← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 268 OF 313

Sashe 268

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

You'll never regret buying from us.* Personal Driver din Ceo yayi parking a babban parking space din dake cikin gidanta, ta bude back seat ta sauka MD ma ya sakko daga front seat yana kallonta, entrance din shiga mansion din nata ta nufa yana biye da ita a baya, babu kowa a babban parlon gidan ta wuce upstairs, MD ya zauna a parlon ya bi ta da kallo har ta haura sama, bayan dan lokaci daya daga ma'aikatan ta da ya sani a gidan ta sauko kasa ta gaishesa da ladabi sannan tace "Sir tace ka sameta upstairs" MD ya mike tayi leading dinsa zuwa wani babban parlor a sama, nan ma dai babu kowa ciki ya zauna, zuwa yanzu shi kansa ya kagu ya ji dalilin kawosa gidanta da tayi by this time, yayi sensing akwai wani abu me muhimmanci da yasa ta kawosa gidan and he is eager to know what that is, bayan kusan minti goma sai ga ta ta shigo parlon tana kallonsa a hankali tace "Come in Aliyu" Mikewa yayi ya bi bayanta suka bi wani corridor me fadi sannan ta bude daya daga kofofi hudu dake wajen ta shiga yana biye da ita a baya, babban daki ne sosai that is well furnished, babu abinda babu a cikin dakin, kwance saman gadon wata kyakkyawar mace ce da bazata haura shekara 42 ba cikin babban duvet, tsaye a dakin wata registered nurse ce sai maid biyu, Ceo ta karasa kusa da ita ta zauna tana shafa dogon gashinta a hankali tace "Meet Dr Aliyu" Kallonsa kawai matar take babu ko kiftawa, MD ya dan kirkiri murmushi yace "Good Morning ma'am" ta dai kafesa da ido, Ceo ta sauke idonta kasa, bayan few seconds ta kwantar da ita a hankali tana kallonta, Maid din dake tsaye ta karasa da sauri ta gyara mata duvet din da pillow, Ceo na kallon nurse din dakin tace "Ya aka yi bata yi bacci ba har yanzu?" Da ladabi nurse din tace "Farkawa tayi Ma" Ceo ta sauke idonta tace "Sorry i interrupted ur sleep, pls get me a Syringe and Needle" Nurse din ta juya ta bude wani kofa ta shiga ciki, ba a dau lokaci ba ta dawo rike da shi, Ceo na kallon MD tace "Come over Aliyu" Ya karasa kusa da gadon, shi ta sa ya debi jinin, matar was calm har ya gama diban jinin, bayan few minutes Ceo tayi pecking forehead dinta sannan ta kwantar da ita, Daga haka ta mike ta nufi kofa tana fita MD ya bi bayanta, tsaye ya sameta a parlor ta fada duniyar tunani, ya sunkuyar da kansa don shi dai at this point he is confuse at what she is up to, ga jinin dake cikin karamin roba inside a ziploc da ke hannunta, to wace mata ce wannan da ta sa ya debi jininta don shi dai duk zuwansa gidan bai san da ita ba, bai kuma taɓa ganinta ba duk da har upstairs ya kan kai ma Ceo sako, ya dai san ma'aikatan gidan kaf dinsu amma banda wannan mata dake kwance wanda ga dukkan alamu she is not even stable, kallon Ceo ya sake yi ya ga ta dan yi murmushi tana goge hawayen da ke taruwa idonta without looking at him tace "We are going back to the hospital now Aliyu" Ya gyada kai yace "Ohk Ma" Shi ya fara nufar kofa cike da mamaki ya fita daga parlon sannan ta bi bayansa tana tafiya a hankali, karfe biyu da rabi suka isa asibitin, Dr Balogun da shigowarsa reception kenan ya karasa yana ma Ceo sannu da zuwa, Ba tare da ta kallesa ba tace "An maida Mary Ann ward ne ko har yanzu tana da Emergency?" Da ladabi yace "An maida ta ward ma, ai numfashin nata is stable yanxu" Tace "Wani ward din take?" Gaya mata yayi ta nufi ward din MD na biye da ita, Aunty Mariya ce zaune ita kadai a ciki sai Mayraah da ta samu bacci, Aunty Mariya tayi ma Ceo din sannu da shigowa ta koma gefe, Ceo ta amsa idonta na kan Mayraah sai kuma ta kalli MD, calmly tace "Get a Syringe and Needle" MD ya juya ya fita ward din wondering abinda zata yi da shi, bayan few minutes sai ga shi ya dawo, Ceo tace "Take her blood sample" MD was stunned jin instruction din da ta basa, haka nan dai ya debi jinin Mayraah sannan suka fita daga ward din Aunty Mariya dai ta bi su da ido, MD ya raka Ceo har office dinta, bayan ta zauna ta basa sample din da ta sa ya diba a gidanta, a hankali tace "Genetic testing for the both samples nake so Asap" Mamaki ne ya cika MD ya dinga kallonta, har mamakin ya kasa boyuwa a fuskarsa, genetic testing kuma? To me hakan ke nufi? What is her aim nayi genetic test for the both samples, ya dai yi karfin halin amsan samples din yana kallonta, can ya juya ya nufi kofa ta bi sa da kallo idonta cike da wasu sabbin hawayen. Washegari da safe bayan Ceo ta shiga