallonsa, tuni ya zare belt dinsa ya fara lafta ma Badiyya ta wajen kan belt din kamar an aikosa, Ihu Badiyya take iya karfinta tana kokarin tashi amma ta kasa tsabar yanda belt din ke shigarta ta dinga birgima kamar macijiya tana cewa "Na shiga uku na lalace, Hajjaaaa" Mayraah da duk ta gigice ta tafi kofar kitchen da zai yi leading dinka zuwa backyard din gidan zata bude ya daka mata tsawa yace "Kina budewa zan hada da ke" Makalewa tayi jikin kofar zuciyarta na bugawa tana kallon yanda yake dukan Badiyya ba kakkautawa, bude kofar kitchen din Aunty Mariya tayi a gigice don tana saukowa parlor ta fara jiyo ihu kamar daga kitchen, a sama kuma ba a jin komai, Badiyya na ganin Aunty Mariya cikin gigicewa ta dinga cewa "Wayyo Aunty ki shigo ki taimakeni zai kasheni, wallahi kasheni zai yi ki kira har da su Hajja da Ammi" Aunty Mariya na ganin abinda ke faruwa ta kullo kofar kitchen din tana murmushi ta koma parlor ta zauna, Sai da yayi mata lilis ya farfasa mata duk jikinta da belt har bata iya motsin kirki tsabar dakuwa sannan ya duka yana kallonta cikin husky voice da idanuwansa da suka canza launi yace "Ko kallon banza ki sake yi mata a gidan nan ki ga" Daga haka ya tsallaketa ya nufi kofar kitchen da Mayraah ke kokarin budewa ya hanata, da sauri ta koma gefe ta basa waje gabanta na faduwa, ya bude kofar ya nuna mata waje yace "Fita mu je" Ba musu ta fita da sauri, shi ma ya fita ya kullo kofar.....
Chapter 59 · 0% Book details