ward din da Mayraah take ta dubata ta fito, har bakin motar ta MD ya rakata da laptop dinta, bayan ta shiga bayan motar ya mika mata laptop din ganin yanayinta yace "Ma'am u need rest" Ta gyada masa kai a hankali tace "Sure, pls ku kula da ita yanda ya kamata" Yace "We will do that Ma" kulle mata motar yayi daga haka ya juya ya koma asibitin, a reception ya tadda Musharraf ya fito daga ward din da Mayraah take, MD na kallonsa ganin zai fita yace "Ina zaka?" Musharraf yace "Airport, my flight is in 30mins time" MD yace "Why did u book without telling me?" Musharraf yace "Mami ai ta gaya maka yau zan koma kano" MD yace "Allah ya tsare" Daga nan ya wuce sama, Musharraf kuma ya fita daga reception din. Daga wannan ranan Ceo bata sake shigowa asibitin ba, a kwana hudu Mayraah ta samu sauki sosai har tana iya cin abinci, all through this 4 days Aunty Mariya ce tare da ita a asibitin sai Usman da Ammi dake zuwa dubata kullum, don Abba ya hana Ammi kwana asibitin. Yau da yamma suna haraban asibitin da Aunty Mariya bayan sun yi strolling kamar yanda likitocin suka ce ta dinga yi duk yamma, Mayraah ta kalli Aunty Mariya da damuwa tace "Aunty wai me yaya yaje yi a kasar waje ne har yanzu bai dawo ba?" Aunty Mariya tace "Wani aiki ne ya kai sa mana, amma nasan ya kusa dawowa in sha Allah" Mayraah dai tayi shiru tana nazarin abinda Aunty Mariya tace, can dai ta sake kallon Aunty Mariya tace "Shine zai tafi bayan yasan bani da lafiya?" Aunty Mariya tayi dariya tace "Gaskiya kam, don kamata yayi ya ajiye masu aikin ya zauna kusa da kanwarsa har sai ta samu lafiya" Murmushi Mayraah tayi bata sake cewa komai ba, Aunty Mariya tace "Ta shi mu shiga ciki ai kinyi strolling din da yawa yau" Mikewa Mayraah tayi suka koma cikin asibitin tare da Aunty Mariya, a haka dai har Mayraah suka yi kwanaki bakwai tare da Aunty Mariya a asibitin, all this while MD gaba daya attention dinsa da curiosity na kan Genetic testing din da Ceo ta basa ayi, ya rasa dalilin kaguwan da yayi result din ya fito, sai kirga kwanakin yake, a washegarin ranan kuma Abba ya bukaci ayi discharging dinsu a gaya masa bill in dai babu sauran matsala don kowa yaga Mayraah yasan ta samu lafiya sosai, Bayan azahar Dr Khalil na kallon MD dake zaune kan office chair dinsa bayan ya sanar masa bukatan Abba yace "Amma kai ya ka ga? Ni dai a ganina ya kamata ayi discharging dinsu" MD yayi shiru, shi kansa yasan Mayraah ta samu sauki yanzu, kuma tunda case din nata a hannunsa yake shi ya kamata yayi discharging dinta amma yaki yin hakan beside ita ma Ceo bata ce yayi hakan ba don kullum sai ta kirasa ta tambayi jikinta asibitin ne dai taki shigowa, Dr Khalil yace "Wai tunanin me kake ne sir? Ko baka gaji da ganinta bane har yanzu?" Da murmushi ya kare maganar, Shi dai MD bai tankasa ba, can yace "Ban gane ban gaji da ganinta ba, let me call Ceo first...." Da mamaki Dr Khalil yace "Ceo kuma? Ita da bata kasar, beside naga ba a taɓa sanar mata ba idan za a sallami patient?" MD yace "Tana kasar nan, beside file din a hannunta yake not me...." Dr Khalil yace "Really, naga yau sati daya bata shigo ba, na zata ta koma ne wallahi....." MD yace "Bata da lafiya ne, but she is better now" Dr Khalil yace "Allah ya bata lafiya" MD ya dau wayarsa yayi dialing number Ceo yana fara ring ta daga, bayan ya gaisheta ya sanar mata dalilin kiran, Ceo tayi shiru, bayan few seconds tace "Zaka iya discharging dinsu, as for bill da ya tambaya kuma, tell him basu da bill" a hankali yace "Ohk Ma'am" Tace "Yaushe result din nan zai fito Aliyu?" Yace "Zuwa anjima in sha Allah" cikin sanyin murya tace "No bill for them" Yace "Ohk Ma'am" Mikewa yayi ya nufi kofa Dr Khalil ya bi bayansa. Tun da Mayraah taji an sallamesu take farin ciki don gaba daya ta kagu su bar asibitin ta koma gida, shi dai Usman bai gane dalilin da zai sa MD yace babu maganar bill everything is free ba, Aunty Mariya na kallonsa tace "Aa fa barrister, ni a ganina saboda staff dinsu ce shi yasa suka ce babu zancen Bill" Usman yace "Gaba daya yaushe ta fara aikin har ta zama staff dinsu? Kinsan yau kwananta nawa a asibitin nan kuwa? ko ICU kinsan nawa ake biya a rana daya balle wannan asibitin me tsada, kuma tayi kusan sati daya a ICU, hatta drugs da alluran da aka dinga mata kwanaki masu tsada ne, ga kuma abincin da ake bata sau uku a rana, so i don't understand dalilin da zai sa yace babu Bill" Mayraah dai sai kallon Usman take, Aunty Mariya tace "Mu dai koma menene
Chapter 268 · 0% Book details